Docstoc

DAGA DUTSEN DALA

Document Sample
DAGA DUTSEN DALA Powered By Docstoc
					…………….Daga Dutsen Dala
 2
Kano Qwaryar Qira…...

 KANO QWARYAR QIRA MATATTARAR
   ALHERI, LITTAFI NA XAYA:
   KANO DAGA DUTSEN DALA

          SHIMFIXA
    Kano babbar qasa ce mai daxaxxen tarihi,
da albarkar qasa, da shahara. Saboda haka ta zama
abin duba ga masu neman tarihin duniya
musamman na qasashen waje. Kaxan daga cikin
masu bincike a kan tarihin Kano, waxanda suka
fara sanar da duniya labarin a cikin littattafan da
suka rubuta, sun haxa da Leo Africanus wanda ya
ziyarci Kano (wacce ya kira "Cano") a 1513-1515,
a lokacin Sarkin Kano Kisoki jikan Sarkin Kano
Muhammadu Rumfa. Ya rubuta littafi a kan
wannan ziyara tasa mai suna History of Africa and
Memorable Things Contained Therein, London
(1600). Sai kuma Captain Hugh Clapperton wanda
ya zo Kano a 1824, zamanin Sarkin Kano Ibrahim
Dabo, ya rubuta littafinsa; Narrative of Travels
and Discoveries in the North Central Africa,
London 1826.
    Sauran marubuta akan tarihin Kano su ne
Heinrich Barth, wanda ya zo Kano a 1851, da
1854, a zamanin Sarkin Kano Usman xan Dabo,
ya rubuta littafinsa; Travels and Discoveries in the
North Central Africa, London 1890. Sai Paul             3
           …………….Daga Dutsen Dala

Staudinger wanda ya zo Kano a 1885, lokacin
Sarkin Kano Bello xan Dabo, ya rubuta littafinsa
da Jamusanci mai suna Im Herzen der Haussa
Lander, Berlin 1889, sannan aka fassara shi da
turancin Ingilishi da suna: In the Land of Hausa,
London 1968.
    Wannan hali na zamowar Kano babbar qasa
ya ci gaba da bawa marubuta sha‟awa har ya bada
damar yin bincike mai zurfi a cikin tarihin
bunqasarta dangane da arziqin qasa da rayuwar
jama'arta. Tun daga 1960 har zuwa 1980, masu
bincike a kan tarihin Kano daga kowanne vangare
na duniya sun yi rubuce-rubuce masu yawa a
kanta. Cikin irin waxannan rubuce – rubuce,
akwai littattafai guda huxu na mutane daban –
daban waxanda ya kamata a ambata:-
  i. Littafin    M.G. Smith Mai Suna
    Government in Kano. Littafin John
    Paden mai Suna Religion and Political
    Culture in Kano.
  ii. C.N. Ubah – Yayi Nazarin Ph.D akan
    tarihin Kano.
 iii. Adamu Fika ya rubuta Littafi mai suna
    Kano Civil War and the British Over
    Rule.
   Waxannan nazarce-nazarce da rubuce-rubuce
sun qarawa labarin Kano shahara da aminci.            4
Kano Qwaryar Qira…...


   Amma abin takaici a cikin waxannan rubuce-
rubuce a kan tarihin Kano shi ne gudunmuwar
'yan bokon Kano ba ta da yawa a ciki, idan ma
akwai ta. Saboda haka ne na quduri niyya a kan
cewa in Allah Ya yarda sai na rubuta littafi a kan
tarihin Kano da harshen Turanci domin kar a ce
"an zo garinmu an fi mu rawa".

YUNQURIN FARKO
   A shekarar 1967, lokacin da nake xalibi a
fannin tarihi a Abdullahi Bayero College/ Ahmadu
Bello University, ABC/ABU (yanzu Bayero
University, Kano), sai na rubuta wata maqala mai
taken Notes on the Influence of North African
Traders on Kano, wacce aka buga ta a cikin
mujallar Kano Studies, Vol. I, No. 4, 1968, wato
shekarar da na gama xalibtar. Fitowar wannan
maqala tare da maqalar M. Al-Hajj mai suna
Warqa Maktuba Fiha asl al-Wangariyin al-
Muntasibin, wacce ta qunshi labarin zuwan
malaman Wangarawa Kano, a zamanin Sarkin
Kano Muhammadu Rumfa, ya ba ni fice da
shahara a tsakanin marubuta tarihi na wannan
lokaci. A nan ne nake qara bayyana godiyata ga
malamina, marigayi Professor John Lavers, wanda
ya qarfafa min zuciya wajen rubuta wannan            5
            …………….Daga Dutsen Dala

maqala kuma ya taimake ni da yi mata tushen
bayani.
    Shekaru kaxan bayan rubuta wannan
maqala sai ta zama xaya daga cikin littattafan
tarihi waxanda ake neman sani a cikinsu a kan
nazarin tarihin qabilu da al'adun qasar Kano. Sai
ga shi mutane suna zuwa waje na akai-akai suna
neman qarin bayani a kan wani abu wanda suke
neman qarin fahimta a cikinsa. Wasu kuma sukan
zo min da shawarwari masu amfani a kan ko zan
yi wa maqalar 'yan gyare gyaren abin da yake
rauni a cikinta, kuma in faxaxa ta, ta zama
cikakken littafi. Duk lokacin da aka zo min da irin
wannan shawara na kan ba da amsa da cewa ai an
rubuta maqalar ne saboda wata buqata ta daban,
saboda haka akwai iyakar labarin da ya kamata a
kawo a cikinta. Ita dai wannan maqala na rubuta ta
ne ta hanyar jin labaran iyaye da kakanni na
larabawan Tripoli mazaunan Kano, wanda suka ji
daga bakin iyayensu. Domin ni na girma a cikinsu
tun ina qaramin yaro har na zama saurayi, saboda
haka ne na riqe labaransu da yawa a zuciyata.
    Amma sai na ci gaba da bincike da tara
labarai akan tarihi da al'adun qabilun qasar Kano
daban-daban, a duk lokacin da na sami damar yin
hakan. Ta haka ne na ci karo da wasu littattafai da
wasiqu da larabawa suke rubutawa a Kano            6
Kano Qwaryar Qira…...

musamman larabawan Libya. Daga cikin
waxannan rubuce-rubuce na larabawan akwai
littattafan Malam Adamu na Ma‟aji na unguwar
Alfundiki, Al-athar al-Kanawiyya da kuma Al-
I’ilani bi tarihi Kano. Ta cikin wannan binciken
ne kuma na samo littafin Alqalin Kano
Muhammadu Zangi mai suna Taqyeedul-
Akhbar, daga hannun Shehu Nasiru Kabara a
1972. Sabo na da Larabawan Yamal ya sa na sami
abokai masu yawa a cikinsu, saboda hakan na san
labarin iyayensu da kakanninsu. A cikin birnin
Kano kuma abotata da 'ya'yan Agalawa da na
Tokarawa, da na Barebari, da 'yanuwana Fulani ta
qara min sha'awa a kan yadda qasar Kano ta zama
qasar qabilu iri-iri amma al'umma xaya, addini
xaya, al'adu xaya a qarqashin Sarki xaya sarkin
Kano, cikin zaman lafiya da lumana.

RUBUTA LITTAFIN FARKO CIKIN
TURANCI
    A cikin 1998, bayan shekara talatin da buga
maqalar farko ta 1968, sai wata damar ta sake
samuwa. Aka gayyace ni don na faxaxa maqalar
farko, na gyara ta, na gabatar da ita a wani taro da
aka yi a wannan shekarar: International
Conference on Cultural Interaction and
Integration Between North and Sub-saharan             7
            …………….Daga Dutsen Dala

Africa. Jami‟ar Bayero ta Kano da World Islamic
Call Society ta qasar Libya sune suka shirya
wanan taro wanda aka yi a ranar huxu zuwa shida
(4-6) ga watan Maris na 1998, a nan Kano. Kamar
yadda maqalar farko ta yi fice wannan ma sai ta
yi, ta kuma ba da sha'awa fiye da ta farko,
musamman a tsakanin samari da 'yanmata,
waxanda suka ji ta inda al'adun iyayensu da
kakanninsu suka fito. Ban da wannan kuma
ayyukan da na yi a ma'aikatun N.A. da na
Gwamnati sun ba ni damar shiga cikin shirye-
shiryen tsara sabuwar rayuwar jama'ar Kano ta
arziqi da zaman lafiya.
    To waxannan abubuwa su na bi na yi
amfani da su na rubuta tarihin Kano da harshen
Turanci mai suna: Confluences and Influences:
The Emergence of Kano as a City-State, wanda
aka buga shi ya fito a cikin shekarar 2001, a Kano.
Fitowar wannan littafi ta warkar min da takaicina
na rashin samun wani xan bokon Kano da ya
rubuta cikakken tarihin Kano da harshen Turanci
sai dai baqin Turawa da sauran qabilun Najeriya.
Bayan wannan huce haushi nawa, sai kuma na ga
ya kamata na rubuta wannan tarihi na Kano da
harshen Hausa domin xumbin jama'a masu jin
harshen Hausa su san cikakken tarihin Kano tun
daga farkonsa har abin da ya zo cikinsa na zamani.            8
Kano Qwaryar Qira…...

Saboda haka na rubuta wannan littafi na sa masa
suna: Kano Qwaryar Qira matattarar Alheri.
Na raba wannan littafi izuwa kashi biyar, kuma
kowanne kashi an yi masa kanun labari domin a
fahimci wani vangare na tarihin Kano, da ya qunsa
kamar haka:
1.  Littafi na Xaya: Kano Daga Dutsen Dala
   Wannan littafi ya qunshi Tarihin Kano tun
   daga kafuwarta da ire – iren hukomomin da
   suka mulke ta tun daga kan Bagauda har
   zuwa kan Muhammadu Alwali na biyu
   wanda mulkin Have ya faxi a hannunsa.

2.  Littafi na Biyu:
   Kano Daga Kwazazzabon ‘Yarkwando
   Shi kuma wannan littafin ya qunshi tarihin
   bayyanar Shehu Usmanu Xan Fodiyo da
   almajiransa na Kano da Jihadin da suka yi
   har mulkin Fulani ya samu. Haka kuma yayi
   bayanin mulkin Sarkin Kano Sulaimanu da
   kuma Ibrahim Dabo.

3.  Littafi na Uku: Kano Da Maqwabtanta
   Wannan littafi yayi bayanin mulkin „ya‟yan
   Sarkin Kano Dabo biyu wato Usman Maje
   Ringim da Abdullahi Maje Karofi da irin
   zaman da Kano tayi da Maqwabtanta kamar            9
           …………….Daga Dutsen Dala

   Ningi da Kazaure da Hadejia da Gumel da
   Damagaran a wancan lokacin.

4.  Littafi na Huxu: Kano Daga Garko
   Shi kuma wannan littafin bayani yayi akan
   sarautar Sarkin Kano Bello Xan Dabo da
   rigingimun da suka faru tsakaninsa da
   „ya‟yan xan uwansa Abdullahi Maje Karofi
   waxanda suka haifar da yaqin Basasa a
   Kano. Haka kuma yayi bayanin sarautar
   Sarkin Kano Alu.

5.  Littafi na Biyar:
   Kano Daga Dutsen Bompai
   Shi kuma wannan littafi bayanin zuwan
   turawa qasar Hausa yayi. Da yadda suka ci
   Kano da irin sauye – sauyen da mulkin
   turawa suka haifar a Kano da ma shauran
   qasashen arewacin Najeriya baki xaya.

    Amma kafin mu shiga cikin tarihin Kano
ka‟in da na‟in zai yi kyau mu fara warware wasu
qulle - qullen da suka dabaibaye tarihin Kano da
ma na Hausawa gaba xaya. Haka kuma zai yi
matuqar amfani, mu sanar da mai karatu hanyoyin
da aka bi wajen nemo sahihin tarihin wannan gari
kamar yadda wannan littafi ya qunsa.           10
Kano Qwaryar Qira…...


WAHALAR NEMAN TARIHIN QASAR
HAUSA
    Wata matsala mai wahala da take fuskantar
duk wani mai neman sanin tarihi a qasar nan, ko
yake son rubuta tarihin qasar, ita ce rashin samun
rubutattun littattafai, masu yawa na tarihin qasar
nan.
    Akwai masu da‟awar cewa wai a da kafin
Fulani su fito da jihadinsu akwai littattafai masu
yawa, waxanda malaman Wangarawa suka rubuta
a kan tarihin qasar nan, wai amma Sarkin
Musulmi Bello da „yan‟uwansa suka qona su, wai
don labarin kafirai ne. Wannan magana ba gaskiya
ba ce kuma an yi ta ne don a munana tarihin
jihadin Fulani da kyakkyawan sunan nan na
Sarkin Musulmi Bello xan Shehu Usman
Xanfodiyo.
    Wannan magana wanda ya sa aka rubuta ta
a cikin gabatarwa ga littafi na biyu na Labarin
Hausawa Da Maqwabtansu, (littafin Tarihin
Kano), shafi na 6. shi ne R.M. East, a cikin 1933.
Shi kuma Mr. East ya lave ne wajen yin wannan
magana tasa da qagen da Shehun Borno
Muhammadu El-Kanemi ya yi wa shugabannin
jihadi a kan wani yaqi da aka yi tsakanin Malaman
„Yandoton Tsafe da mabiya Shehu Usman. A            11
           …………….Daga Dutsen Dala

wannan yaqi na „Yandoton an watsa takardun
malaman „Yandoton a ko ina cikin kwararo. To
amma wannan abu ya afku ne bisa kan tsautsayi,
ba bisa kan niyya ba. (Mai karatu zai sai cikakken
bayanin abin da ya faru a kan wannan lamari a
sashi na biyar na littafi na biyu kamar yadda
muhawar Shehu Borno da Sarki musulmi Bello ta
fayyace.)
     To qaddara ma dai bisa kan niyya xin ne
aka yi wannan abu, yanzu a ce waxannan takardu
da aka watsar na malaman „Yandoto su ne duk
tarihin qasar Hausa yake cikinsu? Ko zai yiwu a
ce a „Yandoton Tsafe ne aka tara duk littattafan
tarihin Hausa, wanda wai Wangarawa suka rubuta
kuma Sarkin Musulmi Bello da „yan‟uwansa suka
qona wai don rubutun kafirai ne? Shin wai su
wane ne „yan‟uwan Sarkin Musulmi Bello ne
masu qona tarihin Hausawa a lokacin jihadi? Ai an
yi jihadi a Kano da Katsina da Daura da Hadeja da
Zazzau da Gobir. Waxannan qasashen su ne Hausa
Bakwai.
    Ko Mr. R.M. East da duk wani mai da‟awar
Sarkin Musulmi Bello da „yan‟uwansa sun qone
littattafan tarihin Hausawa za su iya gaya mana
yawan littattafan da aka samu a kowane gari da
Fulani suka ci cikin garuruwan nan na Hausawa da
muka zana? Dattijo ba ya da‟awar abu ya vata, ko            12
Kano Qwaryar Qira…...

an qona abu, ko an sace, sai ya san da samuwar
abin tun da farko. To idan ya ga abin ya vata,
sannan zai iya yin da‟awar da yake so. Kuma ko
akan haka ma sai mutum ya tabbatar da yadda aka
vatar da abin.
    Muhammadu El-Kanemi ya san Fulani sun
yi jihadi a Borno, har Gwani Mukhtar ya cinye
Ngazargamu, littattafai nawa na tarihin Borno
Fulani suka qona a Borno? Ko Borno ba ta da
rubutaccen tarihi ne a lokacin da Fulani suka ci ta
da yaqi?
    Mr. H.A.S. Johnson ya ambaci wannan
qagen a cikin littafinsa mai suna The Fulani
Empire of Sokoto inda ya ce wannan magana ba
gaskiya ba ce. Abin da ya faru a qasar nan game
da tarihinta shi ne babu marubuta tarihinta da
yawa. Don haka ba a samu littattafan tarihin
sarakunan Hausa a rubuce kamar yadda ya kamata
ba, saboda „yan qasar ba kasafai suke yin ilimi ba,
su kuma Malaman Wangarawa, malaman fada ne.
Malamin fada kuma ya fi ba da himma a wajen
taimakon sarki da asirce-asircen yaqi da na
mallakar jama‟a. Ina ruwan malamin fada da
nishaxin rubuta tarihi? Akwai masu qoqarin rubuta
tarihin a qasar Hausa jefi-jefi, amma tarihin baka,
da aka ji daga bakin tsofaffi da kuma waqoqin
malamai da na „yan ma‟abba sun fi yawa, kuma su            13
            …………….Daga Dutsen Dala

aka fi sani a matsayin mavuvvugar tarihin qasar
nan.
    Idan ma aka duba yadda fannonin ilimi suke
a cikin al‟ummar Musulmi, Malaman Wangarawa
ba sa cikin irin malaman da aka sani da rubuta
tarihi, domin ba fannin da suka sani ba ne. Kamar
yadda Dr. Ibrahim Hassan ya faxa a cikin littafinsa
Tarihil Islam: ilimi ya kasu izuwa fannoni biyu;
ilimin Naqali da ilimin Aqali. Shi ilimi naqali shi
ne ilimin da ake samu daga cikin Alqur‟ani da
Sunnar Manzon Allah (S.A.W). Wato shi ne ilimin
Shari‟a da Tafsiri da Hadisi da Fiqihu da Nahawu
da Lugga da Bayani, kuma wannan shi ne ilimin
da Malaman Wangarawa suke da shi. Amma
ilimin Aqali shi ne, ilimin Falsafa da Handasa da
Ilimin sihiri da na Labarin Qasa da Tarihi. To irin
wannan ilimin shi kuma ya fi yawa ga
shugabannin jihadi kamar Sarkin Musulmi Bello
da „yan‟uwansa, kuma shi ya sa suka zama
malaman tarihin qasar Afirka ta yamma gaba
xayanta a zamaninsu. Bayan iliminsu na shari‟a da
shauransu.

TARIHIN MALAMAN WANGARAWA
   Tun da yake an yi da‟awar cewa malaman
Wangarawa sun rubuta littattafai na tarihin qasar
Hausa amma Fulani sun kona, bari mu bi kaxan            14
Kano Qwaryar Qira…...

cikin tarihin zuwan su Wangarawan qasar Hausa,
mu ga wasu daga cikin abubuwan da suka yi na
ilimi, mu ga ko akwai rubutun tarihi a ciki; ko
babu. Tarihin Arbab Hazal-baladi, wato tarihin
Kano, ya yi bayanin zuwan Malaman Wangarawa
a zamanin Sarkin Kano Ali Yaji A.D. 1349-1385,
kamar haka:
    “A cikin zamanin Yaji ne Wangarawa
    suka zo daga Malle, suka kawo
    Musulunci. Babbansu Abdulrahmani
    Zaite, da kuma Yakubu, da
    Mandawari, da Famure, da Balkasim,
    da Kanaji, da Dukure, da Sheshe, da
    Kebe, da Mutuku, da Limamin Jujin
    „Yan-labu uban Sarkin Pawa, da
    Kurdumasa, da Auta, da Lawan, da
    Limamin Madatai da waxansun su na
    cikin arbabi. Yayin da suka zo suka
    umarci Sarki da sallah, sai ya yi. Suka
    sanya Gurdumus limaminsa, Lawan
    ladaninsa, Auta mai yanka dukkan
    naman da ake ci, Mandawari limamin
    dukka Wangarawa tare da manyan
    Kanawa, Zaite aka sa shi alqali”.

  To tun daga wancan lokacin malaman
Wangarawa suka ci gaba da ayyukansu na alheri a            15
            …………….Daga Dutsen Dala

Kano da sauran qasashen Hausa. Suna yaxa
addini, da ba da ilimi, da limanci, da alqalanci da
sauran abubuwan da suka shafi wayewar kai na
xa‟a da halayen musulunci, amma ba nishaxin
rubuta tarihin qasa ba.
    Amma duk da haka bari mu bi tarihin da
suka rubuta da kansu, na zuwansu Kano da sauran
qasashen Hausa, domin mu ga ko gaskiya ne su
masu kula da tarihin qasa ne har ma suna rubuta
shi, ko kuwa arar bakinsu aka yi aka ci musu
albasa?
    Malaman Wangarawa sun rubuta tarihin
zuwansu Kano da sauran qasashen Hausa wanda
ya sava da wanda tarihin Kano ya faxa a sama. A
cikin littafin da suka rubuta tarihin zuwansu Kano,
mai suna: Warqa Makatuba Fiha Asalul-
Wangariyyina Al-muntasibina, sun ce sun zo
Kano ne a zamanin Sarkin Kano Muhammadu
Rumfa (1463 – 1499), a lokaci guda da zuwan
Shaihu Maghili Kano. Amma ba su rubuta wannan
littafin na tarihin su ba, sai a zamanin Sarkin Kano
Kukuna (1651). Wato sai bayan sun yi wajen
shekara xari biyu a Kano sannan su ka rubuta
tarihin su, idan ma an bi da‟awarsu ta cewa
zamanin Rumfa suka zo. Idan kuwa aka bi zancen
littafin tarihin Kano to sai bayan shekara xari uku
suka rubuta tarihin su. To mai wannan irin hali na            16
Kano Qwaryar Qira…...

rashin kulawa da tarihin kansa, shi ne za‟a ce ya
rubuta tarihin waxansu amma masu jihadi sun
qona, wai don labarin kafirai ne? Wannan littafi na
Wangarawa yana nan a Kano ana amfani da shi
tun wancan lokaci har zuwa yau. Kuma daga
wannan littafi ba wani abu na tarihin qasar nan da
aka ji Malaman Wangarawa sun rubuta.

MALAMAN TARIHIN KANO
    Duk da cewa kaji bayanin da muka yi akan
rashin kula da tarihi a wancan lokaci, wannan
baya nufin cewa babu masu qoqarin rubata tarihi.
Domin kuwa kafin Jihadin Shehu Usmanu ya
bayyana akwai shahararrun malamai na tarihi a
nan Kano, kamar su Malam Ishaqa (Isyaku) xan
Malam Muhammadu Gabi. An ce wannan malami
shahararre ne a Kano wajen sanin tarihi. Bayan
Ishaqa kuma akwai Malam Muhammadu Falaki da
kuma Limanin Fanisau da kuma Malam
Muhammadu Male, waxannan malamai su ne jiga-
jigan tarihin Kano kamar yadda na ji musamman
ma tarihin jihadi, amma har yanzu ban sami
littafin ko malamin xaya daga cikinsu ba.
    Yanzu bari kuma mu karkata akalarmu
wajen bayanawa mai karatu littattafan da muka
dogara da su wajen binciko tarin qasar Kano
sahihi.            17
           …………….Daga Dutsen Dala

(1)   MALAM MUHAMMADU ZANGI
    Ban da waxannan malamai da aka ambata a
sama akwai kuma Malam Muhammadu Zangi xan
Alqalin Kano Malam Salihi, na qabilar Jollave
(Gyanawa). Shi Malam Muhammadu Zangi shi ne
Alqalin Kano na uku bayan jihadi, kuma ya gaji
mahafinsa ne Malam Salihi a alqalanci tun daga
zamanin Sarkin Kano Usman xan Dabo (1846-
1855) har cikin zamanin Sarkin Kano Abdullahi
Maje-Karofi (1855-1882). Shi alqalin Kano Zangi
da iyayensa aka yi jihadin Kano, a sannan shi yana
yaro qarami, kuma ya yi karatu a wajen su Malam
Isyakun nan da muka ambata a baya. Kamar yadda
yake a al‟ada ga sarakuna sukan sa malamansu su
rubuta tarihin qasa tasu, haka Sarkin Kano
Abdullahi Maje Karofi ya sa Alqalin Kano Zangi
ya rubuta tarihin jihadin Kano, da malaman da
suka yi da qabilarsu, da kuma sarakunan Fulani
waxanda suka yi sarauta bayan jihadin. Alqali
Zangi ya rubuta tarihin Kano, kamar yadda Sarkin
Kano Abdullahi ya umarce shi, kuma ya kira
littafin da suna TAQAYIDIL-AKHBARI. Wato
TAQAITACCEN LABARIN JAMA‟AR SHEHU TA
KANO. Xaya daga cikin dalilan da suka sa Sarkin
Kano Abdullahi ya sa Alqalin Kano Zangi ya
rubuta tarihin Jihadin Kano shi ne ganin manyan
malaman da suka yi jihadin sun kusan qarewa            18
Kano Qwaryar Qira…...

saboda haka ya ji tsoron kada su qare duk ba a
samu tarihin abin da ya faru ba, don haka na baya
su zo su ringa yin musu da jidali akan abin da ba
su sani ba, kamar yadda Yahudawa da Nasara
suke jidali akan Annabi Ibrahima, waxannan su ce
Bayahude ne, waxancan su ce Banasare ne, wato
suna jifa a cikin duhu, duk daga qarshe Allah ya
qaryata su.
    Wannan littafi da Alqalin Kano Zangi ya
rubuta shi ne abin da na dogara da shi wajen
tarihin jihadin Kano. Ko da yake na bi waxansu
littattafan da kuma labarin manyan mutane, amma
duk da haka wannan littafi na Alqali Zangi shi ne
muhimmi akan tarihin jihadin Kano da na
sarakunan Fulani na farko.

(2)   LITTAFIN TARIHIN KANO
    Wannan littafi asalin sunansa Tarikhil
Arbab Hazal Balad al-musamma bi Kano an
rubuta shi zamanin Sarki Kano Bello xan Dabo.
Ba‟a faxi sunan malamin da ya rubuta wannan
littafi a zamanin Sarkin Kano Bello ba. Amma an
fi zaton Malam Yusufu shafannoni ne ya yi
rubutun. Shi Malam Yusufu mutumin Tsangaya ne
ta qasar Gaya. Sarkin Kano Bello ya shigo da shi
cikin birni ya bashi gida a Marava, bayan gidan
Sarki daga gabas, ya zama Malamin sa. An samar            19
           …………….Daga Dutsen Dala

da wannan littafi ne domin a shigar da tarihin
Sarakunan Fulani daga kan Sarkin Kano
Sulaimanu zuwa Sarkin Kano Usman na xaya.
   Wannan bayani ya kore abin da Mr. Palmer
ya rubuta a cikin littafin sa na turanci – Kano
Chronicle, (fassarar Tarikhil Arbab Hazal
Balad…) inda ya yi da‟awar cewa wai wani
balarabe ne, ya rubuta littafin. Wannan da‟awa
bata da tushe ko kaxan, domin Sarkin Kano Bello
bai saki jiki da larabawa ba, balle ya amince musu
har su rubuta masa wani abu na tarihin Kano.
Yaqin da aka yi na basasa inda larabawa suka goyi
bayan „ya‟yan Abdullahi Maje Karofi maimakon
na Bello shi ya nuna rashin kulawar Bello da
larabawa.

(3)  MALAM MUHAMMADU TUKUR
   Wannan malami mutumin Zogarawa ne ta
Dawakin Kudu, kuma malamin Sarkin Kano
Tukur ne. Da Basasar Kano ta tashi tsakanin
Yusufawa da Tukurawa sai ya goyi bayan Sarkin
Kano Tukur. Har ma aka ce Sarkin Kano Tukur ya
naxa shi Alqali. Wataqila a cikin wannan hali na
Basasa ne ya rubuta littafinsa mai suna FA‟IDA
KADIR FI AUSAF AL-MALIK AL KHARIR. A
cikin wannan littafi Malam Muhammadu Tukur ya
ba da nasa labarin game da Basasar Kano wanda            20
Kano Qwaryar Qira…...

ya sha bamban da labarin Yusufawa. Koda yake a
lokacin da na karanta wannan littafi na samu
takardu biyu daga cikin littafin sun vata, wato
shafuka huxu ke nan, amma duk da haka akwai
isasshen labarin Basasar daga ra‟ayin Tukurawa.

(4)  WAZIRI MUHAMMADU BUHARI
    Wazirin Sakkwato Muhammadu Buhari shi
Sarkin Musulmi Abdu Xanyen-kasko ya aiko
Kano don ya naxa Tukur xan Bello Sarkin Kano,
maimakon Yusufu xan Abdullahi Maje Karofi.
Don haka shi Waziri Buhari shi ne ya shiga cikin
rigimar Basasar Kano tsundum daga farkonta har
qarshenta. Saboda wannan ne ya rubuta littafinsa
mai suna Kitab fi ma jara baini wa baina Amir
Hadejia wa Yusufu. A cikin wannan littafi ne
Wazirin ya bayyana abin da ya gudana tsakaninsa
da Sarkin Kano Yusufu da kuma Sarkin Hadeja
Muhammadu Mai Shahada wanda ya zo taimakon
Yusufu a lokacin Basasa amma Wazirin ya hana
shi shiga cikin lamarin.

(5)  MALAM ADAMU NA MA‟AJI
    Malam Adamu xan Malam Muhammadu
Mai Xinkin takalmi na unguwar Alfindiki ne ta
cikin Birnin Kano, kuma iyayensa Larabawa ne
mutanen Ghadamus (Libya). Abin da ya sa ake            21
            …………….Daga Dutsen Dala

masa laqabi da Malam Adamu Na Ma‟aji shi ne
saboda qanin mahaifinsa, Ma‟aji Babale shi ne
Ma‟aji a lokacin Sarkin Kano Abbas (1903-1919).
Malam Adamu almajirin Ma‟ajin Kano Sulaimanu
ne xan Limamin Kano Isma‟ila. Saboda haka
littafin da ya rubuta a kan tarihin Kano, mai suna
AL I‟ILANI BI TARIHI KANO, ya saka sunan
Ma‟aji Sulaimanu a farkon littafin don
girmamawa. Malam Adamu shi ne kaxai a cikin
malaman Tarihin Kano wanda ya yi amfani da
fannonin ilimi, irin su ilimin taurari da na Jafriyya
wajen rubuta Tarihin Kano, don kuwa shi ya haxa
ilmin Naqali da ilmin Aqali a kansa. Ya rubuta
wannan littafi ne daga farkon sarautar Sarkin
Kano Usman (1919-1926) zuwa farkon sarautar
Sarkin Kano Abdullahi Bayero (1927-1953). Haka
kuma ya sake rubuta wani littafin mai suna Al-
Asar Al-Kanawiya wanda a cikinsa shi ma ya yi
bayani a kan tarihin Kano da sarautar Sarkin Kano
Sulaiman da labarin Sarkin Kano Al-Wali da
xansa Chiroma xan Mama.

(6)  MALAM ABUBAKAR DOKAJI
   Malam Abubakar xan Wazirin Kano Gixaxo
ne, kuma shi ma ya yi Wazirin Kano daga 1960-
1972. Kamar yadda Sarkin Kano Abdullahi Maje
Karofi ya sa Alqalin Kano Zangi ya rubuta tarihin             22
Kano Qwaryar Qira…...

jihadi haka ma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi
(1953-1963) ya sa Malam Abubakar Dokajin
Kano ya rubuta tarihin Kano wanda ya sa wa suna
KANO TA DABO CI GARI. Shi wannan littafi da
Hausar boko aka rubuta shi, a cikinsa akwai
lissafin duk sarakunan Have da sunayensu. Shi
Malam Abubakar abokin Malam Adamu na Ma‟aji
ne tun shi Malam Abubakar xin yana xalibta a
Makarantar Kwaleji ta Katsina. Don haka ne shi
ma Malam Abubakar yake da ilimin taurari da na
hisabi.

(7)  WAQAR BAGAUDA
    Wannan waqa an rubuta ta a cikin zamanin
Sarkin Kano Abbas bayan ya shekara goma sha
huxu da sarauta, wato a cikin 1916 ke nan.
Manufar wannan waqa wadda makafi suke yin
bara da ita kwararo-kwararo, kuma matan aure
suna yin niqa da ita, shi ne ta koya wa yaran Kano
sanin tarihin sarakunansu na Kano, tun daga
zamanin Bagauda har kan Sarkin da yake sarautar
Kano a wannan lokacin. Ita wannan waqa
malaman Kutumbawa ne suka rubuta ta. An ce
wanda ya rubuta ta wani malami ne Bakutumbe,
mutumin qasar Rano, mai suna Malam Ahmadu.
Amma an buga ta ta zama littafi ba a faxi sunan
            23
           …………….Daga Dutsen Dala

mawallafin nata ba, sai dai sunan kamfanin da
ranar buga ta da kuma garin da aka buga ta.

(8)  MALAM UMARU BA-KABE
  An haifi Malam Umaru xan Malam Abubakar
Ba-kabe a Unguwar Tudun Maqera ta cikin birinin
Kano, a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Maje
Karofi (1855 – 1882), bayan Sarkin yayi shekara
uku da cin sarauta. Yayi karatun Alqur‟ani da na
ilimi a hannun mahaifinsa Malam Abubakar
Bakabe, da kuma makarantar Malam Muhammad
Taqiqi xan Malam Lukuti, a Unguwar Magoga ta
cikin birni.
  Da mahaifin Malam Abubakar ya rasu shi
kuma sai yayi niyya ya bar Kano ya tafi Sakkwato
domin qara ilimi. Bayan yayi wata biyu a
Sakkwato Sarkin Kano Abdullahi ya rasu a Karofi
ta Katsina, aka naxa Sarkin Kano Bello a
Sakkwoto, a idanun Malam Umaru, a lokacin yana
xan shekara ashirin da biyar da haihuwa. Ya ci
gaba da neman ilimi da fataucin Gwanja da
Dagomba har ya zauna yayi ka-ka gida a garin
Kere –Krachi ta qasar Togo, inda ya zama
Limamin garin, kuma shugaban qungiyar
Kanawan Togo, ta haka ne ya zama abokin wani
babban jami‟in mulkin mallakar Jamusawa na
qasar Togo mai suna A. Mischilch.           24
Kano Qwaryar Qira…...

  Malam Umaru xan Malam Abubakar Bakabe,
shi ne Bakano na farko da ya rubuta tarihin Kano,
da na Sakkwoto, da na Zamfara, da na Kebbi, da
na Gwanja da Dagwamba da harshen Hausa
(rubutun ajami).
  Wannan littafi na sa shi turawan Jamus suka
xauka suka fassara shi cikin harshen Jamusanci da
na Ingilishi suka sa masa suna Hausa Prose
Writing in Ajami by Alhaji Umaru: From A.
Mischilch H. Solkens Collection, 2000. Dietrich
Preimer Verlang Berlin.
  Malam Umaru ya rasu a Kere – Krachi ta Togo
a ranar 30 ga watan yuni 1934, bayan yayi wajen
shakaru tamanin a duniya. Wannan littafi na
Hausa Ajami akwai shi a hannun mawallafin
wannan littafi.

WAHALAR KARATUN LITATTAFAN
MALAMANMU
   Rashin samun rubutattun tarihe-tarihen
qasar nan masu yawa, ba shi kaxai ne wahalar da
mai rubuta tarihin qasar nan ya ke fama da shi ba,
a‟a ko da karanta „yan qalilan xin littattafan da
wasu daga cikin malaman namu suka rubuta shi
ma wahala ce mai ximbin yawa. Na farko dai irin
waxannan littattafai a cikin harshen Larabci aka
rubuta su, shi kuma Larabcin ba lafdin sharqiyya            25
           …………….Daga Dutsen Dala

ba ne, wato ba Larabci ne irin lahajar Misra ta
Gabas ta tsakiya ba. Da yawa littattafan da
malamanmu suka rubuta, sun rubuta su ne da
lafdin “Magharib” wato lafdin da ake ce masa
lafdin Tumbuktu. Qasashen Maghrib dai su ne
Maroko da Tunusiya da Tirifoli (Libya) da Biladi
el-Shangil (Mouratenia). Rubutun Magharib yana
da wuyar fahimtar harufansa da jimlolinsa. Idan
mutum bai yi zurfi a cikin nahawu ba, ba zai iya
karanta irin waxannan littattafai ba, balle ya
fahimce su. Galibi kuma malaman sukan gauraya
Larabci da ajami wajen rubuta littafi, koda yake
suna yi wa duk wata kalma ta ajami, wadda suka
yi amfani da ita, wasali don a gane bambancinta
da kalmar Larabci, wani lokacin ma sukan faxi
yadda ya kamata a karanta wata kalma ta ajami,
misali, kalmar KANO sai su ce a yi wa harafin Ka
fataha, a yi wa harafin Na rufu‟a, sannan a ja Wa
wato ya zama KANO ke nan. To wannan fa shi ne
dalilin da ya sa marubuta tarihin qasar nan
waxanda ba su san Larabci ba musamman Turawa
suke ta bilinbituwa, suna kame-kame wajen rubuta
tarihin qasar nan, domin ba za su iya karanta
littattafan iyayenmu da kakanninmu ba, ballantana
su iya fahimtar abin da yake ciki na tarihi, su yi
amfani da shi.
            26
Kano Qwaryar Qira…...

    Marigayi Sardaunan Sakkwato Mai girma
Sir Ahmadu Bello ya tava yin irin wannan
maganar a cikin wata wasiqa da ya yi wa Mr.
Hogben a kan wani littafi da shi Mr. Hogben xin
ya rubuta. Sardauna ya ce littafin da Hogben ya
rubuta akan tarihin qasar Hausa zai yi wa yaran
qasar nan amfani, kafin su ma su taso, su karanta
tarihin iyayensu da kakanninsu, wanda suka
rubuta masu da Larabci, da Hausa da Fulfulde, su
ma su rubuta tarihin Arewa na qwarai. Ya ce
domin rubuta tarihin Arewa sai xan arewa.

GUDUMMAWAR TURAWA GA
TARIHIN QASAR NAN
   Tun kafin Turawan Ingilishi su zo su ci
qasar Hausa, suka sami labarin cewa qasar Hausa
qasa ce mai asali da tarihi kuma harshen Hausa
rubutacce ne kamar harshen Larabci da sauran
harasa masu asali. Turawa sun sami wannan labari
ta hannun matafiya irin su Major Clapperton da
Henry Barth, da marubutan tarihin qasar
Tukururu, wato qasar Sudan ke nan ta Hausawa.
Da Ingilishi suka ci qasar nan sai suka sami
abubuwa masu ban sha‟awa na zaman duniyar
Hausawa. Sun sami tsarin sarauta mai kyau; Sarki
da hakimansa da dagatansa da „yan majalisa tasa,
kuma da sarakunan yaqinsa. Sun sami tsarin            27
           …………….Daga Dutsen Dala

alqalai da majalisun shari‟a, da tsarin makarantun
allo da kuma malamai masu ba da ilimi a
makarantun kansu. Haka kuma Turawa suka tarar
da sarakunan Hausa suna da magatakarda a
kowace majalisar sarki wanda aikinsa ne karatu da
rubutun takardun da sarakuna suke yi wa junansu,
har ma wasiqun da suke tsakaninsu da Turawan
kamfani. A taqaice dai Turawa sun sami qasar
Hausa da ilimi da ci gaba, da mu‟amula da
qasashen duniya musamman qasar Santambul
(Turkey). Wannan abu ya bai wa Turawa sha‟awa
da gaske, don haka sai suka xauki niyyar gane
tarihin qasar Hausa ta hanyoyi biyu:

  1.  Hanya ta farko ita ce xora wa kowane
     Baturen da za a aiko Arewa don aikin
     mulki (D.O.) cewa dole ne a gare shi ya
     koyi harshen Hausa, da xabi‟un
     Hausawa kafin ya iso arewa ya fara aikin
     mulki.

  2.  Hanya ta biyu ita ce roqon sarakuna akan
     su sa malaman qasarsu su fassara tarihin
     kowane lardi na arewa cikin Hausa, don
     Turawa su san yadda za su yi amfani da
     shi a cikin harshen Turanci.
            28
Kano Qwaryar Qira…...

  To waxannan abubuwa su ne suka sa sarakuna
suka himmatu wajen sa wa a fassara tarihin
qasashenmu daga Larabci zuwa Hausa don mafi
yawan mutane su karanta shi da Hausar boko. An
fassara manyan littattafai kamar su INFAQUL
MAISURI in da Sarkin Musulmi Muhammadu
Bello ya ba da tarihin dauloli da sarakunansu na
qasar Sudan ta Hausawa, wato tarihin sarakunan
Ghana da Mali da Songhai da Borno. Haka kuma
malaman Arewa suka fassara tarihin Borno wato
Girgam da labarin yaqe-yaqen Sarkin Borno Idrisu
Aloma, suka fassara tarihin Kano wanda Mr.
Palmer ya juye shi a cikin Turanci kuma ya sa
masa suna Kano Chronicle. Kafin 1933 wannan
nishaxi na fassara ya haifi wasu mashahuran
littattafai guda biyu, wato Labarun Hausawa Da
Maqwabtansu littafi na farko da na biyu. Littafi na
farko ya qunshi labarun Hausa Bakwai da Banza
Bakwai har zuwa labarin qasar Bade. Littafi na
biyu ya qunshi labaru tun daga tarihin Kano har
qarshen tarihin Adamawa. To waxannan littattafai
su ne manyan littattafan da aka dogara da su,
kuma ake yin amfani da su wajen buxe tarihin
qasashen Arewa, a makaratun boko. Amma
littattafan tarihin qasar nan waxanda aka rubuta da
harshen Larabci suna nan a voye, har yanzu ba a
tono da yawa daga cikin su ba. Muna fata mutane            29
            …………….Daga Dutsen Dala

masu zuwa a nan gaba za su yi matuqar qoqari su
tono su don tarihin qasar nan ya yalwata.
    Abin takaici a cikin wannan al‟amari na
waxannan Turawa na farko shi ne duk abin nan da
aka yi na fassara tarihi sai suka buga shi, suka sa
sunayensu a kai wato su ne ke nan suka wallafi
littattafan, domin ba sunan mawallafi ko wanda ya
fassara da Hausa ko na sunayen sarakunan da suka
sa a yi wannan. Amma yanzu an gane wannan abu
kuma ana gyarawa.

LABARIN TSOFAFFI
    Ban da waxannan littattafai da na yi amfani
da su wajen rubuta wannan littafi na yi amfani da
labarin da tsofaffi suke bayarwa na tarihin gari
wanda ake samun sa daga iyaye da kakanni.
    Su irin waxannan labarai da ake ji a wajen
tsofaffi yau da kullum sukan taimaka qwarai da
gaske wajen bayyana abin da littafi ya faxa game
da tarihin gari ya qara wa littafin gaskiya, ko kuma
ya qaryata shi gwargwadon sani ko rashin sanin
marubucin tarihin gari. Amma kuma raunin irin
waxannan labaru na tsofaffi ga me da tarihin gari
shi ne qarin gishiri, ko son kai wajen ba da tarihin
mutanen gari da yaqe-yaqe da nasara tasu ko
faxuwa tasu a cikin rayuwa tasu ta tarihi. Domin
kowace qabila so take a ji ta bayyana alfaharin            30
Kano Qwaryar Qira…...

tarihinta, ba tare da kulawa da tarihin wata qabilar
ba. Haka kuma ba kasafai irin waxannan labarai
suke bayyana gazawar qabilar su ba.
    Amma duk da wannan na zavi wasu labarun
tsofaffin na mutane daban-daban waxanda na
yarda da su kuma na kawo su cikin wannan littafi
kamar yadda na ji su daga bakin waxanda suka
gaya mini kamar haka:
  1.   Labarin gidan Dabo na ji shi daga
      zuriyar Danrimin Kano Al-barka, su ne;
      Alhaji Abubakar Sadauki (Wakilin
      Panshekara) da kuma Alhaji Abubakar
      xan Xanrimi Allabar sarki.
  2.   Labarin gidan Gebi da Xantunku na
      Yarimawan Xanbatta da Kazaure, na ji
      shi daga bakin Alhaji Umaru Xanbatta
      (Wakilin gona), na gidan Gebi, da kuma
      Waziri Ala (Masinjan D.O.), na gidan
      Xantunku.
  3.   Labarin Ningi na ji shi daga bakin Sarkin
      Ningi, Alhaji Inusa Muhammad
      Xanyaya da kuma Sarkin Rano
      Abubakar Xan-Ila jikan Sarkin Rano
      Jibir.

  4.  Labarin Hadeja na samo shi daga wajen
     Tafidan Hadeja Alhaji Abubakar            31
          …………….Daga Dutsen Dala

   Maigari daga littafin da ya rubuta na
   tarihin Hadeja (ba a buga littafin ba).
5.  Labarin Gumel na same shi daga Sarkin
   Gumel Muhammadu Sani da Wazirinsa.
6.  Labarin Damagaram na ji shi daga bakin
   Madawakin    Damagaram     Malam
   Ahmadu a gaban Sarkin Dagamaram
   Omar Sanda xan Ahmadu xan Bassa
   (1950-1978).
7.  Labarin cinikin Gwanja da Agalawa na ji
   shi daga wajen Madugu Jaji na Adakawa
   cikin Birnin Kano.
8.  Labarin Larabawan Turabulus (Libya)
   da cinikinsu na Sahara na ji shi daga
   wajen Mahadi Ganaba na Fagge ta
   Arewa da kuma Salim Ahmad xan Bil-
   Aluwa na Fagge ta Kudu.
9.  Labarin cinikin Larabawan Chadi da
   Sarkin Zango na ji shi daga bakin Alhaji
   Bature jikan Sarkin Zango malam
   Maikano.
10.  Labarin rigimar Dutse da Kila da kuma
   abin da ya faru tsakanin Sarkin Kano
   Bello da dagatan nan nasa kamar Sarkin
   Jahun Moddibo da Sarkin Dutse
   Sulaiman da Sarkin Gaya Abubakar Mai
   juni-juni da sauransu na ji shi ne daga          32
Kano Qwaryar Qira…...

     wajen wani malami wai shi Malam Sule
     mutumin Jahun a wajen Wakilin Gona
     Alhaji Umaru Xanbatta.

  Waxannan mutane da na lissafa a sama ba su
ne kaxai na ji labarin tarihin Kano da na sauran
qabilu a wajensu ba, na ji ma a wajen mutane da
yawan gaske amma na kawo waxannan ne kawai
domin misali.
            33
           …………….Daga Dutsen Dala

       SASHI NA XAYA

        ASALIN HAUSAWA:
  DAGA MISRA, KO DAGA BAGADAZA?
    An sami savani akan bayanin tarihin
Hausawa, tsakanin Malaman nazarin tarihi, da
rubuta shi, da kuma masu tarihin baka na
tatsuniyar Bayajida, mijin sarauniya Daurama.
Wannan tatsuniya ta kawo duhu a cikin tarihin
Hausa bakwai da banza bakwai tun lokacin da aka
qirqireta, har zuwa yanzu.
    Amma a cikin mutanen da suka nazarci
tarihin asalin Hausawa daga littattafan tarihin
Misra, Lugard(1) a cikin littafinsa (A tropical
Dependency) ya ce Hausawa daga qabilar
qibxawan Misra suke. Sunansu da sunan
harshensu, an same su ne daga sunan Fir’auna
Hausal kakan Fir‟auna Namrudu, na qabilar bani
Kan‟ana. Shi kuma Fir‟auna Namrudu shi ne;
jikokinsa suka kafa qasar Hausa da Mulkinta na
Daura domin haka ake yi wa sarakunan Daura
kirari da jikokin Lamarudu har yau xin nan.
    Tarihin Masar qunshe yake da bayanai
waxanda suka nuna tsohuwar dangantaka tsakanin
mazaunan bakin kogin Niger da mazauna bakin
kogin Nilu (Qasar Masar da Habasha da qasashen
Hausa). Fahimtar wannan dangantaka tana buqatar           34
Kano Qwaryar Qira…...

nutsuwa wajen karanta tarihin Masar na gargajiya,
wanda manazarta suka tara, suka rubuta, suka
adana shi. A cikin wannan nazari an ce Fir’auna
Hausal da zuri‟a tasa, sun yi mulki a Masar. An
gaya mana cewa ma‟anar Hausal bawan Venus
(wata tauraruwa) kenan. To, wannan bayani ma
iya danganta shi da shekarun da Phoenicians
(Banu Kan‟ana) suka mallaki Masar suka kawo
bautar Venus har ta mamaye qasashen da suke
kewaye da kogin Nilu. Abin lura a nan shi ne ko
kafin Fir‟auna Hausal ya yi sarauta, sarakunan
Misra sun saba zuwa qasashen baqar fata na
yamma da su inda suke ganin abubuwa masu ban
mamaki, a cikinsu.
    Amma daga zamanin jikansa ne Fir‟auna
Lamarudu, wanda ake yiwa kirari da “Lamarudu
Toron Giwa, Lamarudu xan Hausal”, muka sami
cikakkiyar dangantaka tsakanin Misra da qasashen
yammacinta, musamman qasashen Hausa. Nazarin
ya bayyana mana Lamarudu a matsayin
shahararran sarki, kuma adali wanda a zamaninsa
Misrawa suka sami zaman lafiya. Amma sai ya
sami matsala daga baya. Wani xan wansa wanda
ya rasu yana auren wata mace matsafiya sai ta
gudu da xanta, bayan Lamarudu ya hau gadon
sarauta, ta yi kudu da shi. Anan ta yi amfani da
tsafinta tasa xan ya zama sarki shi ma. Da            35
            …………….Daga Dutsen Dala

Lamarudu ya sami labari, sai ya xaura yaqi ya bi
ta, amma bai yi nasara ba, xan ya ci gaba da zama
sarki. Wannan shi ne abin da tarihin Misra ya
faxa.
    Amma Yarabawa waxanda suke cikin banza
bakwai sun ce su ma daga Bani Kan‟ana suka fito
wato Phonecian ta qabilar Lamarudu. Suka ce duk
qabilun da suke zaune akan duwatsu a qasar arewa
„yan uwansu ne, suke barinsu a gurin, lokacin da
suka gudo zuwa inda suke a yanzu. To, wannan
danganta tsakanin „ya‟yan matsafiya da „ya‟yan
Fir‟auna Lamarudu wataqila ita ce asalin Hausa
bakwai da banza bakwai. „Ya‟yan Fir‟auna
Lamarudu suka zama Hausa Bakwai, „ya‟yan xan
uwansa na matsafiyar suka zama banza bakwai
tare da Yarabawa. Wannan bayani zai fi karvuwa
fiye da bayanin Hausa Bakwai da Banza Bakwai
na tatsuniyar Bayajida.
    A nasa bayanin kuma game da alaqar qasar
Hausa, da Misra, sarkin musulmi Muhammadu
Bello ya faxa a cikin littafinsa; Infaqul-Maisuri fi
Biladil-Tukururi(2) cewa qasar Hausa ita ake kira
Biladil-Tukururi, a qasashen Misra, da na
Habasha, da Makka, da Madina, tun asali. To, idan
ka haxa wannan taqaitaccen bayani da abin da
zaka karanta a cikin wannan littafi na game da
hukumar Kano ta farko, wato hukumar Dala,            36
Kano Qwaryar Qira…...

wacce aka ji labarinta a hijirar Annabi Isa ta
shekara xari uku (300), bayan fakuwa tasa, da
hukuma ta biyu hukumar Maxatai wacce ita ma
aka ji nata labarin a Hijira ta xari biyar (500)
bayan fakuwarsa, zaka ga cewa mulkin Daura na
Hausa bakwai da banza bakwai zai yi aqalla
shekara dubu biyu (2,000) kafin a qirqiri
tatsuniyar Bayajida, da saurauniya Daurama.
    Wannan ra‟ayi Hambali Jinju(3) ne ya
qiyasta shi a cikin littafinsa, Garkuwar Hausa.
Wannan qiyasi na jinju ya yi kama da abin da
tarihin Misra ya faxa na game da zuwan Fir’auna
Barkhou tare da mayaqansa 700,000(4) qasar
Hausa a hijra ta 1,500 kafin haihuwar Annabi Isa,
inda Fir‟aunan ya zauna kimanin shekara goma
sha xaya, yana yawo a cikinta, kudu da arewa
gabas da yamma, saboda samun bayi, da dinare,
da tagulla, da dabbobin daji da shauran abubuwa
masu amfani waxanda babu su a Misra, da shauran
qasashen gabas, kafin ya koma Misra. Qaburburan
Fir‟aunonin Misra (Pyaramids) da gurin bauta tasu
(Temples) duk da gumin baqar fatar Afirka ta
yamma aka gina su.

Bayanin labarin baka na Bayajida
   Masu labarin baka akan tarihin asalin Hausa
bakwai da banza bakwai, sun dogara ne akan abin            37
            …………….Daga Dutsen Dala

da tatsuniyar Bayajida ta qunsa akan tarihin
Daura. Tatsuniyar ta danganta asalin Sarakunan
qasar Hausa da garin Bagadaza, ta cewa wai wani
mutum mai suna Abayajida(5) (Abu Zaidu), xan
Abdullahi sarkin Bagadaza shi ne ya yi faxa da
Ubansa, ya gudo qasar Hausa tare da mayaqansa
masu yawa. Amma ya yi xan zama a Borno har
sarkin Borno ya yaudare shi, ya aurar masa da „ya
tasa, Magira, ta haka ya qwace masa mayaqa, ya
nemi kashe shi. Mata tasa Magira ta sanar da shi
suka gudu tare, tana da tsohon ciki a lokacin ya
barta a Garun Gabas ta haifi xa Namiji, aka sa
masa suna Biram. Shi ne xan Bayajida na fari.
    Wai sai shi kuma Bayajida ya qarasa Daura
da daddare, ya sauka a gidan wata tsohuwa wai ita
Ayyana. Ya nemi ruwa zai baiwa dokinsa, ta ce da
shi ba za‟a sami ruwa a wannan ranar ba, domin
rijiyar da ake samun ruwa a ita, akwai macijiyar
da suke bautawa mai suna Sariki, wacce in ta ji
motsin guga take biyo shi ta fito ta kashe mutumin
da ya zura gugan. Ya ce ta bashi gugan shi zai
xebo ruwan. Ta bashi gugan, ya tafi ya zura a
cikin rijiyar, macijiyar ta biyo za ta kashe, sai ya
sareta da takobinsa, ya yanke kanta ya saka a
aljihu, ya xibi ruwansa, ya koma gidan Ayyana, ya
baiwa dokinsa ruwan, ragowar ya baiwa Ayyana.
            38
Kano Qwaryar Qira…...

    To, wannan bajinta ita ce ta ruxa duk garin
Daura da gari ya waye, mutane suka ga an kashe
tsafin da suke bautawa, macijiya Sariki. Labari ya
je kunnen Sarauniya Daurama, ta zo ta gani, ta
tambayi mutane wanda ya yi wannan aiki domin ta
raba garin ta bashi rabi. Kowa ya fito ya yi
da‟awar shi ne sai a qure shi; in an ce ya kawo kan
sai ya kasa. Anan ne Ayyana ta ce da sarauniya
akwai baqo a gidanta wanda ya je rijiyar jiya da
daddare, ya xebo ruwa ya shayar da dokinsa, har
ni ma ya bani. Sarauniya ta ce ta je gidan tazo da
shi. Ayyana ta koma gida tazo da shi Sarauniya ta
tambaye shi ko shi ne ya kashe Sariki. Ya ce i shi
ne, ta ce ya kawo kan a gani da ya kawo sai
Sarauniya ta ce za ta bashi rabin gari, ya ce ya fi
son ya aure ta. Ta yarda suka yi aure, ta haifi xa ta
sa masa suna Bawo mo gari. Domin kafin ta haihu
kuyangar Bayajida ta riga ta haihuwa ta sawa
xanta suna Karaf gari, wato mun karvi gari, don
haka ne Sarauniya ta sawa nata xan bamu
garinmu. To, wai wannan xa Bawo shi ne ya haifi
sarakunan Hausa Bakwai, wato Daura da Kano, da
Katsina da Zariya, da Gobir, da Rano. Kuma
akwai xan na fari Biram. Wannan tatsuniyar ta
dangantaka asalin Hausawa da Bagadaza, ta qasar
Labarawa maimakon Misra qasar Qibxawa. Kuma
             39
           …………….Daga Dutsen Dala

akan haka ne zamu warware wannan qulli na
tatsuniyar gizo da qoqi, da waxannan bayanai.

Rashin abin dogaro a cikin tatsuniyar Bayajida
  Wannan taqaitaccen labari na tatsuniyar
Bayajida da aka karanta a baya, babu wani abin
dogaro a cikinsa, wanda zai nuna asalin Hausawa.
Ba ma shi da wata alaqa da tarihin Hausawa na
asalinsu, ko na harshensu, ko na tsarin mulkinsu.
In ban da ambaton sarauniya Daurama da na
macijiya Sariki, da aka yi a cikin tsatsuniyar ba
wanda zai fahimci abin da ake nufin ginawa a
cikin tsatsuniyar saboda waxannan dalilai.

  1. Kafin musulunci ya bayyana Bagadaza
   qauye ne inda gonar sarkin Kisra Anu
   Sharwana take. A nan ne bayinsa da
   barorinsa suke zaune. Bagadaza ba ta zama
   wani abu ba, bayan Musulmi sun ci Iraq(6)
   sai a lokacin mulkin banul Abbas, da
   halifansu na biyu Abu Ja‟afarul Mansur
   (754 – 775) ya gina ta, ta zama birnin
   Bagadaza ya mai da ita kujerar mulkinsa.
   Bagadaza ta samu bunqasa da shahara a
   duniya a zamanin Halifa Harun al-Rasheed
   (786 – 809). A wannan lokacin Bagadaza ta
   fito, ta bunqasa aka santa a duniya baki            40
Kano Qwaryar Qira…...

   xaya, saboda juyin juya hali da musulmi
   suka kawo a wannan fanni na rayuwar xan
   Adam har zuwa hijra ta 878 A.D, wanda
   wataqila a waxannan shekaru ne aka fara
   qirqirar wannan tatsuniya. To, abin
   tambaya a nan shi ne; tun an yi da‟awar
   Bayajida xan Sarkin Bagadaza ne to wane
   Halifa ne a cikin Halifofin Banul-Abbas ya
   zama ubansa? Da Bayajida xan Halifar
   Banul-Abbas ne da Hausawa sun zama
   musulmi quraishawa na Banu Abdul-
   Muxallib bin Hashim, tun lokacin zuwansa
   da aure da ya yi da Daurama. Da kuma
   Shehu Usmanu bai yi jihadi a qasar Hausa
   ba a 1804, domin Hashimawa ne suke
   mulki a lokacin.

 2. Abu Yazidu ko Abu Zaidu, wanda
   Hausawa suka mai da shi sunan Abayajida
   xan sarkin Bagadaza sunayen iska ne ba na
   yanka ba ne. Suna Abu Yazidu sunan al-
   kunya ne a harshen larabci wanda ake voye
   sunan haqiqa, don sakayawa, sai ayi kiran
   mai sunan da sunan xansa, ace baban
   Yazidu. Zaidu kuma sunan misali ne wanda
   ake amfani da shi a darasin ilimin Nahawu.
   Ana sarrafa wasali da shi, ace Zaidun,            41
         …………….Daga Dutsen Dala

  Zaidan, Zaidin. Tsohuwar da aka ce ya
  sauka a gidanta sunanta Ayyana, shi ma
  wannan suna na misali ne ba na yanka ba
  ne. Shi ma yana daga cikin alatun koya
  Nahawu a wajen gina zance, irin waxannan
  sunaye su ne: Ayyana, da Aina da Ainama
  da Kaifama, da sauransu. Ana iya sawa
  kowa suna Zaidu ko Yazidu.

3. Zuwan Bayajida xan sarkin Bagadaza,
  Daura da aurensu da Sarauniya Daurama a
  shekarun da Palmer ya qirqira ya ce an yi
  abin wato 999 A.D. shi ma labarin baka ne.
  Domin kafin wannan shekara ta Palmer
  mulkin Daura wanda jikokin Fir‟auna
  Lamarudu suka kafa tun daga kan
  Sarauniya ta farko, mai suna Kufuru (Sunan
  Fir‟auna Khufu) har zuwa kan Daurama,
  mulkin ya gushe an daina shi, a qalla da
  shekara xari uku (300). Kowacce qasar
  Hausa ta kama gabanta domin babu
  hukumar tsakiya wacce za ta mallake su
  gaba xaya. Bautar Macijiya kuwa Sariki,
  wanda shi ne addinin kakaninsu ya koma
  Dala, a Birnin Kano, inda ake yiwa
  Tsumburbura Haji da Umara a duk shekara,
  kamar yadda za ka karanta a cikin wannan          42
Kano Qwaryar Qira…...

   littafi. To, a cikin wannan sabon bayani
   namu zamu nuna duk babu gaskiyar
   samuwar Bayajida xan Sarkin Bagadaza,
   babu na Ayyana babu na Macijiya Sariki, to
   babu auran Daurama, balle haihuwar xanta
   Bawo. Don haka labarin da yake cikin
   tarihin Daura na Bayajida tatsuniyar gizo da
   qoqi ce ya kamata a ce an gama ta,
   qurunqus kan xan varya.

 Fatarar da aka samu a tsakanin hijrar
 Bagaudan Kano na farko da Bagaudan
 Daura na biyu
   Da yake mun yi da‟awar cewa an samu
 wata fatara a cikin mulkin Hausa a qalla ta
 shekara xari uku, 300 A.D tsakanin lissafin
 sarakuna Hausa na 999. A.D. wato shekarun da
 Palmer ya qirqira da hijrar Bagauda xan
 Farauta ta 500 A.D. wacce ba a san yawan
 sarakunanta ba, to bari mu kasafta shekarun a
 lasafce, domin muga kwatancin lissafinmu ko
 yafi na Mr. Palmer zama daidai. Za dai a
 karanta a cikin wannan littafi cewa waqar
 Bagauda ta „yan Farauta waxanda suka yi
 hukumar Kano ta biyu ita ce ta fito da wannan
 givi inda ta bada bayanin zuwan Bagauda xan
 Farauta da suka koma noma, yunwa ta afku a            43
              …………….Daga Dutsen Dala

   duk qasashen Hausa. Daga baya aka sami
   babban juyin-juya-hali na arziqin qasa da
   bunqasar ciniki da qasashen larabawa har aka ji
   labarin wannan nasara a zamanin Sayyadina
   Umar, (634 – 643). To, daga wannan hijra
   zamu yi wannan lissafi, domin a lokacin zuwan
   musulunci qasar Afirka ta yamma, babu wani
   bayani na hukumar qasashen Hausa ta
   Sarauniya Daurama. Ga yadda na yi wannan
   lissafin:
   a. Na tara lissafin shekarun sarakunan Hausa,
     daga Bagaudan Daura (999AD) har zuwa
     Alwali na biyu (1781 – 1807) a cikin
     littattafai biyar ga bambancin da na samu.

1. Tarihin    Shekaru  = 750
  Kano
2. Taqyidul     =    = 720.6    29.6.
  Akhbar                Bambanci


3. Aliilani     =    = 1,078.2  Bagauda/Ali
                    328 banbanci
4. Waqar      =    = 1,036.0  41.2
   Bagauda              Bambanci

5. Umaru      =    = 750
   Bakabe
              44
Kano Qwaryar Qira…...

   In ka xebe 750 a cikin 1,078.2 ta Bagauda,
za ka sami bambancin shekara 328.2. Waxannan
su ne shekarun fatara tsakanin mutuwar sarauniya
Daurama da labarin zuwan Bayajida xan sarkin
Bagadaza garin Daura a shekara ta 999 AD.

Abin da masu tatsuniyar Bayajida suke son su
faxa, amma aka hana su
   Malaman da aka sa suka rubuta tatsuniyar
Bayajida suna da abin da zasu faxa na tarihin
Hausa bakwai na qwarai, fiye da na tatsuniyar
Bayajida. Amma turawan mulkin mallaka
musamman Mr. Palmer suka yaudare su, suka
saka su tsaya akan tsatsuniyar Bayajida kawai,
kada su xara daga nan, saboda waxansu buqatu
nasu na son kai da qin Allah. Ga kuma abin da ya
kamata malaman su faxa, amma aka hana su.

Hijirar farko ta jikokin Lamarudu daga Masar
   Mutane sun yiwo hijira daga qasar Kan‟ana
(Masar) suka zauna a qasar Palasixinu daga farko.
Daga nan ne wani mutum daga cikinsu, wanda ake
kira Najib (sunan qibxawan Nubiya ne), na bani
Kan‟ana, ya sake yin hijra daga Palasxinu, tare da
duk iyalansa, ya taho yamma ya shigo qasar
Libya, wacce a lokacin tana xaya daga cikin
Lardinan Masar. Anan ya zauna tare da iyalinsa,            45
           …………….Daga Dutsen Dala

shekaru masu yawa. Sai kuma wani mutum daga
cikin „ya‟yansa, mai suna Abdul-Dar (Bawan
Gida) xan Najib shi ma ya sake yin hijra daga inda
suke ya koma kusa da Tripoli (Turabulus). Bayan
ya yi kaka gida a gurin sai ya nemi sarautar
Tripoli, amma mutanen garin suka qi yarda da shi.
Bayan wannan ne Abdul-Dar ya sake yin hijra
yamma tare da duk jama‟a tasa, har ya qaraso
wani tabki mai ruwa (Oasis) mai suna Kusugu,
inda ya zauna, zamansa na qarshe. Wannan gurin
tsohon tabkin Kusugu, shi ne garin Daura na
tsohon birni. Abdul-Dar ya haifi „ya‟yaye, kafin
ya zo Daura, amma duka mata ne, sunayensu su
ne; Bukaiya, da Gambo, da Kafai, da Waizamu da
Daura, wacce ita ce auta tasu. (Hodgkin; 1960).(7)
    Tarihin Daura na yanzu ya qara bayani akan
abin da aka faxa a sama, inda ya bada lissafin
„ya‟yan Abdul-Dari, xan Bani Kan‟ana mata har
guda goma sha shida, waxanda suka yi mulki a
Daura. Takwas na farko daga cikinsu sun yi
mulkin tsohon birni, mil shida arewa da birnin
Daura na yanzu. Wannan tarihi na asalin Hausawa
har yanzu ana tunawa da shi a Daura, inda ake
kaxawa sarakunan Daura tambari, ana yi musu
kirari da „ya‟yan Lamarudu xan Kan‟ana(8). Daga
cikin waxannan sarakuna na Daura na farko,
wacce ta fara mulki a cikinsu an naxa ta da sunan            46
Kano Qwaryar Qira…...

sarautar Fir’auna Khufu ne, amma tarihin Daura
ya kira ta Kufuru(9), kuma duk sunayen shauran
sarakuna da suka biyo bayanta suna da sunansu na
yanka, kuma suna da na sarautar fir‟auna, kamar
yadda yake a cikin tsarin sarakunan qibxawan
Misra. To, wannan tarihi na Asalin Hausawa daga
Masar shi turawan mulkin mallaka suka ga
qyashinsa, suka sa a musanya da na iska domin a
kawo ruxani da shakka a cikin tarihin Hausawa na
gaskiya su kuwa turawa su cimma maqasudinsu na
sharri da qin gaskiya, da hassada.

Maqasudin Turawa a wajen dankwafe tarihin
baqar fata
   Maqasudin turawa a wajen dankwafe duk
wani abu na alheri na qasashen da suka mallaka a
Afirka ta yamma, yana da yawa, amma guda biyu
sun fi muni.
1. Dankwafe tarihin baqar fata domin su gayawa
   shauran duniya cewa baqar fata ba shi da
   tarihi, domin ba shi da asali. Bai haxu da
   kowa ba a cikin qabilun duniya da aka sani,
   shi ya sa suke kiransa Negro. Saboda haka
   tarihinsa ya fara ne da zuwan turawa Afirka,
   inda suka tsince shi, suka gina masa tarihi.
   Wannan maqasudin shi suka yi wa take da
   turanci kamar haka: The History of Africa is            47
            …………….Daga Dutsen Dala

   the History of European in Africa. Ma‟ana
   tarihin Afirka ya fara ne daga tarihin zuwan
   turawa Afirka, don mulkin mallaka.
2. Dusashe duk wani haske da musulunci ya
   haskaka a cikin al‟umar baqar fata suka gani,
   suka bi domin su sami shiriya su bar duhun
   jahilci da arnanci, da vata. Anan sai turawa su
   dinga yaxa propaganda suna cewa addinin
   musulunci ya vata al‟adun gargajiya na
   waxanda ba musulmi ba, ya hana su shan
   giya, da batsa, da cin mushe da tafiya tsirara,
   da shauransu. Waxanda „yancin xan Adam ya
   gada musu. A nan an nuna addinin
   musulunci, addinin koma baya ne saboda
   hana „yanci.
   A saboda da su cimma waxannan maqasudai
guda biyu sai turawa suka xauki matakai na
propaganda guda biyu, na xaya sai suka tuhumi
shugabannin Jihadin Shehu Usman B. Fodio,
Muhammadu Bello da „yan uwansa da cewa sun
qone duk tarihin qasar Hausa waxanda malaman
Wangarawa suka rubuta aka tara su a „Yan Doton
Tsafe. Domin haka (su Turawa) sun sa an sake
rubuta sabon tarihi na Bayajida xan sarkin
Bagadaza wanda shi ne tsatson sarakunan Hausa
bakwai, da banza bakwai. Na biyu sai suka tuve
sarkin Daura na Fulani; Murnai, suka naxa sarkin            48
Kano Qwaryar Qira…...

Daura Musa na asalin Sarautar Daura ta jikokin
Lamarudu xan Kan‟ana (Amma da cewa shi jikan
Bayajida ne). Kaga a nan an canjawa tarihin
Hausawa alqibla daga Masar zuwa Bagadaza,
domin a kawo ruxu da shakka cikin lamarin.
   Bayan wannan sai aka haqa sabuwar rijiya
aka sa mata suna Kusugu, ta zama rijiyar da
macijiya Sariki take, wacce Bayajida ya kashe, ya
xebi ruwa. To, a wannan guri aka yi bikin naxin
sabon Sarkin Daura na asalin Have, inda a ka
gayawa duniya cewa turawan Ingilishi(10) sun mai
da asalin tarihin Hausawa, wanda Fulani suka
qona, kuma sun mayar wa da Hausawa mulkinsu
na Daura na asali wanda fulani suka qwace a
lokacin jihadi. Wannan kaxan ka gani a cikin
munafuncin turawa. Amma yanzu asirinsu ya
tonu, ana warware qarya tasu.

Hanzarinmu akan wannan bayani
    Ko da yake mun kawo kokwanto akan
tatsuniyar Bayajida, inda muka yi da‟awar cewa
ba gaskiya bace, duk da haka zamu ci gaba da
ambaton sunayen da suke cikin tatsuniyar irinsu
Bagauda xan Bawo jikan Bayajida, ko Bagauda
xan Daurama a matsayin laqabi kawai domin
tarihin ya tafi tare dasu, kafin a samu wanda ya fi
su alamar gaskiya, a jefar dasu. Ban da wannan            49
            …………….Daga Dutsen Dala

kuma ba ma da‟awar wannan xan bayani da muka
yi na cewa Hausawa da harshensu da addininsu
(kafin zuwan musulunci), sun fito daga Masar ne,
bisa ga asali, ya wakilci ra‟ayin shauran qasashen
Hausa, a‟a mu mun yi wannan karambani ne
kawai domin mu buxe qofar nazari akan sabon
tarihin asalin Hausawa, da harshensu, da al‟adunsu
wanda zai yi daidai da darajar da Allah ya yi musu
ta hazaqa, da muzakkaranci a cikin duk wani
vangare na rayuwar xan adam.
    Tastuniyar Bayajida ta dabaibaye tarihin
Hausa ya kasa tafiya ko ina. Lokacin da aka yi
wannan tatsuniya, lokacin jahilci ne. A yanzu ilimi
ya yi yawa ya yaxu ko ina, mutane sun samu buxi
na hankali da tunani, saboda samun ilimi akan
kowane fanni, saboda haka ya kamata a sake
sabon tarihin Hausa bakwai, da Banza bakwai mai
inganci, da karvuwa a wajen jama‟a. Amma duk
da abubuwan da muka faxa ba za mu jefar da
labarun baka na gargajiya ba. Za mu ci gaba da
amfani da su musamman masu nagarta a cikinsu.
            50
Kano Qwaryar Qira…...

        SASHI NA BIYU
   QASAR KANO DA FUSKOKINTA
    Qasar Kano tana daga cikin qashashen
Sudan masu ni'ima, musamman a kudancinta gurin
da bishiyoyi masu yawa suke.(1) Qasar Kano tana
da nisan kilomitar 840, daga gavar Sahara, kuma
tayi nisan kilo meter 472.45, a sama da gavar
tekun Atlantic. A cikin birnin Kano akwai
duwatsu guda biyu; Dala da Gwauron Dutse,
wanda suke kusa da shahararriyar qoramar da ake
kira Jakara daga kudu da su. Ita qoramar Jakara a
wancan lokacin kewaye take da manyan bishiyoyi
wanda ake kira Kurmi, kuma ruwan da yake
taruwa a kwaryata baqi ne mai haddasa tsoro a
cikin zuciyar jama'a. Domin haka ta zama gurin
bautar Kanawa saboda neman tsarin kai. Shugaban
bautar Jakara na wancan lokaci sunansa Mazauda,
wanda yake taimakon Barbushe jikan Dala.
    Haka kuma a arewa da waxannnan duwatsu
akwai qorama mai tara ruwa da yawa, wanda ba
ya qafewa. Mazauna Kano na farko sun yi da'awar
cewa ruwan wannan qorama ragowar ruwan
Xufana ne, tun na zamanin Annabi Nuhu (A.S.).
Duk lokacin da wannan qorama ta cika ta kawo sai
ta malala tayi arewa maso gabas inda take karya
garun birnin Kano na Qofar ruwa ta wuce.
Sarakunan Kano na Have da na Fulani sun sha            51
           …………….Daga Dutsen Dala

wahala wajen gyara wannan qofa a duk lokacin da
wannan ruwa ya karya ta, har sai da aka gaji aka
rufe ta a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero
1926-1953.
    A tsakanin wannan qorama da waxannan
duwatsu guda biyu waxanda ake kira, Dala da
Gwauran Dutse, akwai qasar noma mai albarka da
kuma ma'adinai na haqo tama wanda ake narkawa
ayi qarfe da ita. A saboda samun abubuwan
rayuwar xan Adam, irin waxannan da sauran su,
ya sa Kano ta zama gurin yin hijirar mutane daga
ko'ina a qasashen Sudan ta yamma. Wannan kuma
shi ya kawo hijirar maqera, da masu narka qarfe,
da sauran masana'anta, da manoma daga Gaya
zuwa Kano, inda suka zauna suka yi auratayya da
mazaunan wannan guri na asali. Asalin mazaunan
Kano kafin baqi su zo qabilun Qwararrafa ne,
kamar yadda Malam Adamu na Ma'aji ya faxa.(2)
    An ce wannan suna na Qwararrafa an same
shi ne daga sunansu na asali-Qwarara- na-Ofa
(Ofa ta qasar Ilorin). Ma'anarsa shi ne qabilu ne
masu zane iri daban - daban a fuskokinsu. Kuma
sune suka fi kowace qabila rassa a qasashen
arewa. Kamar yadda Tanko Yakasai yace(3)
rassansu sun haxa da qabilu irin su Bura da Babur
a qasar Bi'u, da Bolewa, da Ngamo, da Ngizim, da
Karekare, da Bedde duk a Yobe, da Waja, da            52
Kano Qwaryar Qira…...

Rumawa da Warji da Jarawa, da Ankwe a
qasashen Bauchi da Kano, da Plateau. Da Eggon
da Wamba, da Alago, da Keana, da Awe da
Doma, a jahar Nassarawa da wani vangare na
Nupawa, da Gwari a jihar Niger da Igala, da Igbira
a jihar Kogi. Da Igara a jihar Edo Da Wawa da
Aro a tsakani qabilun Ibo da Idoma da Onoja, da
Jukun da wani vangare na qabilar Hausawa da
shauran qabilu masu zanan uku-uku a bakinsu, ko
bille a fuskarsu ko kwale a kundukukinsu.
Akasarin qabilun arewa duka ana zaton asalin
kakanninsu daga qabilar Qwararrafa suke.
    Waxannan qabilun su ne wasu qabilun suka
yo hijira daga gabas maso arewa suka shigo
cikinsu suka zauna suka yi auratayya suka koya
masu sababbin dabaru na sarrafa abubuwan
rayuwa da iya riqon jama‟a har suka mallake su
suka zama sarakunansu. A saboda wannan ne
mafi yawa daga qabilun arewa suke da'awar cewa
asalin sarakunansu na yanzu daga gabas suka fito,
a gabas xin kuma bata shige Yamen, ko Makka,
ko Misira, Ko Bagadaza, ko Habasha da sauran
ire-irensu.
    Ban da waxannan abubuwa da muka faxa na
wasu sifoffin qasar Kano akwai kuma manyan
koguna guda biyu a arewa da qasar. Waxannan
Koguna su ne kogin Haxejia mai tsawon tafiyar            53
           …………….Daga Dutsen Dala

kilomita 328, da kuma Duddurun - Gaya wacce ta
taso tun daga tudden kudancin Kano tayi tafiya
kilomita 362, kafin ta faxo cikin tafkin Chadi mai
nisan kilomita 320, arewa maso gabas da Kano.
Ita kanta qasar Kano tayi hawa da gangara amma
ba masu tsanani ba, kuma gangaren nata a wajen
Arewa maso Gabas yake inda gurin ya zama bai
xaya, in ban da dutsen Dala da Goron dutse. Sai
kuma babban kogin Kano wanda ya taso tun daga
duwatsun Riruwai waxanda su ma wani bangare
ne na jerin duwatsun Rano.
   Fiye da Rabin qasar Kano a kan duwatsu
masu taushi take waxanda tavo da qasa suka rufe
su, saboda haka in an haqa rijiyoyin burtsatse ake
samun ruwan sha a irin waxannan gurare. Amma
kuma akwai tarin tsofaffin duwatsu da suka mutu,
suka kuma yi vangori a kan su da kwibinsu. Ana
samun irin waxannan duwatsu a gabas da arewa
maso gabancin Kano, a layinsu wanda ya ratsa
garuruwa irinsu Kiyawa, da Dutse-gadawur, da
Gaya a gabas, da Xanbatta, da 'Yan Kwashi a
Kazaure da sauran su a arewa. A da, ana haqo
dutsen niqa daga cikin irin waxannan duwatsu,
kamar yadda ake samo wa daga Dutsen Gima a
Makoxa, ta Xanbatta. Da irin su ake yin gilashi a
yanzu a wasu qasashe na duniya.
            54
Kano Qwaryar Qira…...

    Shi kuma mulmulallan dutse wanda
shekarunsa basu kai na mutuwa ba, ana samun irin
su a vangaren kudu da yammancin Kano ta layinsu
da ya bi ta Rano, da Riruwai da kuma Qaraye. A
irin waxannan duwatsu ake samun ma'adinai iri-iri
na arziqin qasa.
    Ban da ire-iren waxannan duwatsu kuma
akwai jajayen duwatsu waxanda tarin qasa ne
kawai na Allah, amma a sama dasu akwai jan birji
mai jar tsakuwa ko marmara, wadda ta lulluve su.
Irin waxannan duwatsu su ne dutsen Dala, da
Gwauron Dutse, da dutsen Panisau da sauran ire-
iren su, manya da qanana.

YANAYIN QASA DA HAVAKAR NOMA(4)
    Qasar Kano qasa ce wacce Allah ya ba
ni'imomi masu yawa. Da farko dai ga ta da yawan
jama‟a. A zamanin da, lokacin da ba'a san qidayar
mutane ba, an tabbatar Kano tafi kowacce qasar
Hausa yawan mutane ta hanyar haihuwa. Saboda
matan Kanawa galibinsu akwai masu haihuwa a
duk shekara. Saboda haka ake cewa da irin
wannan nau‟in na `haihuwar matan Kano
kwanika, ma'ana wai irin haihuwar da matan
Kano suke yi. Ban da wannan kuma yawan
mutanen Kano yana qaruwa ne a kullum ta hanyar
hijirar mutane masu zuwa Kano su zauna a            55
            …………….Daga Dutsen Dala

cikinta, zama na dindindin, tun lokacin da aka kafa
garin Kano har zuwa yau. Ko da a qidayar
zamaninmu na yanzu, jama'ar Kano a qidayar
1990 sun kai 5,632,040. Ana kuma tsammanin
kashi 70% manoma ne. Magidanta 394,243 ake da
su, kuma kowanne maigida yana da qiyasin hekta
a matsayin gonar sa.
    Ni'imomin da Kano take da su sun haxa da
rana da dare makusanta duk shekara, da gonaki
masu tsarin kunya da kadada, a cikin qasa mai
rangwamen hawa da gangara. Akwai matsakaicin
ruwan sama da rashin tsananin zafi ko sanyi. Kano
tana da iskoki busassu, da dabbobi, da tsirrai da
sauran su. Kuma ita ce ta zama cibiyar kasuwanci
a duk Afrika ta yamma tun lokacin hukumar Kano
ta biyu wacce ake kira hukumar Madatai. Muna da
yanayin noma iri biyu, noman rani da na damina,
da iskoki iri biyu, mai kawo sanyi da mai kawo
zafi. Yawan ruwan sama a Kano ya kai
870.20mm, a wasu wuraren. Daminar ta kan yi
kwana 100-150, ko wata biyar, daga tsakiyar
watan (Mayu) zuwa tsakiyar watan goma
(Oktoba). Shi kuma rani yakan kai wata bakwai,
daga tsakiyar (Oktoba) zuwa tsakiyar watan
(Mayu). Wannan ita tasa ake cewa, "watan bakwai
maqarar rani, kan babu damina da alama"; An dai
san babban kogin mu shi ne Kogin Kano, sai masu            56
Kano Qwaryar Qira…...

bin sa wato kogin Chalawa, da na Watari, dana
Tomar, da na Kafin Ciri, kuma akwai madatsar
ruwa a kowannensu domin noman rani. Akwai
kuma rijiyoyin burtsatse masu yawa a cikin
Fadamu. Muna da raqumar qasa wacce yashi yafi
yawa, sai dai tavo a fadamu. A wasu guraren
kuma muna da mai tauri,

TSARIN NOMA A KANO
    A cikin tantancewar da aka yi game da
tsarin noma, da arziqin qasa, ta hanyar zamani,
Kano tana da hekta miliyan biyu da dubu arba‟in:
Daga cikin wannan adadi akwai hekta miliyan
xaya da dubu xari bakwai da hamsin na gonaki, da
gidaje, da kasuwanni, da hanyoyi, da tashoshi, da
kududdufai da sauran su. Akwai kuma hekta dubu
tamanin na dazuzzuka, da kuma hekta dubu xari
biyu da goma na magudanar ruwa. Tarikhil-Arbab
Hazal Baladi - wato litttafin Tarihin Kano, bai yi
wani bayani ba a kan mutanen da suka fara yin
noman wadata a Kano daga cikin mazaunan Kano
na farko. Amma waqar Bagauda(5) ta tarihin Kano
ta bayyana cewa Maguzawan da suka zo Kano
daga Gaya suna ciranin farauta su ne suka koma
noma domin sun ga Qasar Kano a wancan lokaci
budurwar qasa ce mai albarka. Waqar ta ambaci
mutane huxu waxanda suka zo tare da Bagauda            57
           …………….Daga Dutsen Dala

suka zama sarakunan noma daga baya. Ga abin da
waqar tace game da sunan mutanen da ayyukansu
na noma:

   Ga Gwale da shi da Yakasai da Sheshe Da
   Guguwa manya-manyan Maguzawa.

   Ana cewa da su su ne sarakai
   Na noma suka zuwa gewayawa.

   Garin kallon dawa suka kama gona
   Fa sai aike iyali na tahowa.

   Manoman nan da sunka taho da farko
   Sukai sara suna kuma dandatsewa.

   Sa'annan ruwan bazara ya sauka,
   Sukai shukarsu ta tsira ba qafewa.

   Ka san sabon dawa gero ya kanyi
   Da dawa ba irin da ka tsunburewa.

   Da sukai gero da dawa ba misali
   Fa sai yunwa ta afko mai kashewa.

   Da babu awo dai sai an zo gare su
   Ake samu ana kuma retatawa.           58
Kano Qwaryar Qira…...


   Sukai qarfi na bayi har dawakai
   Fa su ne manyan tajirawa.

   Gabas ta faso yamma har arewa
   Wajen kudu sunka varko Maguzawa.

   Barnawa da Katsina da Daura
   Da Zamfara can ta Have da Gobirawa.

   Sukai ta zuwa suna kamun gidaje
   Kabawa, Kambarawa, Adarawa.

   Da yunwa ta hayaqa ta watsa Azbin
   Gudunsu yawo Kano gun saukakewa.

   A gulbin Kura can suka yada Zango
   Fa har yunwa ta kai jallin wucewa.

   Da qoshi yazo waraka ta samu
   Dare xaya an ka duba babu kowa.

   Amma fa Tokarci bayi ne na Azbin
   Fa sun ka qi bin su sun ga gurin fakewa.

   Bugaje masu yin wasan maqera
   Fa ba su ubangiji sai Azbinawa.            59
             …………….Daga Dutsen Dala


     Tun daga Lambu Sara ne ya kama
     Ta Kanwa ta Kwankwaso har Tamburawa.

     Tun daga Yankatsare gida ya fara
     Ta Mariri ya Gunduwawa.

     Jama'a sun yawa wasu har Sugungum
     Da Jirima abin ya fi lisafawa.

     Mutane ne Sarai duk sun yiwo shaya
     Fa ba sarki fa ba garun tsarewa.

     Tumbi da shi da Washa sun ga banza
     Suna gama kai kame Kanawa.

     Daga nan manya suka ce sai ai sarauta.
     A kai sarki Bagauda mai tsarewa.

   Wannan waqa ta nuna        juyi  uku  a
sakamakon baqi daga Gaya.
(1)    Juyin farauta.
(2)    Juyin noma wanda ya kawo
     arziqi da qarin hijirar mutane da
     kasuwanci.
   (3) Kafa sabuwar hukuma a Maxatai
     a karkashin jagorancin Bagauda.


             60
Kano Qwaryar Qira…...

    Wannan sabuwar hukuma ba
    ruwanta da hukumar farko ta
    Mazauda masu bautar ruwan
    Jakara.
    Tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu
mafiya yawan ko kuma dukkan manomanmu na
karkara suna shuka sama da amfanin gona xaya a
gonakinsu waxanda suke ba a haxe suke ba , misali
mai gona ya iya samun haxakar Dawa, da Gero, da
Maiwa da Wake da Gyaxa, da Gurjiya, da tumatur,
da Tattasai da Barkono, dukkansu a gonarsa kamar
yadda ya zava.
  A saboda waxannan abubuwan alheri ne Qasar
Kano ta zama mafi kyawon gurin zaman xan
Adam. Allah ya kiyaye qasar Kano daga samun
wasu matsalolin rayuwa waxanda suka fi qarfin
xan Adam, irin su tashin guguwar sahara, da aman
duwatsu, da cinyewar ruwan Koguna, da Qoramu
wanda mutenen farko ba za su iya maganin su ba a
Kano. Har ila yau kuma shimfixaxxiyar Qasar
Kano, da qogunanta masu kwarara, da
dazuzzukanta, da duwatsunta sun dace da noma, da
farauta da tsaron kai daga abokan gaba. Daxin
dadaxawa kuma, mazaunanta na farko masu sauqin
kai ne masu qaunar baqi. Ba dan waxannan halaye
ba, da Kano ba ta zama qwayar qira matattarar
alheri ba.            61
           …………….Daga Dutsen Dala

         SASHI NA UKU
   HIJIRAR MUTANE DAGA GABAS
      (MISRA DA PALASXINU)
    A farkon wannan Littafi an yi bayanin
alaqar qasashen Hausa da Misra da kuma hijirar
farko ta wani vangare na qabilar Hausawa da su ka
zo Daura, a qarqashin shugabansu mai suna
Abdullahi xan Najib. Tarihi ya nuna cewa wannan
vangare na Hausawa sune suka fara kafa hukumar
farko ta qasar Hausa, suka mallaki mutanen da
suka tarar suna zaune a Daura, suka mai da su
talakawansu, bayan wannan ne kuma shauran „yan
uwansu na gurare daban – daban suka dinga yiwo
hijira a qarqashin shugabaninsu suna mallake
mazauna gurin na asali, amma dukansu suna yin
caffa ga hukumar farko ta masu hijirar farko ta
Daura, domin asalinsu xaya, harshensu xaya.
    Wannan yunquri na neman sabon gurin
zama ta hanyar yin hijira, saboda gujewa tashin
hankali da neman zaman lafiya shi ya kawo
qabilun Hausawa da na Habashawa zuwa qasashen
Hausa, inda su kai yo hijira daga qasashensu na
asali suka zo suka zauna tare da qabilun da suka
samu na asali a gurin. Wannan yunquri na farko
shi ne ya bunqasa, yayi nasara har ya kafa
qungiyoyin Hausawa, da garuruwan zaman su a
qarqashin jagorancin shugabanninsu, ta hanyar            62
Kano Qwaryar Qira…...

sana‟o‟i iri daban daban. Wasu ta hanyar bautar
gunki, wasu ta hanyar farauta, ko noma, ko kiwo,
ko yaqi da maqwabta da shauransu. To, wannan
yunquri na hijirar Hausawa zuwa qasar Hausa shi
ne ya kafa abin da tarihi ya sa masa suna Hausa
Bakwai, bayan wahalhalun da aka sha na faxi -
tashi da yunqurin juyin zamani, har aka sansu da
sunayen da ake kiransu a yau.

MAZAUNA KANO NA FARKO: QABILAR
 DALA DA TA MAXATAI
    Kano ta bunqasa ne ta hanyar zuwan qabilu
iri daban-daban wannan guri. Su waxannan qabilu
sun yiwo hijira ne daga inda suke suka zo Kano
don su zauna. Dalilan hijira suna da yawa. Wasu a
dalilin yawon farauta ne suka samu wuri mai kyau
su zauna, wasu kuma a dalilin neman wajen kiwo
suka zauna su zama manoma.
    Idan irin wannan hali ya samu qabilu a guri
xaya, sai ka ga kowace qabila ta qware wajen
sana‟ar da ta iya don taimakawa zaman rayuwar
sauran. Ta haka ne dogara da juna da alaqar
rayuwa take samuwa don neman tsaron kai da
zaman lafiya da yaxuwar arziqi.
    Amma dalilan hijira, bayan waxanda da aka
ambata a baya, suna da yawa. Ana ma yin ta don
neman sanin duniya, ko gujewa annoba ko fari ko            63
            …………….Daga Dutsen Dala

yunwa ko girgizar qasa da amon-wuta na duwatsu.
Babbar masifar da take kawo hijira ita ce yaqe-
yaqe tsakanin qabilu, ko hare-hare. Idan wata
qabila ta ga alamar maqwabciyarta ta fi ta qarfi
kuma tana jin tsoron yaqi da ita, sai ta yi hijira don
ta tsira daga masifar hari da kisa ko kamun bayi
cikin „ya‟yanta. Saboda haka ne Hogben da Kirk-
Green suka qara bayani inda suka ce:(1)
     “Tun daga qarni na uku da
  haihuwar Annabi Isa (A.S) 300 A.D. aka
  samu labarin wata babbar hijira daga
  qasar Sudan wato Nubiya bayan Sarki
  Axum na Habasha ya rushe tsohon garin
  nan da ake kira Kush, ya kuma qona
  mashahurin birnin nan nasa mai suna
  Meroe, wanda yake kusa da bakin Kogin
  Nilu. Mutanen wannan guri sun yi hijira
  sannu-sannu suka yiwo wajen Chadi ta
  Kurdafan da Dafur da Wadai, har suka
  iso qasar Kano.”
    Akwai jita-jitar cewa cikin waxannan qabilu
da suka yiwo hijira daga qasashen Habasha ko
Sudan Nubiya akwai wani mutum a cikin su
wanda ya zo nan Kano daga tsibirin Dahlak ya
zauna tare da iyalinsa. Dutsen da ya zauna a kansa
aka sa masa suna Dala, daga kalmar Dahlak.
             64
Kano Qwaryar Qira…...

    Wannan mutum shi ne tarihin Kano ko
kuma mu ce malaman tarihi suke kira Dala
Ubangijin    Tsumburbura   kakan  Barbushe.
Waxannan marubuta da muka ambata a sama sun
ci gaba da gaya mana cewa(2):
     “Akwai almarar wata hijirar da
  manoma na qasar Larabawa ta Yaman
  suka yiwo bayan sun qetare ruwan
  Maliya. Wannan hijira ita ma gujewa
  yaqi na Axum ya kawo ta, a qarni na
  shida daga haihuwar Annabi Isa (A.S).
  Waxannan manoma su ne suka shiga
  cikin qabilun arewacin Najeriya suka yi
  auratayya da su. Don haka babu
  mamaki in ka ji wata qabila ta arewacin
  Najeriya ta yi da‟awar sarakunanta
  daga Yaman suke. Kamar yadda Kanuri
  suke cewa sarakunansu daga Yaman
  suke. (Za ka ji qarin bayani akan
  wannan da‟awa.) Bayan wannan ne
  kuma yunwa ta sa manoman yaman
  suka yi hijira suka zo nan qasar.”
    Ita yunwar da ta kawo hijirar manoma daga
Yaman ta afku ne bayan wata shahararriyar
matarar ruwa ta Ma‟arib ta fashe ruwan ya gudu.
Sunan wannan matarar ruwa na Yaman Sa’d
Ma’arib(3) da Larabaci. Da Turanci kuma sunansa            65
           …………….Daga Dutsen Dala

‘Ma’arib Dam’, kuma shi ne farkon matarar ruwa
da aka yi a duniya. Sarakunan Sabean da
Himyarite, irin su sarauniya Bilkisu ta Annabi
Suleiman su ne suka gina wannan matarar ruwa,
kuma suka ci gaba da kyautata ta, amma
sarakunan baya suka bar ta ta lalace har ta fashe.
Wataqila a tsakanin qarni na biyar zuwa na shida
na haihuwar Annabi Isa (A.S), wato 5-6 A.D. ke
nan.
    Da wannan matarar ruwa ta fashe ruwan ya
gudu sai waxannan manoma suka tarwatse suka
shiga duniya don neman sabuwar hanyar rayuwa.
Wasu suka shiga Hijaz inda suka kafa Makka da
Madina, wasu suka yi arewa inda suka kafa
Damascus da Sham, inda yanzu ake kira Syriya da
Iraqi.(4) Waxannan manoma su ne suka tsallako
kogin maliya suka yiwo yammacin Afirka suka
shigo qasar Hausa har zuwa Kano, inda suka kawo
sabuwar hanyar noma mafi inganci, musamman
noman rani wanda ba a san shi a nan ba kafin
zuwan su. Har ila yau dai su ne suka zo mana da
sababbin iri na shuke-shuke, waxanda ba a san su
a nan ba kafin zuwan su. Waxannan iri su ne Al-
kamh (alkama), Al-bassal (albasa) Dumadum
(tumatiri) waxanda muka mai da su Hausa muna
kiran su, alkama da albasa da tumatir. Ana zaton
waxannan manoma da suka zo nan da farko sun            66
Kano Qwaryar Qira…...

zauna ne a wajen Duddurun Gaya da Kogin
Chalawa don sun yi kama da gurin da suka fito.
Kuma a waxannan gurare ne suka ci gaba da koya
wa mazaunan wannan guri sabuwar hanyar noma.
    Ita wannan hijira kuma ita ce ta buxe hanyar
wata hijirar wadda aka yi bayan bayyanar addinin
Musulunci. A zamanin Sayyidina Umar b.
Khattab, Khalifar Annabi na biyu (634-643).(5) A
wannan lokaci ne Musulmi suka ci Misra, suka
kuma ci Birnin Kisra (Persian Empire) da Kaisaria
(Eastern Roman Empire), suka yaxa Musulunci a
duk qasashen Makka da guraren da ake kira Bilad
al-Fuis, wato qasar Ajami ko mutanen da ba
Larabawa ba. A wannan lokaci ne Amr b. al-As ya
ci Birnin Misra inda ya zama shi ne hakiminta na
farko a cikin daular Musulunci. Wannan kuma ya
kawo hijirar Larabawa zuwa waxannan gurare da
aka ci don neman sabuwar hanyar rayuwa.
    Nasarar waxannan yaqe-yaqe ita ce kuma ta
kawo shimfixa mulkin Musulunci na Daular Banu
Umayyad, a Syriya da na Banu Abbas, a Bagadaza
bayan shekarar fitowar Musulunci. Kowace xaya
daga cikin waxannan dauloli ta yi qoqari cikin
kwanakin mulkinta ta kafa mulkinta a Afirka ta
arewa., tun daga Misra daga gabas har zuwa
Biladal-Andulus (Spain) da Maghrib-al-aqasa
(Morocco) daga yamma. Wannan kuwa ya haxa da            67
           …………….Daga Dutsen Dala

qasashe irin su Turabulus (Libya) da Tunusiya da
Aljeriya. Larabawa sun riqa zuwa waxannan
qasashe suna musuluntar da mazauna gurin na
asali suka yi auratayya da su, suka haxiye su har
suka mayar da su Larabawan Afirka ta arewa.
    Waxannan larabawa masu hijira ba su tsaya
a waxannan qasashe da muka ambata kawai ba,
a‟a, sun ci gaba da tafiya tasu a cikin Sahara
saboda yaxa addinin Musulunci ko kasuwanci ko
malanta har suka iso nan Kano ta varin Gaya a
inda suka tarar da „yan‟uwansu waxanda suka
yiwo hijira tuni daga Yeman da Habasha, don
gudu daga yaqe-yaqe. Kuma a nan ne waxannan
masu hijira suka zo da dabarun noma da sana‟o‟i,
suka koya wa mutanen wannan guri.

GAYA CE TA BA WA KANO SUNANTA
   A taqaice dai wannan bayani da muka yi a
sama ya nuna akwai hijira iri biyu zuwa qasashen
Hausa, sune hijirar qabilar Dala da ta qabilar
Maxatai. Waxannan qungiyoyi biyu su ne tushen
kafa Kano ta farko. Tarihin Kano ya nuna cewa
qauyen Gaya mai nisan kilomita 60, daga Birnin
Kano yana da matuqar tasiri wajen kafa Birnin
Kano. Da farko dai Gaya ita ce zangon qarshe na
duk masu yin hijirar nan da muka ambata daga
qasasashen Larabawa da Habasha da Magarib            68
Kano Qwaryar Qira…...

wato Afirka ta arewa. Kuma ita ce rariyar da suke
bi su shiga ko ina a cikin qasashen Kano.
    Na biyu kuma da alamar Gaya ita ce ta ba
wa Birnin Kano sunansa. Wataqila wannan ya faru
ne ta kan wani maqeri mutumin Gaya xin mai
suna Kanoki,(6) wanda ya yi hijira shi da jama‟a
tasa daga Gaya zuwa dutsen Dala, saboda neman
tama, wadda ake yin qarfe da ita.
    Shi wannan maqeri mai suna Kanoki da
qarfen qira tasa ya qare, sai shi da qungiya tasa
suka fito neman tama suka yiwo yamma har suka
zo Dala, inda suka same ta suka xiba suka koma
garinsu Gaya. Tun daga sannan duk lokacin da
tama tasu ta qare, sai su taho Dala su xiba. Daga
qarshe dai suka ga ya kamata su yi qaura daga
Gaya su komo Dala su zauna don su ci gaba da
qira tasu a nan.
    Bayan da Kanoki ya dawo Dala ya zauna
sai kasuwa ta buxe masa. Mutane daga ko ina suka
riqa zuwa wajensa suna sayen kayan noma da na
farauta da na aikin gidaje. Wannan kasuwa sai ta
jawo masa qabilu iri daban-daban waxanda suka
yiwo qaura suka zo wajensa don su zauna tare da
shi. To da yake kowace qabila ta kan zo da abin da
Allah ya hore mata na sana‟a, sai masana‟antu
suka tashi a gurin. Masaqar tufafi da marina da
majema duk suka yawaita.            69
           …………….Daga Dutsen Dala

   Wannan qaramin buxi na arziqin qasa shi ne
ya kawo kafa Birnin Kanawa a gindin Dala,
wanda ya qunshi dangin qabilu sha xaya, kuma
kowace qabila tana da sana‟ar da ta qware a kai. A
saboda sunan wannan maqeri Kanoki da ya fara
zama a gurin ake kiran gurin Kano, kuma qabila
tasa aka dinga kiranta Abagayawa. Wannan
qaramin juyi ana zaton ya faru ne a tsakanin qarni
na 5-6 daga haihuwar annabi Isa (A.S) kuma su
waxannan qabilu guda goma sha xaya da suka
kafa wannan birni a gindin Dala za ka karanta su a
nan gaba kaxan kamar yadda tarihin Kano ya
ambace su.
   Wani abin sha‟awa cikin rayuwar waxannan
qabilu shi ne zaman lafiya da haxin kai na
taimakon juna. Tun da dabarar yin sarki, a
matsayin shugaban kowa da kowa, ba ta zo ba, to
limamin addininsu shi ne shugabansu. A lokacin
ruwan Jakara suke bautawa kuma Mazauda shi ne
Limanin bautar Jakara saboda haka ya zama
shugaba. To cikin waxannan mutane ne Dala yazo
ya zauna tare da su a kan dutsen Dala. An ce Dala
ya zo wannan guri tare da „ya‟yansa guda bakwai,
huxu maza uku mata. Sunan babban su Gargaji,
shi ne kakan Buzami uban Barbushe, kuma
Barbushe shi ne ya gaje shi daga baya.
            70
Kano Qwaryar Qira…...

DAGA INA DALA YA ZO?
    Malaman tarihin Kano irin su Alqali Zangi
da Waziri Abubakar ba su yi nishaxi mai yawa ba
game da labarin Dala da iyalinsa, balle a san daga
ina ya zo, kuma shi wane ne kafin ya zo xin. Idan
ban da littafin Tarihin Kano na Muhammadu
Bello(7) (Sarkin Kano 1883-1892) ba wanda ya
faxi labarin Dala. Ko shi ma wannan littafin bai
faxi wani abu mai tsawo ba akan zuwan Dala nan
qasar. Abin da littafin kawai ya faxa shi ne:

    “Shi Dala mutum ne baqi kuma
   qaqqarfa kuma mafarauci qwarai.
   Domin shi yakan kashe giwa da
   sandarsa, ya xauko ta a kansa, ya yi
   tafiya da ita kamar mil tara. Ya zo
   garin nan ba a san asalinsa ba. Da
   ya zo ya gina gidansa a Dutsen
   Dala, ya zauna a kanta shi kaxai
   tare da matansa da „ya‟yansa
   bakwai, huxu maza, uku mata. Sunan
   babbansu Gargaji. Shi ne kakan
   Buzami uban Barbushe. Barbushe ne
   ya gaji halayen Dala daga sanin
   dukkan   dangogin   tsafi  da
   al‟ajubansa da sihirinsa da rinjaye
            71
            …………….Daga Dutsen Dala

    ga „yan‟uwansa, domin haka ya
    zama shugabansu”.
    To wannan abin da muka kawo maka na
cikin littafin Tarihin Kano game da Dala shi ne
kawai abin da za ka ji game da shi ba daxi ba ragi.
Wannan kuwa xan bayani na Dala ba zai qosar da
duk wani almajirin Tarihin Kano ba. Kuma tun da
yake babu littattafai a qasar Hausa a yanzu,
waxanda za su taimake mu su bamu haske don mu
san daga ina Dala ya fito, kuma da inda ya koyi
sihirinsa da dabarar sarrafa giwa, to dole ne mu yi
namu qoqarin don neman mu san daga inda ya fito.
    Idan ka yi tsokaci mai nisa cikin abin nan da
littafin Tarihin Kano ya faxa game da Dala, za ka
ga shi wannan mutum ya zo da abubuwa uku
waxanda ba a san su a nan qasar ba, kafin
zuwansa, kuma su waxannan abubuwa da ya zo da
su, su suka sa ya sami shugabancin matsafan
wannan guri har ya bar wa jikansa Barbushe
wannan shugabanci. Su waxannan sababbin
abubuwan dai da Dala ya kawo su ne:

1. Dabarun gina wa gunki xaki na musamman, da
  sa masa ranar bauta, da sallar Idi biyu; qaramar
  salla da babbar salla, kamar yadda ake bauta a
  Ka‟aba a qasar Larabawa a zamanin jahiliyya.
            72
Kano Qwaryar Qira…...

2. Dabarar sihirce-sihirce da tsafe-tsafe wadda ta
  burge mazauna wannan wuri har suka yi wa
  Dala mubaya‟a suka bi jikansa Barbushe da
  gunkinsa Tsumburbura bi na haqiqa.

 3. Dabarar sarrafa giwa wadda ta nuna cewa
   dama can kafin Dala ya zo nan qasar ya san
   giwa da yadda ake sarrafa ta.
  Tun da yake waxannan abubuwa da muka
lissafa haka suke ga Dala, to shi Dalan daga ina ya
fito? Kuma a ina ya sami sanin waxannan dabaru
nasa da muka ambata a sama?
   Shehu Nasiru Kabara ya gaya min cewa Dala
ya zo ne daga tsibirin Dahlak(8) na qasar Habasha.
Wannan tsibiri a bakin kogin Maliya yake, kuma a
yanzu yana cikin qasar Eritrea ne. To kaga ashe
Dala ya fito ne daga cikin qasashen gabas
waxanda suka sami ci gaba wajen ilimin sihiri da
tsafi da bautar gumaka da farauta irin ta wancan
lokaci fiye da na mazauanan Kano na farko. Don
haka suka bi shi dole ba don ra‟ayi ba.
    Amma a nazarin da Lugard yayi akan
tarihin Hausawa a cikin littafin sa mai suna
Tropical Dependency(9) yace masu irin wannan
addini na gunkin tsumburbura wataqila Qibxawan
Misira ne na qabilar Phonecian, wato banu
Kan‟ana kamar yadda aka san su a qasar Hausa.            73
           …………….Daga Dutsen Dala

Saboda haka Dala da jikan sa Barbushe ana zaton
Qibxawan Misira ne suka yiwo qaura daga tsibirin
Dahlak na kogin baharul Maliya, wanda a wancan
lokacin a qarqashin mulkin Fir‟aunonin Misira
yake. Da suka zo nan suka mallake mazauna
wannan qasa na farko; qabilun Qwararrafa, saboda
ci gabansu da qwarewar su wajen tsafi da farautar
giwa.

ZUWAN DALA DA AIKIN HAJI A KANO
   Zuwan Dala wannan garin tare da mata tasa
da „ya‟yansa da sauran jama‟a da ya zo da su ya
kawo ci gaban mazauna wannan wuri na asali. Da
farko dai an samu auratayya tsakanin iyalinsa da
mutanen wannan guri wadda daga qarshe ta haxe
mutanen har aka san su da qabilar Dala. Na biyu
kuma Dala ya zo da sabuwar bautar gunki irin
wadda ake yi a Makka ta su Lata da Uzza kafin
Musulunci ya bayyana.
   Haka kuma shi ne ya fara gina wa gunki
xakin bauta mai kusurwa guda huxu wanda ba mai
shiga sai shi kaxai, ya kirawo wannan gunki nasa
Tsumburbura, (wataqila wannan tayi kama da
Qulais ta Abraha Sarkin Yaman). Bayan wannan
Dala ya sa wa wannan gunki nasa bikin idi a duk
shekara wanda ake yi a daidai da lokacin da ake
hawan Arfa da Babbar salla a Makka. Waxannan            74
Kano Qwaryar Qira…...

sababbin abubuwa sun bai wa Dala girma da
xaukaka daga mabiyansa na ko ina a cikin
kusurwoyi na qasar Kano. Wannan xaukaka ta
Dala ita ce ta havaka har ta zama gadon gargajiya
inda xan jikansa, Barbushe ya gaji duk sihirinsa da
tsafinsa, bayan shi ya mutu. Game kuma da irin
addinin da Dala ya zo da shi wanda ya sha bamban
da bautar Jakara, ga abin da Malam Adamu na
Ma‟aji ya faxa a kai(10):
      “Ana yin bikin Idi sau xaya a
   shekara, a (Dala), daidai da lokacin da
   ake yin Sallar Id-el-Adha a watan Zul
   Hajj a Makka. A ranar sallar Idi
   Barbushe wanda shi ne babban Limami
   shi yake jan duk mahajjata zuwa xakin
   gunkinsu, yana riqe da baqin bunsuru na
   layya. Idan an yanka wannan bunsuru,
   sai a zuba jininsa a cikin wata gidauniya,
   wadda aka ajiye a gaban gunkin. To, a
   nan ne Barbushe zai saurari abin da
   gidauniyar za ta yi. Idan jinin ya yi sanyi
   a cikin gidauniyar to, alama ce ta komai
   zai daidaita a sami zaman lafiya da arziqi
   a wannan shekara. Idan kuma jinin ya yi
   zafi to alama ce ta abin da zai faru a
   wannan shekara na dangin masifu.
   Yawan zafin jinin yawan abin da zai faru            75
            …………….Daga Dutsen Dala

   ke nan ko, yaqi ko annoba ko yunwa.
   Daga nan sai Barbushe ya shaida wa
   maqarrabansa abin da ya gani na
   masifar da za ta afku, da kuma lokacin da
   za ta afku xin. Sannan kuma sai ya ba da
   umarnin kowane mahajjaci ya yi layya da
   abin da ya zo da shi don a roqi gumaka
   su kare masifar da za ta zo, ko su rage ta,
   ta yi wa mutane sauqi yadda za su iya
   jure ta.”
    Wani abin sha‟awa a nan shi ne irin wanan
bauta da ake yi a nan Kano, ita Larabawa suke yi
wa Lata da Uzza a Ka‟aba a Makka kafin fitowar
addinin Musulunci. A cikin littafinsa mai suna
Nurul Yakeen Fi Sirat Sayyadil-Mursalin, Sheikh
Muhammad al-Hadhari ya bayyana irin gidauniyar
da ake zuba jinin bautar gunki a Makka ta waccan
lokacin, ya ce sunan gidauniyar al-Nasab, kuma
dutse ne aka fafe shi ya zama gurin zuba jinin
bauta. Koda yake a nan Malam Adamu na Ma‟aji
bai faxi sunan gidauniyar tsafi ta Barbushe ba, bai
kuma faxi siffar ta ba, wataqila gidauniyar tsafin
Barbushe ta qarfe ce, wadda mutanen Kano suka
qera masa, don irin wannan ibada ta gumaka.
    Wannan siffar bautar gunkin Tsumburbura
da Malam Adamu na Ma‟aji ya bayyana ta yi
daidai da abin da littafin tarihin Kano ya bayyana            76
Kano Qwaryar Qira…...

game da Idin da ake yi a Dala a wancan lokaci,
kuma ga abin da littafin ya ce: Ya fara da
nahiyoyin da ake tahowa Dala domin bikin Idi
biyu; Salla qarama da Salla babba.(11)
  “Tun daga Tudu zuwa Xanbaqoshi, daga
  Duji zuwa Xankwai, dukkansu suna
  taruwa wurin Barbushe daren sallah
  biyu, domin shi ne babbansu cikin tsafi.
  Sunan wurin da gunkinsa yake
  “Kakuwa”,      sunansa     kuwa
  “Tsumburbura”, domin itaciya ce da ake
  ambaton ta “Shamus”, sunan mutumin
  da yake a zaune a qarqashinta dare da
  rana “Mai Tsumburbura”. An kewaye
  itaciyar da gini, babu mai shiga cikin
  ginin sai Barbushe, dukkan wanda ya
  shiga sai ya mutu nan da nan. Barbushe
  kuma ba ya saukowa daga dutsen Dala
  sai idan ranakun Idi biyu sun kusato.
  Sa‟an nan mutane su zo masa daga gabas
  da yamma, kudu da arewa, maza da
  mata. Daga cikinsu waxansu su zo da
  baqin kare, waxansu da baqar kaza,
  waxansu da baqin bunsuru”.
    Wannan ita ce siffar gunkin Barbushe da
masu bauta masa da kuma lokacin da suke yin
wannan bauta, wato Salla babba da Salla qarama            77
           …………….Daga Dutsen Dala

ko kuma mu ce Hajji da Umra, kamar yadda ake
yin su a Makka ta lokacin Jahiliyya. Ban da
wannan kuma ga yadda suke yin hawan arfa da
Xawafi na jahiliyya, bayansu kuma su yi layya.
     “Idan sun taru a qarqashin dutsen
  Dala ranar jajiberi (ranar Arfa) bayan
  la‟asar, sa‟an nan Barbushe ya fito daga
  gidansa da Isha tare da makaxansa (na
  Kuru da Gunduwa da Tsintsima). Ya riqa
  kururuwa da qarfi yana cewa; “Babban
  Jimina akasa mun gama karaga ga laya
  Tsumburbura”. Mutane kuma su ce, ga
  Tsumburbura Kanawa, ga wajen Dala”.
  Bayan wannan ya sauko su tafi tare da
  shi zuwa wurin gunki. Da isa wurin
  gunkin kowa ya yanka abin da ya zo da
  shi, sa‟an nan Barbushe ya shiga cikin
  ginin shi kaxai yana cewa “Ni Magajin
  Dala, da kun qi da kun so ku bi ni ba
  ra‟ayi ba”. Su kuma su ce maigida bisa
  kan dutse, ubangijin Mama, bi mun bi ka,
  ba a ra‟ayi ba”. Suna faxar wannan suna
  kewaye ginin (suna xawafi) har hudowar
  alfijir, sa‟an nan su tsaya tsirara su ci
  abinci. Ya fito, ya ba su labarin dukkan
  abin da zai faru cikin dukkan wannan
  shekara, har da baqon da zai fuskanto           78
Kano Qwaryar Qira…...

  zuwa wannan gari, ko na alheri ne ko na
  sharri ne. Shi ne ma ya ba su labarin
  gushewar mulkinsu da sarewar itaciyarsu
  da qonewarta da ginin wannan
  masallaci. Kuma ya ce musu wani mutum
  zai zo wannan gari tare da rundunarsa,
  ya mallake mu”. Suka ce masa” don me
  ka faxi wannan? Wannan magana ce
  mummuna, ya yi shiru. Sa‟an nan ya ce
  da sannu ku gan shi da alfarmar
  Tsumburbura! Idan bai zo a zamaninku
  ba, ya zo a zamanin „ya‟yanku, ya
  mallaki dukkan wanda ya samu a cikin
  wannan qasa, dukkanta, ya sa a manta da
  ku duk da jama‟arku, ya kuma bayyana
  da qabila tasa zamani mai tsawo.”

   Wannan duba na Barbushe bai yi wa
mabiyansa daxi ba, don haka suka yi baqin ciki
qwarai suka ce masa qaqa za mu yi mu kawar da
wannan al‟amari? Ya ba su amsa da cewa ba yadda
za ku yi sai haquri. Wataqila Barbushe ya hango
wani gagarumin juyi, wanda qabilar Maxatai za ta
zo da shi wanda zai haxiye qabila tasa da sannu, shi
ya sa ya yi wannan duba cikin tsafinsa, ya ga abin
da ya gani na wannan juyi ya gaya wa mabiyansa.
            79
           …………….Daga Dutsen Dala

KOGIN JAKARA
    Koda yake waxannan qabilu ba lokaci xaya
suka zo Kano ba, kuma ba gaba xaya suka zo ba,
a‟a kaxan-kaxan suka dinga zuwa har suka taru
suka yi qungiya iri biyu, qungiyar Dala ta masu
bautar gunki, wato Tsumburbura da qungiyar „Yan
farauta. Lokacin da waxannan qungiyoyi suke
zaune a Kano suna zaune kusa da juna, amma
kogin Jakara da manya-manyan itatuwan da suke
kewaye da kogin su ne suka raba su, qabilar Dala
tana arewa da ita, qabilar Maxatai tana kudu da
ita. Ita dai Jakara wata qorama ce wadda ta faro
daga wani guri, yammacin birni, wanda ake kira
bulbula, a Aisami, gabas da Gwauron Dutse. Ta
keta ta Dausayi ta Karofin Wanka-da-Shuni, ta
cikin Kasuwar kurmi, ta yi gabas har ta je Wasai
ta qasar Minjibir, ta miqe da tafiya har ta kai
Duku, ta qasar Garkin Xirani, inda ta qare, ba ta
sake tafiya ko ina ba.
    Wannan qorama da duhuwarta su ne suka
raba waxannan qabilu gudu biyu, kamar yadda
muka faxa a baya. To su waxannan qabilu tun
zuwan su, sun tarar da mazauna wannan guri na
asali, suka zauna tare da su, suka koya musu irin
sababbin dabarun zaman duniya da suka zo da su
daga inda suka yiwo qaura, waxanda mazauna
wannan guri na asali ba su san su ba.            80
Kano Qwaryar Qira…...

    Kafin Dala, Kakan Barbushe ubangijin
Tsumburbura, ya zo wannan gari, akwai mutane
da suke zaune a nan suna rayuwa irin tasu.
Mutanen da suke zaune a wannan guri, kafin
zuwan Dala qabilu ne iri daban-daban, kuma suna
zaune ne zama irin na rinji. Zaman rinji shi ne
zaman da kowane maigida yake zaune a
qungiyarsa, a waje xaya wadda ta haxa gidansa da
gidan „ya‟yansa da na qannensa da kuma na
barorinsa, ko kuma na waxansu mutane daban da
suka kawo caffa gurinsa don ya riqe su, kamar
yayansa. Kowane rinji akwai sana‟ar da aka san
shi da ita, kuma mutanen da suke zaune cikin
rinjin an san iyakar wuraren da suka mallaka don
noma da waxansu ayyuka na sana‟a.
    Kamar yadda littafin Tarihin Kano ya faxa
wasu daga cikin mutanen da Dala ya samu a nan
suna zaune ne kusa da kan Dutsen Dala, inda shi
kansa ya hau ya gina nasa gidan. Waxannan
mutane kamar yadda tarihin Kano ya bayyana su
ne: Gunzago mai gida a qarqashin Goron-Dutse da
Gagiwa wanda yake kama giwa da igiya don
qarfinsa da Gubanasu da Ibrahim da Bardoje da
Nisau da Kamfatsu da Duje da Janberi da
Gamakora da Gaftaro da Hangugu da Qar-dangi.
Waxannan mutane su ne tarihin Kano ya bayyana
su da cewa su ne muqarraban Barbushe, jikan            81
           …………….Daga Dutsen Dala

Dala. Wataqila ma auratayya ce ta haxa
kakanninsu da qabilar Dala wadda ya zo da ita har
wannan dangantaka ta samu tsakaninsu.
    Har ila yau akwai wasu Rinjinan (Rijau) da
shugabanninsu suka yi caffa ga Dala da gunkinsa
koda yake su ma zaman kansu suke yi, kuma nesa
da Dala suke. Waxannan qabilu su ne :
    (1) Qabilar Xanvuru wanda yake zauna a
Jigirya, wajen mil goma gabas da Dala.
    (2) Qabilar Jandamisa wanda ake kira
Ruma. Shi kuwa a kan Dutsen Magwam yake,
wato Nassarawa ta yanzu, kuma qabilar wannan
mutum wato Rumawa sun fi kowace qabila yawa a
Kano a wancan lokacin. Domin su ne suka yaxu
tun daga inda suke har zuwa Salanta wato kudu da
Dala kamar mil goma.
    (3) Sai Qabilar Hamvarau waxanda suke
zaune a kan Dutsen Tanagar.
    (4) Qabilar Nisau waxanda suka zauna a
kan Dutsen Fanisau. Shi Nisau shi ne uban
Gumban xaya daga cikin manyan da suke bin
Tsumburbura da Barbushe.

JAKARA AKE BAUTAWA KAFIN
TSUMBURBURA
   Kafin Dala ya zo garin nan ya kawo dabarar
bautar gunki, da gina masa xaki na musamman,            82
Kano Qwaryar Qira…...

mutanen wannan guri da maqwabtansu na kusa
ruwa suke bautawa da duhuwar da ta kewaye
ruwan. Wato tabki, ko babban gulbi, mai ruwa da
yawa, wanda ba ya qafewa rani da damina, kuma
manyan bishiyoyi sun yi masa duhuwa, suna zubar
da ganyayyakinsu a cikinsa har ruwan ya zama
baqi qirin. Irin waxannan ruwaye su ake kira
“shu‟umi” wato wanda ba a san kansa ba ke nan.
Ko kuma a ce ruwan yana da aljannu, da „yan
ruwa da Maikilago, masu cinye mutane. Mutanen
da suke zaune daga cikin irin waxannan ruwaye da
aka sani har yanzu su ne, Gulbin Auyo, Tafkin
Xankwai da Kurmin Baqin-ruwa wato Jakara ke
nan.
    A lokacin da ake bauta wa Jakara, qwaryar
tafkinta ya taso ne tun daga unguwar Baqin-ruwa
ta Rijiya-huxu, ta Karofin Wanka-da-shuni, ya
mamaye har Larabar Kanawa ta cikin Kasuwar
Kurmi. Duk kuwa duhuwa ta kewaye wannan guri
a da can, don haka ruwan ya zama baqi kuma
mutane suke bauta masa. Tarihin Kano ya bayyana
wannan siffa ta qwaryar Jakara da irin bautar da
ake mata inda ya ce(12):
   “ana ambaton ta Kurmin Baqin-ruwa,
   domin shi ruwa ne baqi, duhuwa ta
   kewaye shi, ana kiyaye dukkan masiba da
   ita da gunkinsu, mafarinta kuwa daga            83
           …………….Daga Dutsen Dala

   Gurgumasa har zuwa Dausara. Qirarinta
   da zartakenta ba su motsi, sai idan
   masiba ta gabato wannan gari ya yi
   kururuwa sau uku, hayaqi ya riqa fitowa
   daga cikin Tsumburbura, wanda ke cikin
   tsakiyar ruwan, sai su nemi baqin kare su
   yanka a qarqashin Tsumburbura, kuma
   su nemi baqin bunsuru a cikin duhuwar.
   Idan hayaqi da kururuwa sun daxu, sai
   masiba ta sadu da su, idan kuwa ba su
   haxu ba, babu masiba. Sunan duhuwan
   nan kuwa Madawa, kuma sunan
   Tsumburbura Randaya”.
   Bayan musulunci ya bayyana an daina bautar
Jakara sai aka yi mata Sarkin Jakara wanda shi ne
ya ke yi mata hanya in ta cika.
            84
Kano Qwaryar Qira…...

        SASHI NA HUXU
   MASARAUTUN KANO NA FARKO
  An sami savanin ra'ayi a tsakanin masu bada
labari a kan tarihin Kano game da masarauta ta
farko, kamar yadda Malam Adamu na Ma'aji ya
faxa.(1) Wasu suna ganin an fara kafa masarauta a
Kano a farkon qarni na uku bayan haihuwar
Annabi Isa, wato a farkon A.D. 300. Masu wannan
ra'ayi suna ganin zuwan Dala Kano daga Dahalak
ta qasar Habasha a lokacin mulkin Habashawa
masu bautar ruwan Jakara da tsafin da ya zo da shi
tare da sabuwar hanyar bauta ta gunkin
Tsumburbura, ita ce lokacin kafa hukumar Kano ta
farko. Domin Dala da jikokinsa su Barbushe sun
mallaki mutanen gurin na asali na qabilun
Qwararrafa, da Abagayawa masu bautar ruwan
Jakara a qarqashin shugabansu Mazauda, Tarihil-
Arbab Hazal Baladi (Tarihin Kano), yayi bayanin
wannan hukuma ta farko a Kano, da shugabanninta
na wancan lokacin, kamar yadda za a karanta a nan
gaba kaxan.
    Hukumar Kano ta biyu kuma an kafa ta ne
farkon qarni na biyar, bayan haihuwar Annabi Isa,
wato A.D 500 ke nan. Masu wannan ra'ayi kuma
suna da'awar zuwan Bagauda da 'yan farautarsa da
suka zauna a Maxatai Kano shi ne farkon kafa
Masarauta a Kano. Tarihin Kano bai yi bayani a            85
           …………….Daga Dutsen Dala

kan zuwan Bagauda Kano da kafa hukumarsa ba.
Saboda haka ya bar babban givi a tarihin
mutanenta. Amma an yi sa'a waqar Bagauda ta
tarihin Kano ta cike wannan givin. An ce Bagauda
da mutanensa sun taho Kano ne daga wasu
qauyuka na qasar Gaya, irin su Batayya, da
Gwagwaranda da Kadaimi. Da suka zo Kano sai
suka yi zangonsu a Maxatai, inda suka zauna. Ita
kuma Gaya a wancan lokaci ba gari ba ne, asali
zango ne a kusa da Kadaimi inda masu hijira daga
gabas da arewa maso gabas suke sauka su huta,
kafin su qaraso Kano. Mutanen da suke kusa da
gurin suna cewa gurin “Gayyar mutane", har aka
zo ana kiran gurin Gayya daga qarshe gurin ya
zama gari ana kiransa Gaya. Kamar yadda "Fagen
kayan rafi” na gabas da birnin Kano, wanda
Buzaye da Barebari suka kafa ya qasaita aka
mayar da shi garin Fagge a yanzu. Game da
hukumar Bagauda wacce ya kafa a Maxatai ga
abin da waqar ta faxa:
    Bagauda shi ya sari Kano da farko
    Ta na daji sa'annan babu kowa.

   Ta na dawa qirmiji sai ko gumakai
   Da Imbeci da Vaunaye da Giwa.
           86
Kano Qwaryar Qira…...

   Yana Gaya shi Bagauda na garinsa
   Maharbi ne riqaqqe mai kashewa.

   Da yazo cirani yai zango Maxatai
   Ya zauna 'yan uwansa suna tahowa.

   Maharba gurguzu suka xora taro
   A gurinsa suna kisan Zaki da Giwa.

   Da nama yai yawa xanye qafaffe
   Fa ba mata maza ne ke dafawa.

   Madafa da yawa bukka da bukka
   Fa sai aike fa mata na tahowa.

   Ga Gwale da shi da Yakasai da Sheshe
   Ga Guguwa manya-manyan Maguzawa.

    Za‟a yi qarin bayanin wannan a hukuma ta
biyu ta Bagauda.

KAFA HUKUMAR FARKO A KANO
   Addini da sarauta aikin su iri xaya ne, shi ne
haxa dangantaka tsakanin shugaba da mabiyansa.
Wannan dangantaka tsakanin shugaba da
mabiyansa ta na bada wasu fa‟idoji na arziqi da
girma ga shugabanni. Kuma ta baiwa mabiya            87
            …………….Daga Dutsen Dala

zumunci da „yan uwantaka a tsakaninsu.
waxannan fa‟idoji sune suke kawo zaman lafiya
da qaunar juna da auratayya a tsakanin mabiya.
Wannan kuma shi ya ke kawo yaxuwar arziqin
mabiya na kasuwanci da noma da sana‟a.
   Lokacin da Kanawan farko suke zaune a
nan, tsari irin na sarauta, kamar yadda ake yi a
yanzu bai zo musu ba, saboda haka basu da Sarki.
Amma shugabansu na addini, wato Mazauda, shi
ne shugaba mai bada umarni na hani da horo. A
qarqashinsa akwai shugabannin qabilu guda goma
sha xaya wanda yake tafi da al‟amuran yau da
kullum tare da taimakonsu. Wato sun zama sune
„yan majalisa, kuma kowace qabila cikin qabilun
goma sha xaya, tana da sana‟ar da ta qware akai,
aka san ta da ita saboda taimakon sauran. Ga kuma
yadda tsarin zaman mulkin na su yake(2):

Lamba   Suna        Sana’a
 1    Mazauda   Limamin Bautar Jakara
            da bukukuwan ta. Mai
            bada umarni na hani da
            horo, shi ne kakan
            Sarkin Makafi.
  2    Giji-Giji  Maqerin kayan aikin
            gona da na farauta. An
            ce shi ne kakan            88
Kano Qwaryar Qira…...

          Abagayawa na Maqera.
          Wataqila    wannan
          mutum shi ne Kanoki,
          wanda yayi wo qaura
          daga Gaya, aka sawa
          Kano sunan sa.
 3   Bugazau  Shi ne mai dafa giya
          saboda   bukukuwan
          addini da nishaxin
          sauran jama‟a.
 4   Hamvurki Shi ne mai daka
          magunguna na itace da
          ganyenyaki   domin
          warkarwa.    Matan
          Maguzawa sune su ke
          yin tallan magani a
          Kano. Ana kiran su „yar
          mai ganye.
 5   Xanvintinya Shi ne mai sadawa
          tsakanin qabilun Dala
          da    Maqwabtansu.
          Kuma ya kanyi aikin
          Sankurmi, mai tsare
          masu laifi.
            89
         …………….Daga Dutsen Dala


6  Doran Maje Shi ne mai kula da
        tarbiyar Samari da
        „Yan mata. Shi ne
        Sarkin Samari a Datsa
        ko       Dandalin
        wasanannin Samari da
        „Yan mata.
7  Jan Dodo Shi ne Sarkin makaxa
        da raye – rayen tsafi, da
        farauta, da wasannin
        samari da „yan mata.
        Gangunan su na tsafi
        sune, Kuru da tsintsima
        da gunduwa.
8   Magaji  Shi    ne   Kakan
        Maguzawa, shi ne mai
        fitar da qarfe daga qasa,
        kuma ya narka shi
        (wataqila    wannan
        mutum shi Kanoki ya
        samu yana yin qarfe da
        tamar da ake samu a
        Dala. Suka zauna tare
        har suka zama xaya)
         90
Kano Qwaryar Qira…...


 9    Asanne  Shi ne kakan mawaqa,
          shi ne kuma sarkin su
          na rawa da waqa ta
          rawar tuji. Wannan
          rawa tsirara ake yin ta,
          Maza da Mata a gidan
          Sarki   da  Gidajen
          hakiman sa, a ranakun
          sallah qarama da sallah
          babba. Shi kuma sarki
          ya fito da banten
          Darazau da mayafi na
          bunu tare da magajiya
          su kalla. An daina
          rawar tuji bayan an
          rushe      gunkin
          tsumburbura.
 10   Baqon yaqi Shi ne Sarkin Maharba
          mai yin kwari da baka
          domin yaqi da farauta.
 11    Awar   Shi ne kakan awarawa
          shi ne mai yin gishirin
          awar.   Kuma   yayi
          Sarkin ruwan duk
          wannan qasa ta Kano.
            91
           …………….Daga Dutsen Dala

   Dukkan waxannan mutane da muka lissafa
a sama, kowanne xayan su yana da qabila tasa
masu yawa, kuma sune asalin Kano. Sune suka
qafa mulkin farko a Kano na jamhuriyya, wato
Republic da turanci, domin basu da Sarki basu da
Talaka sai mai bada umarni na hani da horo da
masu karva su aiwatar, saboda tafi da aiyukan
jama‟a.

QABILUN DA SUKE NESA DA JAKARA(3)
    Idan ka dubi yadda waxannan qabilu goma
sha xaya suke zaman duniyarsu, za ka ga cewa
dukkansu sun yarda da aikin kowanensu, kuma
sun dogara da shi, kamar yadda shi ma ya dogara
da su. To har ila yau ban da su akwai wasu qabilun
„yan‟uwansu da suke zaune a nahiyoyin nan huxu.
Waxannan nahiyoyi ana kiran su da waxansu
sunaye a wancan lokacin. Amma a yanzu
waxannan sunaye sun vata. Jakara a da ita ce
cibiyar waxannan nahiyoyi, wato daga ita ake yin
kwatancen kowace nahiya. Gabas da yamma kudu
da arewa. Ga yadda littafin Tarihin Kano ya
lasafta waxannan nahoyoyi da kuma sunayensu
daga Jakara. Tuni dai ka ji yadda Jakara ta raba
birnin Kano na yanzu biyu, wato kudu da arewa.
To wannan rabon a da duk qasar Kano ne gaba
            92
Kano Qwaryar Qira…...

xaya kamar yadda na faxa cewa littafin Tarihin
Kano ya yi, kuma ga yadda yake:

Lamba     Arewa Da    Sunan
        Jakara     Nahoyiyinta
1.       Daga Jakara  Gazarzawa
        zuwa      Sheme
        Damargu
        Daga
        Damargu
        zuwa Kazaure
        Waxannan
        nahiyoyi su
        ne suka haxe
        da Daura da
        Zinder ta
        Damagaram
            93
      …………….Daga Dutsen Dala

2.  Kudu Da    Zadawa
   Jakara     Funkui
   Daga Jakara  Sheriya
   zuwa Santolo  Gaude
   Daga Santolo
   zuwa Barku
   Daga Santolo
   zuwa Shike
   Daga Barku
   zuwa Kara
   Daga Kara
   zuwa
   Ammango
   Waxannan
   nahiyoyi su
   ne suka yi
   iyaka da
   Bauchi

3.  Gabas Da   Rauna
   Jakara    Tokawa
   Daga Bampai
   zuwa Wasai
   Daga
   Karmashe
   zuwa Ringim,
   A  wannan      94
Kano Qwaryar Qira…...

        lokacin   ne
        mulkin Auyo
        ya zo har
        Ringim tun da
        a   wannan
        lokaci   ba
        mulki a Kano,
        kowa zaman
        bilkara yake
        yi sai dai
        bautar Jakara
4.       Yamma Da    Dundunzuru
        Jakara
        Daga Watari
        zuwa Dutsen
        Karya.
        A   wannan
        nahiya ne ake
        samun
        garuruwa irin
        na su Tuda da
        Xanbaqoshi
        da Duji da
        Xankwai
   Duk qabilun da suke waxannan nahiyoyi da
muka ambata sun san mutanen da suke a Jakara,
su ma na Jakaran sun san su, amma ba wani mai            95
           …………….Daga Dutsen Dala

bin wani, domin kuwa kowa yana da abin bautarsa
ko ruwa ko itace ko daji. Idan mutum ya lura da
wannan tsari sai ya ga cewa nahiyoyin Gazarzawa
da Sheme sun yi iyaka da mulkin Daura da
Katsina daga arewa. Daga kudu kuma nahiyoyin
Zadawa da Funkui da Sheriya da Gauda da Gaji,
sun yi iyaka da wuraren da suka zama Bauchi da
Zariya. Haka kuma nahiyoyin Rauna da Tokawa
suka yi iyaka da mulkin Auyo wanda su ma ruwa
suke bautawa. Yamma kuma Dunduzuru ita ma ta
yi iyaka da abin da ya zama qasar Katsina daga
baya. Duk waxannan iyakoki da muka ambata, da
babu su a wannan lokacin don kuwa ba wani sarki
da ya mallaki wuraren balle ya kafa iyaka. Amma
daga baya da mulki ya kafu a Kano, waxannan
nahiyoyi su ne suka zama tushen qasashen Kano
gaba xaya, waxanda sarakuna suka yi ta yaqi da su
har suka haxe su da Kano. Kuma wani wurin suka
faxaxa nahiyar har ta kai faxin qasar Kano ta yau.
Nan gaba za ka karanta yadda „ya‟yan Bagauda
suka yi qoqarin haxe waxannan nahiyoyi don su
zama qarqashin mulki guda wato mulkin Kano.
Wannan rigima ta haxe waxannan nahiyoyi da
garuruwan da suke ciki don su zama qasashen
Kano ita ce ta ci gaba tun daga farkon mulkin
Have har zuwa mulkin Fulani.
            96
Kano Qwaryar Qira…...

MA’ANAR HANGEN NESAN BARBUSHE(4)
    Kirdadon Barbushe da hangen nesan da ya
yi a lokacin da ya gaya wa mabiyansa cewa wani
mutum zai zo wannan gari ya kau da gunkinsu ya
mallake su, ya mai da su ba komai ba, ba kawai ya
yi shi ne don tsafinsa ya gaya masa ba, a‟a
wataqila shi kansa ya gano wani juyi ne da su
mabiyansa basu gani ba. Wataqila Barbaushe ya
lura da shigowa da baqi suke yi a kullum suna
daxa qaruwa, har ya fahimci cewa waxannan baqi
komai daxewa sai sun rinjayi mazauna wannan
guri na asali, wato mabiyan Tsumburbura.
    To abin tambaya a nan shi ne su wane
waxannan mutane da Barbushe ya ce za su zo su
mallaki mabiyan Tsumburbura? Kuma menene
bambancinsu da mutanen wannan gurin? Kamar
yadda Malam Adamu Na Ma‟aji ya faxa a cikin
littafinsa, mazauna wannan guri da a yanzu ake
kiransa Kano qabilun Qwararrafa ne kuma su ne
irin qabilun da suka zama Warjawa da Kulawa da
Umbutu, wato qabilun da a yanzu suke zaune a
qasashen Sumaila da Birnin Kudu da Ningi.
Sauran kuwa wasu an haxiye su sun zama
Hausawa ko kuma sun gudu sun yi kudu inda suka
yi Bauchi da kudancin Zariya da Fulato da wani
gari na Kogin Binuwai wato qasar Jukun a taqaice.
            97
            …………….Daga Dutsen Dala

    Lokacin da waxannan qabilu suke zaune a
wannan guri, sannan gurin yana da qoramu masu
ruwa da yawa kuma ga itatuwa da daji mai yawan
ruwa da isasshen abincin dabbobi wanda ya jawo
namun daji iri daban-daban, kamar su giwa da
zaki da vauna da sauran namun da ake farautarsu.
Waxannan namun daji su ne suka jawo „yan
farauta daga wasu tsofaffin garuruwa daga varin
gabas da arewa da wannan guri. Waxannan
tsofaffin gurare su ne kamar su Gaya da Auyo da
Garun gabas da Daura. Daga arewa kuma guraren
su ne irin su Daura da Tumbi da Washa.
Waxannan „yan farauta tun suna zuwa suna yin
farautar cin rani, wato su zo bayan sun girbe
amfanin gonarsu, sannan su zo su yi farauta su
sami nama mai yawa su koma gida, har dai suka
ga gurin ya yi musu daidai saboda lafiya tasa, suka
xebo iyalinsu suka tare a wurin.
    Bayan „yan farautar nan sun zauna da
gindinsu, sai suka ga ma ya kamata suyi noma a
nan domin kuwa ga daji nan mai yawa na Allah ba
mai shi. Saboda haka sai suka yi ta kama gonaki
suna yin noman dawa da gero. Da yake sabon daji
ne ba a tava noma a cikinsa ba, sai Allah ya bai wa
gonakin nan nasu albarka, suka girbi hatsi mai
yawa da ba su san yadda za su yi da shi ba, domin
kuwa yafi qarfin cin su komai yawansu a wannan            98
Kano Qwaryar Qira…...

lokaci. To ana cikin wannan hali ne na wadatar
abinci a nan sai yunwa mai tsanani ta afka wa
Afirka ya tamma. Da qabilun waxannan gurare da
yunwa ta afkawa suka sami labarin ba inda ake
samun hatsi sai nan garin, sai kuwa suka fara
takowa daga ko‟ina, gabas da yamma kudu da
arewa. Qabilu irin su Barnawa da Katsinawa da
Daurawa da Zamfarawa da Gobirawa duk suka zo
suna sayen hatsi, kai wasu qabilun ma kamar su
Kabawa da Kambarawa da Adarawa duk sai suka
tare a nan. Haka kuma da yunwar ta hayaqa ta
watsa Azbin su ma sai suka gudo nan don su sami
waraka.

TSARIN RAYUWAR QABILAR DALA(5)
   Kafin mu ci gaba da bayanin qabilar
Maxatai, wadda aka fi sani da qabilar Bagauda, ya
kamata mu duba tsarin rayuwar qabilar Dala da
maqwabtanta, don mu ga menene matsayinsu na
rayuwa a kan harkar arziqin qasa da rayuwar jin
daxinsu a wancan lokaci. Yin hakan zai ba mu
dama mu yi makari na tsakanin tasu rayuwar da
kuma rayuwar kishiyarsu, qabilar Maxatai, idan
muka zo bayanin rayuwarta. Kamar yadda muka
gani a baya, qabilun da suka haxu suka yi qabilar
Dala qungiyoyi ne na manoma da sana‟o‟i. Wato
ban da noma kowace qabila tana da sana‟ar da ta            99
           …………….Daga Dutsen Dala

qware, a cikinta, tana yi saboda sarrafa abubuwan
rayuwa da musayar abubuwan buqata na rayuwar
yau da kullum. Misali Rinjn da ake yin qirar kayan
noma da ayyukan gida sai ya yi musaya da abin da
Rinjin masu yin gishiri yake yi don su biyun su
sami buqata tasu. Irin wannan zama, zama ne na
koma baya, tun da babu shigowar baqi da fita tasu,
kuma babu fatauci da hada-hada, wato abin da ake
kira da Turanci (External trade). A saboda
wannan ne kowace qabila ba ta noma fiye da abin
da take buqata ya ishe ta a shekara. Gama kuma
idan ta noma fiye da buqata to wanene zai saye
sauran? wato (Surplus). Saboda haka zaman
hannu-baka-hannu qwarya suke yi, su ba sa
fatauci, kuma babu ciniki mai zuwa musu daga
nesa. (wato (External trade).
    Wajen kuma rayuwarsu ta jin daxi da
sakewa nan ma zaman koma baya suke yi. Domin
a wannan lokacin gwado suke yafawa kuma su
xaura bante a gindinsu. Ga kuma yawan shan giya
a duk lokacin bukukuwansu na addini. Haka kuma
aka ce a lokacin ba su da dabbobin hawa da na
xaukar kaya, irin su doki da jaki da shanu.
Waxannan sun zo musu ne daga baya a lokacin da
qabilar Maxatai ta zo da su. Wajen shugabanci
kuma qabilun Dala ba su da Sarki da fadawa,
kuma ba su da masu kuxi. Shugabanninsu na           100
Kano Qwaryar Qira…...

addini ne kawai wanda Mazauda shi ne babbansu,
kuma shi ne wakilin Barbushe, wanda ya zauna a
kan Dutsen Dala. Tun da ba su da sarki ba su da
„yan kasuwa to ba su da masu yi musu zalunci tun
da  babu   bambancin   tsakanin  mutane.
Shugabanninsu na addini ne, girma kawai suke
samu daga sauran jama‟a masu bin su, amma babu
wani mata‟i da ake ba su bayan girman.
   A taqaice dai qabilun Dala su ake kira da
Turanci (Classless Society). Wato jama‟ar da ba
talaka ba saraki ba masu kuxi a cikinta, kowa
daidai yake da kowa babu qungiyar jari hujja
(wato capitalism).
            101
            …………….Daga Dutsen Dala

      SASHI NA BIYAR
    ZUWAN QABILAR MAXATAI:

    Labarin hijira ta biyu wadda ta biyo bayan
hijirar Dala ta sha bamban da ta Dala xin. Littafin
tarihin Kano ya yi bayani mai tsawo a kan zuwan
qabilar Dala Kano da duk abin da suka zo da shi,
kamar yadda muka yi bayani a baya. Amma shi
wannan littafi bai zo da wani abu na tarihin qabila
ta biyu ba, wato qabilar Maxatai. Kuma ba ma
wani littafi na tarihin Kano da ya zo da tarihin
qabilar Maxatai. Wannan kuwa givi ne mai faxi a
wajen rubuta tarihin Kano. Sai dai mun yi sa‟a
waqar Bagauda(1) ta cike wannan givi, inda ta
kawo cikakken labarin qungiyar da tasirin da ta yi
a Kano, wanda ya canja gaba xayan rayuwar
Kanawa. Wannan canji kuwa an gane shi ne ta irin
yadda hanyar noma ta canja ta zama sabuwa mai
inganci.
    In an tuna dai a baya mun ga inda aka ce
manoma daga Yaman sun yiwo qaura daga can
zuwa nan qasar, bayan madatsar ruwa ta Saddu
Ma’arib (Ma‟arib Dam) ta fashe, kuma suka qare
hijira tasu a Gaya. Haka kuma aka ce qabilun
Magharib, masu tafiya suna farauta suna noma,
don su tsira daga mulkin mallaka su ma a Gaya
xin suka yi zangon su na qarshe kafin su iso Kano.            102
Kano Qwaryar Qira…...

Ba a san haqiqar lokacin da waxannan qabilu suka
zo wannan qasar ba, amma tun lokacin da suka zo
xin sun yi cuxanya da mutanen da suka tarar a
nan, suka koya musu sabuwar hanyar noma
musamman noman rani, kuma suka kawo iri
wanda babu shi a nan qasar, kamar su alkama,
albasa da tumatur.
    Waxannan mutane su ne suka koya wa
mutanen qasar nan yadda ake yin noma ta hanyar
ilimi da qwarewa. A sari daji a yi gona mai
kusurwa huxu ko uku, amma ba mai da‟ira ba.
Sannan a kewaye gonar da itatuwa waxanda suke
jure qarancin ruwa, irin su jema da ararravi da
bini-da-zugu da fid-da-sartse, da sauran irin su,
waxanda suke nuna iyakar gonar kowane manomi.
Bayan an yi iyaka sai kuma a yi kunya-kunya a
cikin gonar sannan a yi kadada a cikinta. Ta haka
ne manomi zai san yawan kwanakin da zai yi
kafin ya qare noman gona tasa, a kowace damina.
    Haka kuma wajen noman rani sun koya
yadda ake nome guri a bakin kogi, ko tafki ko
qorama, a share yayin a raba gonar fangali-fangali,
sannan a yi hanyar ruwa wadda za ta shayar da
shukar da aka yi a cikin waxannan fangaloli. A yi
jigo da guga na xebo ruwa daga inda yake don ban
ruwan shukar rani. Da haka ake kulawa da shukar
rani ana renon ta har ta nuna a ci amfanin ta.            103
           …………….Daga Dutsen Dala

Wannan hanya ta ilimin noma na rani da na
damina ya bunqasa ne tun daga Duddurun Gaya
har zuwa Kogin Chalawa (za ka ga garuruwan da
waxannan manoma suka fito da wanda aka kafa a
nan bayan zuwan su, duk a bakin kogin Dudduru
da na Chalawa). To wannan shi ne abin da qabilar
Maxatai ta zo da shi daga Gaya ta hannun „yan
farauta waxanda suka koma noma daga baya, har
Kano ta bunqasa, saboda noma, masana‟antu da
kasuwanci. To, waxannan mutane waxanda suka
zo mana da wannan sabuwar hanyar noma su ake
kira qabilar Maxatai kamar yadda za ka karanta a
qasa.
    Kamar yadda muka yi bayani akan qabilun
Dala da irin halin zamansu na harkar rayuwa ta
zaman cuxanya da juna a harkar arziqin qasa, haka
kuma za mu duba yadda qabilar Maxatai ita ma ta
faru, kuma ta yi nata zaman rayuwar.
    Kamar yadda waqar Bagauda ta faxa,
qabilar Maxatai ta samo asali ne tun daga zuwan
waxansu „yan farauta zuwa wannan guri da ake
kira Kano. Waxannan „yan farauta sun zo ne daga
wasu qauyuka na qasar Gaya, misalin kilomita
sittin gabas maso kudu daga birnin Kano.
Waxannan qauyuka da aka ce qungiyar „yan
farautar sun zo daga can su ne Tsangaya da
Batayya da Kadaimi da Gwagwarandan da Gaya.           104
Kano Qwaryar Qira…...

Waxannan qauyuka ba su da nisa daga Duddurun
Gaya inda aka ce Yamalawa sun zauna a gurin.
    A wancan lokacin qungiyoyin „yan farauta
irin ta masu yawon farauta daga wannan guri zuwa
wancan ana kiran ta “vago” da Hausa, kamar
yadda Mahadi (1978)(2) ya rubuta a cikin littafinsa.
Irin wancan qungiyar a qalla tana qunsar mutane
kamar xari biyu zuwa xari uku a cikinta. To ka ga
ashe inda duk wannan irin qungiya ta sauka gurin
kuwa ya zama gari. Da waxannan suka iso Kano
sai suka sami namun daji iri-iri, manya da qanana,
irin su Zaki da Giwa da Vauna. Qananan kuma
irin su Barewa da Gada da Gwanki da sauransu.
    Saboda haka, sai suka kafa bukkokinsu a
Tudun Maxatai, wanda a yanzu ba shi da nisa daga
fadar Sarkin Kano, suka yi ta xiban nama, na gashi
da na dahuwa mai yawa a kowace bukka, kuma
suna aikawa da qafaffe zuwa ga iyalinsu da kuma
inda ake buqata.
    Da labarin wannan gagarumar nasara da
waxannan „yan farauta suka samu ta je kunnen
„yan‟uwansu maharba na nesa, sai suka dinga
zuwa wajen su a nan Kano don su ma su ci
albarkacin da „yan‟uwansu suka samu a gurin.
Garin wannan ne ya sa su „yan farautar da suka
fara zuwa suka ga ya kamata su yi kaka-gida a nan
su zauna tare da iyalinsu zama na din-din-din. Don            105
           …………….Daga Dutsen Dala

haka sai suka aika iyalansu duk su taso daga
qauyukan da suke a da, su komo Kano su zauna
tare da su. Ka ga a nan an maimaita abin da
Kanoki ya yi, wato hijira daga Gaya zuwa Kano,
amma ba don neman tama ba.
    Da waxannan „yan farauta suka yi kaka-
gida, suna yawon farauta tasu sai kuma suka gane
cewar qasar Kano, qasar noma ce, domin kuwa
budurwar qasa ce mai albarka. Saboda haka sai
suka fara yin noman abinci. Waqar Bagauda ta ba
da sunayen mutanen da suka fara komawa sana‟ar
noma daga cikin shugabannin „yan farautar nan.
Waqar ta nuna su kamar haka:-

  Lamba     Sunaye     Inda suke a
                  yanzu
  1.    Gwale       Cikin birni
  2.    Yakasai      Cikin birni
  3.    Sheshe      Cikin birni
  4.    Guguwa      Dawakin Tofa

   Kowane xaya daga cikin waxannan
shugabanni sai ya kama wurin noma wanda a
yanzu ake kiran gurin da sunansa. Uku daga cikin
waxannan sunayen wato Gwale da Yakasai da
Sheshe unguwanni ne a cikin Birnin Kano. Na           106
Kano Qwaryar Qira…...

huxun kuwa, wato Xanguguwa garin dagaci ne a
qasar Dawakin Tofa.

ZUWAN SABON JUYIN JUYA HALI
NA ARZIQIN QASA(3)
    Ba wanda yasan dalilin da yasa waxannan
shugabanni suka mai da hankalin su akan noma,
bayan farauta, amma ganin ximbin nasarar da suka
yi ta samun abinci mai yawa a wannan noma, sai
tasa duk sauran „yan farautar ma suka mai da
hankali wajen noma. Cikin xan lokaci kaxan sai
noma ya havaka a Kano aka yi abinci wanda yafi
qarfin mutanen da suka noma shi.
    Da wannan abinci ya taru aka rasa yadda
za‟ayi da shi, sai kuma Allah ya kawo yunwa a
duk qasar Afrika ta yamma. Ba inda ake samun
abinci sai dai an zo nan Kano. To fa wannan hali
shi yasa qabilun shauran qasashe suka dinga barin
garuruwansu suna gudowa Kano don su tsira daga
masifar yunwa. Waxanda suka fara gudowa daga
garuruwan su, kamar yadda waqar Bagauda ta
nuna sune:
            107
            …………….Daga Dutsen Dala

Lamba     Sunaye      Inda suke a
                  yanzu
1.    Barnawa       Borno
     (Barebari)
2.    Katsinawa      Katsina
3.    Daurawa       Daura
4.    Zamfarawa      Zamfara
5.    Gobirawa       Gobir
6.    Kabawa        Birnin Kebbi
7.    Kambarawa
8.    Adarawa       Birnin    Adara
               (Niger)
9.    Azbinawa       Birnin    Azbin
               (Niger)

   Zuwan waxannan qabilu Kano ya kawo
bunqasar ciniki da sana‟oi. Domin kuwa ko wacce
qabila ta zo da abin da ta qware a ciki na sana‟a da
dabarar sarrafa abin duniya don xan adam yayi
amfani da shi. Kowa zai yi sana‟ar da ya iya don
ya sayar ya samu abin sayen abinci da sauran
buqatun kansa da na iyalinsa. Nan da nan Kano sai
ta havaka da masana‟antu daban – daban kamar
Marina, da Masaqa, da Maqera, da Masassaqa da
dai sauransu. Kuma a sakamakon wannan ne su
Mafarautan nan da suka komo noma, suka zama            108
Kano Qwaryar Qira…...

manyan attajirai. Suka tara dukiya mai yawa, ta
bayi da dawakai da raquma da abubuwan da ba‟a
tava sani ba a nan Kano kafin wannan juyin na
noma ya zo.
   Ko da yake daga bisani Allah ya kawo
sauqin wannan yunwa kuma waraka ta samu, har
sauran qabilu sun koma garuruwansu duk da haka
waxansu sun qi komawa sun yi zaman su anan
Kano. Don haka sababbin garuruwa suka fara
yaxuwa a Kano. Waqar Bagauda ta nuna wasu
daga ciki garuruwan nan na farko kamar su:

No   Sunaye   Inda suke a yanzu
1.  Lambu   Qaramar hukumar Tofa
2.  Kanwa   Qaramar hukumar Madobi
3.  Kwankwaso Qaramar hukumar Madobi
4.  Kura    Qaramar hukumar Kura
5.  Tamburawa Qaramar     hukumar
        Dawakin Kudu
6.  Yankatsari Qaramar     hukumar
        Warawa
7.  Mariri   Qaramar     hukumar
        Warawa
8.  Gunduwawa Qaramar     hukumar
        Warawa
            109
           …………….Daga Dutsen Dala

    Waxannan sababbin garuruwa da suka yi
yawa, suka yi gabas har sai da suka zo Sugungum
da Jarima a Gabas da Kano.
    Waxannan garuruwa ba suka cika nisa da
kogin Chalawa ba, inda ake tsammanin Yamalawa
sun koyawa mutanen gurin noman rani, kamar
yadda muka faxa a baya. To kaga wannan hali
abubuwa guda uku sun faru, na farko an sami
kafuwar ciniki da fatauci da hulxa da wasu qabilu
na nesa wato (External Trade) da dufulomasiya.
Na biyu sababbin garuruwan da ke kafuwa sun
kewaye qabilun Dala. Har ma sun yi yawa da tsari.
Abu na uku kuma shi ne suma qabilun nan na
Maxatai a wancan lokacin ba su da shugaba guda
xaya, bayan shugabansu Bagaudan farko ya rasu.
Amma suna da mutane guda huxu waxanda aka ce
sune shugabannin su, wato Gwale, da Yakasai, da
Guguwa, da Sheshe, to su ma sun gushe.
    To waxannan baqi da suka zo nan Kano
suka kawo sabon juyi na arziqi cikin qasa wataqila
su ne mutanen da suka yi qaura daga Maghrib
zuwa qasar Hausa, kuma suka haxu da Yamalawa
na Gaya, alama ce kuma ta cewa daga wani guri
suka zo, daga gabas maso arewa. Kafin nan da
wani lokaci „yan farautar nan da suka koma
manoma duk sun zama masu arziqi, saboda sayar
da abinci da suke yi. Nan da nan suka yi qarfi na           110
Kano Qwaryar Qira…...

bayi da dawaki don kuwa su ne manya-manyan
attajirai.
    Su waxannan mafarauta manoma su ake
kira Hausa kuma sun fi qabilun da suka samu a
nan qarfin jiki, kyakkyawar halitta da basira.
Kuma sun zo da qarfe wanda yafi tama daraja, don
haka suka fi mazauna nan gurin nagarta a wajen
noma da farauta har ma nagarta tasu tasa suka yi
abinci mai yawa, wanda qabilu na ko‟ina suka zo
don su saya. Sauran qabilun da suka zo suka sami
waxannan manoma to su ma sun zo da irin ta su
sana‟ar. Saboda haka sai guraran sana‟a irin su
Rini, da Saqa, da Jima, da Aikin Fata, da Xinki da
sauransu suka yawaita a ko‟ina, da haka kasuwa ta
tashi in da ake sai da hatsi kuma a sayi sabon
tufafi da sauran abubuwan qawatarwa. To ashe ka
ga Kano ko dama can da kasuwanci ta fara kafuwa
wadda noma ne ya kawo shi. Shi wannan juyi na
zuwan mafarautan nan da noman da suka yi har
yunwa ta afku a Afrika ta yamma ko kuma mu ce
Sudan ta Bahaushe ya kawo kafa sababbin
garuruwa da auratayya tsakanin qabilun da suka
zo da manoman nan, saboda haka rayuwar mutane
da aiyukansu na yau da kullum suka canza.
Garuruwan da aka fara kafawa a wannan lokacin
sun haxa da Gwale, da Yakasai, da Shehe, da
Kanwa, da Kwankwaso, da Tamburawa. Haka            111
           …………….Daga Dutsen Dala

kuma a kudu da wannan gurin aka kafa garuruwa
irin su Yankatsari da Mariri da Gunduwawa, kai
garuruwan manoman nan sun yi yawa har
Sugungum da Jarima. To wannan shi ne farkon
kafa kungiyar „yan jari hujja a qasar Kano wato
(Capitalism) wanda har yanzu shi ake yi a wajen
kasuwancin Kano.

ZUWAN SABON JUYIN JUYA HALI NA
ADDINI
    Kafin mu shiga labarin hukumar juyin juya
hali bari mu yi xan bayani akan nason addinin
musulunci a duk qasashen Afrika ta yamma, kafin
musulunci ya zo qasashen Hausa gaba xaya a
karve shi. Wannan xan bayani ya zama wajibi a yi
shi domin Malaman tarihin qasar Hausa ba su tava
ganin wata danganta ba tsakanin yaxuwar addinin
musulunci a qasashen Misira, da qasashen Magrib
balle su fahimci tasirin da nason yayi a qasashen
Hausa ba. Ka dai karanta a baya yadda addinin
Musulmi ya zo qasar Misra a zamanin Umar Bin
Khatab a hijirar Annabi Isa (A.S) ta 634 – 643
A.D, da kuma shauran qasashen da musulmi suka
ci na Kisra da Qaisariyya. To ba su tsaya a nan
kawai ba. A Hijirar Manzon Allah (S.A.W) ta 642
ne Sarkin Musulmi na wancan lokaci Ma‟awuya
bin Abi Sufyan ya aiki wani Sahabin Manzo           112
Kano Qwaryar Qira…...

(S.A.W) Uquba bin Nafi‟(4) zuwa Zuwailata
(Fizzan) ta qasar Libya domin yayi jihadi ya kafa
hukumar musulunci a duk qasashen Afrika ta
arewa, inda qabilun Barbar suke zaune. Uquba bin
Nafi‟ ya kafa cibiyar mulkin sa a Marzuq inda
gurin ya zama babban birinin Fizzan. Daga nan
Uquba ya ci gaba da yaqe – yaqe a qasashen Libya
har ya cinye Cyrenaica, da Triboli, da shauran
garuruwan da suke kewaye da su. Cikin waxannan
garuruwa ne larabawa „yan uwan Uquba suka yi
wo ambaliya suka shiga suka zauna suka yi
auratayya da mutanen gurin, suka mai da su
musulmi.
   Waxannan Larabawa sai suka ci gaba da
tahowa Afrika ta yamma, wasu domin cinikayya
da mutanen qasar Hausa inda aka samu sabon
juyin juya hali na arziqin qasa, wasu ko saboda
yaxa addini da Malanta. Shi kan sa Uquba bin
Nafi a cikin shirin sa na jihadi a Magrib, har ya
shirya zuwa qasar Borno domin ya yaxa addinin
musulunci a tsakanin qabilun Kanumbu da na
barebari a saboda haka ne ya xaura niyya, ya taho
Borno a hijra ta 666A.D. Ya yi tafiya mai nisa har
ya kawo Kuwar, wacce ba ta da nisa da Borno
amma rashin sani yasa mutanensa suka ba shi
shawarar ya koma domin suna ganin wataqila
Borno za ta yi nisa mai yawa daga Kuwar. Kash!            113
           …………….Daga Dutsen Dala

ina ma waxannan sahabbai na Manzon Allah
(S.A.W) sun qaraso Borno sun yaxa addinin
Musulunci? Da qasar Hausa ta sami Musulunci
daga sahabban Manzon Allah ba daga wajen „yan
kasuwa Wangarawa ba, na qabilar Buzaye ba
kamar yadda ya faru daga baya ba.
    Bayan komawar Uquba daga neman Borno
sai ya ci gaba da jihadin yaxa addinin Musulunci a
tsakanin qabilun Barbar har suka karvi addinin
Musulunci, suka zama mayaqansa. Ta haka ne har
ya ci Tunusiya a hijra ta 670. Da Uquba ya ci
qasar bai zauna a cibiyar mulkinta ta da ba, wanda
ta ke gavar kogin Rum, wato Tunisia, sai ya matsa
yamma da garin gefan Sahara ya kafa sabon
Birninsa wanda ya sawa suna Qairawan. Wannan
sabon Birnin kusa yake da tsohon garin
Cathaginiya, wanda Rumawa suka rushe bayan
sun kori Girkawa daga qasar. Gina garin Qairawan
da mai da shi cibiyar mulkin Sarkin yaqin Sarkin
Musulmi, Mu‟awiya Xan Abu Sufuyanu na
qasashen Maghrib a Afrika ta Arewa, General
Uquba bin Nafi‟ ya kawo shigar musulunci
qasashen Afrika ta hanya xoxar, wacce ta bi ta
tsakiyar Sahara zuwa Gao, da Tumbuktu, da
shauran qasashen baqar fata na Sudan ta arewa.
Kuma wannan shi ya jawo kafa daulolin
musulunci na Ghana da Mali da Songhai kuma ta           114
Kano Qwaryar Qira…...

wannan hanyar musulunci ya zo Kano a zamanin
sarki Ali Yaji.
    To guguwar wannan juyin juya hali na
shigowar addinin Musulunci waxannan qasashe da
suke maqwabtaka da qasar Hausa, ita ce ta taso ta
haxe da ta sabon juyin juya hali na arziqin qasar
Hausa da ya faru a lokaci xaya da na zuwan
musulunci waxannan qasashen. Kuma tasirin
waxannan abubuwa sune suka canja qasar Hausa,
suka kawowa shugabanninta sabon tunani akan
tarihinsu na asali. Da musulunci ya shigo daga
baya waxanda suka karve shi suka koyi rubutu da
karatu a cikinsa, sai suka qirqiri tatsuniyoyi
waxanda zasu danganta asalinsu da larabawa
domin jahilci da raina kai. To, wannan shi ya jawo
sarakunan Hausa suka ce su „ya‟yan Bayajida xan
sarkin Bagadaza ne, na Barebari suka ce su
„ya‟yan sarkin Yaman Saif Bin Zayyazan ne,
shugabannin jihadin Shehu Usmanu suka yi
da‟awarsu „ya‟yan Uquba Bin Nafi‟ ne.
Dukkaninsu sun manta da cewa su da Larabawa
asalinsu xaya. Domin Larabawa „yayan Samu ne,
Baqar fata kuma „yayan Hamu ne, da Samu da
Hamu kuwa „ya‟yan Annabi Nuhu ne, uwa xaya
uba xaya.(5)
    A cikin bayanin da za muyi na wannan
hukumar ta uku, za kaga tasirin shigowar addinin            115
           …………….Daga Dutsen Dala

Musulunci a cikin ayyukan sarakunan hukumar,
da ra‟ayoyinsu, da sunayensu, tun ma addinin bai
gama shigowa Kano ba, har lokacin da ya shigo
suka karveshi ya zama addininsu na gaskiya ba na
tsafi ba wanda suka gada. Wannan guguwa ta
shigowar Musulunci qasar Hausa ita ce ta ci gaba
har qarfinta ya haifar da jihadin Shehu Usmanu
Xan Fodiyo, wadda za ka ji bayaninsa a littafi na
biyu.

MATSALAR TSARO
    Ka dai riga ka karanta a baya cewa mutanen
da suke bautar Tsumburbura da Jakara basu da
sarki, sai dai shugaban gunkinsu; Barbushe, wanda
shi ne suke bi. To haka waxannan baqi da suka zo,
daga Gaya su ma ba su da sarki bayan rasuwar
Bagaudan farko, har sababbin garuruwan da suke
ginawa. To tun da haka ne kuwa menene
bambancin da ke tsakanin qabilun nan guda biyu,
wato masu bin Barbushe da manoma „yan farauta
da baqin su da suka zo don sayen abinci? Amsar
wannan tambaya ita ce mutanen Barbushe da
waxannan baqi zama guri guda ne kawai ya haxa
su, amma ba addini ko sarauta ba. Shi Barbushe da
mabiyansa suna zaune ne a gindin Dala. Su kuwa
waxannan mafarauta-manoma da baqinsu suna
zaune ne a wani guri da ake kira Maxatai, kudu da           116
Kano Qwaryar Qira…...

Dala, kuma ba nisa da gidan sarki na yanzu. Abin
da ya raba waxannan mutane da junansu shi ne
gulbin Jakara, don haka ba wani mai zuwa wajen
wani. Su qabilun Barbushe suna bautar gunkinsu,
su waxannan baqi suna noman su da cinikinsu ba
ruwan su da kowane gunki balle su bi Barbushe da
Tsumburbura. To amma duk da haka sai da
mutanen Dala da na Maxatan sai suka sami kansu
cikin haxari da rashin kwanciyar hankali. Abin da
ya kawo haka kuwa shi ne su sarakunan waxannan
gurare da muka ambata a baya inda waxannan
„yan farauta suka fito da farko, sai suka dinga
xauro yaqi suna zuwa suna kwashe arziqin
waxannan manoma da mutanen da suke ciniki da
su, suna mayar da su bayi don sun ga ba wani
sarki mai kare su. To su kuma da yake sun rigaya
sun kafu, sun zama al‟umma xaya, koda yake sun
zo daga garuruwa daban-daban da farko, sai suka
taru suka kai qara wajen Daurama Sarauniyar
Daura ta wancan lokaci, suka ce ta naxa musu
sarki don ya kare su daga zaluncin waxannan
sarakuna, musamman Sarkin Washa da na Timbi.
Da Sarauniyar Daura ta ji qarar waxannan mutane
sai ta naxa xanta guda, wani mai suna Dawuda, ta
ce ya je can ya zama sarkinsu. Wannan suna daga
baya ya zama Bagauda (Sarkin Kano daga Daura).
            117
           …………….Daga Dutsen Dala

    To wannan labari da ka ji na sabon juyin da
„yan farauta, manoma suka kawo Kano tun daga
zuwan su har naxa Bagauda Sarkin Kano na farko,
wataqila shi Barbushe ya hango, kuma ya faxakar
da mabiyansa cewa zai afku, kuma ba za su iya
hana afkuwarsa ba. Duk wannan abu da ka ji, mai
waqar Bagauda ya ambata shi a cikin waqarsa inda
ya raba juyin kashi biyu. Kashi na farko maganar
farauta, kashi na biyu kuma noma da ciniki da
sarauta.
           118
Kano Qwaryar Qira…...

        SASHI NA SHIDA
  HUKUMA TA UKU TA HIJIRA 999 A.D
       (SARKI DAWUDA)
   Hukumar Kano ta uku ita ce hukumar da
mutanen Daura suka kafa a Kano a dalilin neman
da Kanawa suka yi, har Daurama ta naxa Dawuda
ya zama Sarkin Kano na farko.(1) An ce hukumar
Kano ta uku ta fara ne farkon qarni na tara, 999
A.D. Kafin Dawuda da mutanen sa su zo Kano
daga Daura, ba a san ma‟anar kalmar “Sarki” ba a
lokacin, akan cewa mai qasa kenan. Saboda haka
sai Kanawa suka ci gaba da kiran sa da sunan
sarautar da suka saba da ita wato Bagauda, su
kuma mutanensa suna kiran sa Sarki. Abin da ya
kawo wannan ruxani shi ne rashin zaman Sarki
Dawuda a cibiyar mulki xaya a Kano, inda dukkan
qabilun Dala da na Maxatai za su san shi ne
shugabansu kuma su manta da sarautun su na da,
su karvi sunan Sarki a maimakon su. Wannan ruxu
kuma shi ne ya shiga cikin tarihin Kano har ake
cewa Sarkin Kano Dawuda xan Bawo jikan
Bayajidda shi ne Bagauda shugaban „yan farauta
da suka zo Kano daga Gaya. Jahilci da kasalar
bincike akan tarihin shi yake kawo irin waxannan
kurakure. Da ma lokacin da waxannan hukumomi
suke lokacin jahiliyya ne, babu karatu da rubutu
ko kaxan, balle a rubuta abubuwan da suke faruwa            119
           …………….Daga Dutsen Dala

a lokacin. Bayan addinin musulunci yayi qarfi,
ilimi ya samu sai Malamai suka mayar da kai
wajen koyarwa, da limanci, da alqalanci, suka bar
Tarihi, sai abin da aka ji daga bakin tsofaffi da
tatsuniyoyi su ake rubutawa ba tare da bincike don
a samu haqiqa ba.
    Game kuma da zamanin Sarkin Kano
Dawuda a Kano tarihi ya nuna cewa bai zauna
guri guda ya mulki Kano ba, kuma da yazo ya yi
yaqi da shugabannin Kanawa da ya tarar a garin.
Game da wannan ga abin da tarihin yace:
  “Bagauda ya zo tare da rundunarsa masu
  yawa sune farko daga cikin Sarakunan
  wannan gari, sunansa Dawuda, sunan
  uwarsa Qaunasa. Ya gina gida a Durani ya
  zauna a cikinsa shekara da shekaru sannan
  ya tashi ya tafi Burka ya gina birninsa
  wadda ake ambato Talautawa (wajen qofar
  xan Agundi da Gandun albasa) ya zauna
  shekara biyu. Sunan manyan kafirai da
  Bagauda ya samesu sune: Jankare, da
  Biju, da Bodari, da Ribau. Ya mallake su,
  ya yanka babbansu Jankare. Daga nan
  yayi qaura ya tafi Sheme (tsakanin Qunci
  da Kazaure).
           120
Kano Qwaryar Qira…...

YAQIN HAXA KAN QABILUN KANO
GURI GUDA
    Koda yake naxin Bagauda ya zama Sarkin
Kano na farko ya kawo kafa hukumar sarki ta
farko a Kano, duk da haka waxannan qabilu wato,
qabilar Maxatai ta manoma da tajirai da qabilar
masu bautar gumaka ta Dala ba su haxe sun zama
xaya ba. Kowace qabila ta ci gaba da zaman kanta
ba ruwanta da xayar. A game da qabilar Dala dai
ba wani littafi ko labarin baka da ya nuna cewa
Bagauda, a matsayinsa na sabon sarki, ya xauki
wani mataki don ya hana musu bautar gunkin da
suke yi ko na shekara ko na yau da kullum, bayan
kuwa shi da mabiyansa ba wanda ya yarda da
bautar gunki, koda yake ba a san irin addinin da
suke bi ba.
    Haka kuma Bagauda bai zo da dabarar saka
haraji a kan waxannan qabilu ba har da yawan
arziqin da yake qaruwa, yau da kullum, saboda
ciniki da qara gina sababbin garuruwa da ake yi.
Shi dai haraji shi ne yake kafa dangantaka ta
siyasar mulki tsakanin sarki da talakawansa
saboda su san wanda suke bi, don ya tsare musu
qasa tasu daga hare-haren zalunci, na wasu
mayaqa, da „yan ta‟adda. Daga qarshe ma dai
Bagauda bai zauna guri guda ya yi mulkin Kano
ba, a‟a sai ya yi nan ya yi can har daga qarshe ya            121
           …………….Daga Dutsen Dala

yi zamansa a Sheme, wadda ba ta da nisa daga
inda uwarsa, Sarauniya Daurama take mulki.
Wannan hali ya nuna Bagauda bai damu da
mulkin Kano ba qwarai a wancan lokacin. Amma
duk da wannan, tsoronsa ya hana hare-haren da
ake yi wa mutanen Kano kafin ya zo, don haka
zaman lafiya ya samu.
   To wannan hali na rashin zaman Bagauda a
Kano shi ne „ya‟yansa da jikokinsa suka tashi
haiqan don su canja, su kafa mulki mai qarfi a kan
duk qabilun da suke zaune a Kano da wasu
maqwabtanta, na kusa da na nesa, amma a sannu-
sannu ba lokaci xaya ba, kuma ta hanyar rarrashi
da fari, in abin ya qi a yi da qarfi, wato a ci
qabilun da yaqi.

SARAUTAR BAGAUDA
   Da Bagauda ya zama sarki ba abin da ya sa
a gabansa sai tsaron qasa da faxaxa iyakar Kano ta
arewa. Saboda wannan ne Bagauda bai zauna guri
guda ya kafa cibiyar mulkinsa ba. Ya fara zama a
Durami daga nan sai Talautawa, daga qarshe ya
zauna lokaci mai tsawo a Gazarzawa, wataqila a
tuddan nan na Kalebawa inda ya sami mabiya
Tsumburbura irin su Jankare da Biju da Bodari da
Ribau duk ya yanka su. Wannan aiki ya firgita
sauran mabiya Tsumburbura, kuma da masu zuwa           122
Kano Qwaryar Qira…...

hari wannan gari. Bayan Bagauda ya yi nasara
wajen tsaron gida kuma ya ga babu wata fitina
daga ma‟abota wannan guri sai ya tashi daga
Gazarzawa ya koma Sheme wato Kazaure ke nan.
   Da zuwansa Sheme Bagauda ya sami
manyan garin masu bautar gunki irin su Gubusani
da Bauni da Gazawuri da Xangefe da Fasataro da
Baqin-bunu, ya mallaki duk waxannan shugabanni
da iyalinsu ko ta hanyar faxa, ko kuwa ta lumana.
Zaman Bagauda a Sheme ya kusanta shi da Daura
inda Uwatasa take sarauta, kuma ta yiwu bayin
sarauniyar Daura suna zuwa wajen Bagauda suna
taimakonsa tsaron qasa. Gama tun da aka naxa shi
Sarki ba a sake samun vullowar wani azzalumi ba
wanda yazo ya kama Kano da yaqi. To amma duk
da wannan nasara da Bagauda ya samu ta tsaron
gari, ya yi nisa da mutanen Dala saboda haka
mulkinsa a kudu ba shi da qarfi sosai. Wannan
kuwa wani givi ne babba a cikin mulkin Kano
wanda dole ne a cike shi in dai ana son a mallaki
qasar baki xaya.

MUTUWAR BAGAUDA
   Da Bagauda ya rasu sai xansa, Warisi
(1063-1095), ya gaje shi. Lokacin da Bagauda ya
zo Kano ya zama Sarki a wancan lokacin jama‟ar
Kano suna matuqar neman wani Sarki da zai kare            123
           …………….Daga Dutsen Dala

su daga hare-haren zalunci da ake yi musu. Amma
a lokacin da ya rasu tuni jama‟ar Kano sun yi
yawa, garuruwa sun daxu, qasa ta qasaita. Saboda
haka akwai buqatar haxa kan jama‟a guri xaya don
su zama al‟umma xaya a qarqashin sarki xaya,
wanda zai ba da amru da nahayu, wato hani da
horo, wanda Bagauda bai iya yi ba, saboda wani
dalili nasa na kansa. A saboda wannan ne bayan
Warisi ya hau gadon ubansa, ya zama Sarkin Kano
na biyu, sai jama‟ar Kano suka aika wakilansu
wajen sa suna roqonsa da ya taso daga inda
ubansa yake zaune, wato Sheme, ya dawo
Gazarzawa don ya zama shugaban kowa da kowa
da za a dinga gani yau da kullum, amma Warisi ya
qi karvar wannan shawara, ya ce shi ba zai iya ba
domin shi tsoho ne tukuf-tukuf.
    Haka mutanen birni suka zauna Sarkinsu
yana nesa da su har sai da Warisi ya mutu xansa,
Gijimasu xan Warisi (1095-1134) ya hau gadon
sarauta kuma ya karvi shawarar manyan Kanawa
ya taso daga Sheme ya dawo Gazarzawa, inda ya
kafa kujerar mulkinsa a gindin Dala. Wannan aiki
da Sarki Gijimasu ya yi ya kawo matuqar damuwa
ga shugabannin masu bin addinin qabilar Dala. A
saboda wannan damuwa ce ma shugaban gunkin
Jakara, Mazauda, na wancan lokacin ya kirawo
taron gaggawa na na‟ibansa don su tattauna           124
Kano Qwaryar Qira…...

wannan matsala mai haxari, a wajensu. Da na‟iban
nan nasa suka hallara a wajen wannan taro sai ya
kada baki ya ce da su:

    “Wannan sarki zuwan da ya yi nan ya
    zo ne don ya rushe gumakanmu da
    duk guraren da muke bautar Jakara a
    gurin. Sai wani daga cikin waxannan
    na‟iban nasa ya ba shi amsa inda ya ce
    da shi, ai wannan Sarki ba shi da ikon
    da zai iya rushe gumakanmu a yanzun
    nan lokacin rayuwarmu. Amma ya iya
    rushewa a lokacin „ya‟yanmu ko
    jikokinmu”.

    Ko da yake Sarki Gijimasu ya ji abin da su
Mazauda da na‟ibansa suka faxa game da shi duk
da haka bai yi niyyar ya faxa su da yaqi ba, kamar
yadda kakansa Bagauda ya faxa su Jankare da
yaqi. A maimakon haka sai sarkin ya rarrashe su ta
hanyar diflomasiyya ko hulxar siyasar mulki ya ce
da qabilar Dala su zo su bi shi don a sami kafuwar
al‟umma xaya a qarqashin jagorancinsa na cewa
shi ne Sarkin duk sauran qabilu. Wannan shawara
ta sarki ta qayatar da Mazauda shugaban addinin
Jakara. Da ya yi sha‟awar ya tabbatar da gaskiyar
sarki bisa ga wannan shawara sai Mazauda ya ce            125
            …………….Daga Dutsen Dala

wannan sarki mutumin kirki ne bari in bai wa
xansa „yata don su yi aure. Wannan shawara ba ta
yi wa na‟iban Mazauda daxi ba, saboda haka suka
hana wannan abu na dangantaka tsakanin qabilar
Dala da Sarki Gijimasu ta afku. Suka ce idan aka
yi auratayya da mutanen sarki su za su zama ba
komai ba a nan gaba, saboda haka gara su ci gaba
da bautar gumakansu.
    Wannan kyakkyawar shawara ta Mazauda
da ta tabbata da qabilar Dala sun kuvuta daga duk
wata cuta ko zalunci wanda sarakunan da suka
biyo bayan Gijimasu za su nemi su yi musu. Kuma
qin bin wannan shawara ita ce ta jinkirta shirin da
Gijimasu ya yi na haxe jama‟ar Kano qarqashin
mulki guda ta hanyar rarrashi da lumana, tsakanin
qabilun da suke maqiyan juna a wancan lokaci.
Amma duk da haka Sarki Gijimasu bai yi fushi da
su ba, maimakon haka ma sai ya roqe su da su tara
duk mabiyansu don a gina ganuwa a birnin Kano
don tsaron jama‟a daga harin maqiya da miyagun
dabbobin daji. Wannan sabuwar dabara ta tsaron
gari ba a tava sanin ta a Kano ba sai da Sarkin
Kano Gijimasu ya zo da ita, amma mutanen Dala
suka karvi wannan gayyata ta Sarki cikin murna
da nishaxi suka zo da mabiyansu masu yawa suka
yi aikin gayya har ya nuna wa jama‟ar Dala
karimci inda littafin tarihin Kano ya ce ranar da            126
Kano Qwaryar Qira…...

aka fara wannan aiki Sarki ya ba da shanu masu
yawa da abinci da sauran kayan liyafa. Wannan
hanyar sulhu tsakanin Sarki da mabiya Barbushe
ita sauran sarakunan suka ci gaba da ita har sai a
zamanin Sarki Tsamiya xan Shekarau (1307-
1343), sannan abin ya zama yaqi da gaba, har aka
rushe Tsumburbura kowa ya huta.

SARAUTAR WARISI (1063-1095)(2)
   Da Bagauda ya mutu ka dai ji xansa Warisi
shi aka naxa Sarkin Kano, to amma ya tsufa a
lokacin. Don haka da mutanensa suka ba shi
shawara cewa ya taho kusa da gunkin
Tsumburbura don ya mallake su, ya fara cike givin
mulkin da Bagauda ya bari sai ya qi, ya ce ai shi
tsoho ne tukuf-tukuf don haka ba zai iya ba,
saboda wannan rauni nasa sai Kanawa suka fara yi
masa ba‟a suna kiran sa “Sarki Gwamma jiya”
daga nan aka samu kalmar Gwammaja, wadda a
yanzu unguwa ce a cikin birnin Kano. Akwai ma
wani karin magana a Kano wanda ake cewa
“Gwammaja ma Sarki ne a Kano”.

SARAUTAR GIJI-MASU (1095-1134)(3)
   Da Giji-masu ya yi Sarki sai ya karvi
shawarar mabiyansa, ya taso daga inda suke da ya
zauna a Gazarzawa, inda ya kusanci gunkin            127
           …………….Daga Dutsen Dala

Tsumburbura. A nan ne Giji-masu ya qulla sulhu
da shugabannin gunkin kuma ya yi ta yi musu
alheri da karamci har suka bi shi, suka yarda da
shi cewa Sarki ne managarci. Saboda karamcin da
Giji-masu yake yi wa waxannan mutane har sai da
babbansu Mazauda ya yi shawara ya bai xan Sarki
Giji-masu „yarsa, su yi aure don a sami zuriya
xaya, amma Wazirin Mazauda, wato Bugazau ya
hana ya ce idan aka yi auratayya tsakaninsu da
Hausawa za a haxiye su a manta da qabilarsu.
    Ban da karamci da kula da jama‟a wanda
Giji-masu ya yi ya rinjayi masu bin Tsumburbura,
Sarkin ya yi qoqari wajen faxaxa mulkinsa zuwa
ko ina a nahiyoyin nan huxu. Saboda haka ne
Sarkin ya ba wa Sarkin Rano mulkin wasu
garuruwa irin su Gano da Dabu da kuma Dabi. To
ka ga a nan Sarki ya fara bai wa „ya‟yan Sarki
garuruwa don su taimake shi mulkin qasa. An
kuma ce Giji-masu shi ne ya fara gina qofofi a
Kano, waxanda aka fara tun daga rariya ko kusa
da qofar Na‟isa har zuwa qofar Mazugal. Kuma
duk wannan aiki da aka yi an yi shi ne da
taimakon mabiya Tsumburbura waxanda suka fito
su da dukkan mabiyansu don su bi umarnin Sarki
saboda kirkinsa da yarda da suka yi da mulkinsa.
           128
Kano Qwaryar Qira…...

SARAUTAR XARIKI (1136-1194)(4)
    Malaman tarihin Kano sun haxu a kan cewa
Sarkin Kano Xariki, shi ne Sarkin da ya kafa
birnin Kano, kuma ya riqe ta cibiyar mulkinsa.
Haka kuma aka ce shi ne farkon Sarki da ya xauki
matakin haxe duk nahiyoyin Kano, qarqashin
mulki guda ta hanyar yaqi. Ya xaura yaqi, ya fita
daga cikin birnin Kano ya je Qaraye ya cinye ta,
wato a nan ya yi iyaka da qasar Zariya ke nan.
Haka kuma ya cinye garuruwa irin su Gwarmai da
Farin-ruwa. Wato a taqaice dai Sarki Xariki shi ne
ya fara faxaxa mulkin Kano har zuwa iyakokin
Katsina da ta Zariya , kamar yadda Bagauda ya
faxaxa ta zuwa arewa. Farkon sa wa talakawa
haraji a Kano a lokacin da Xariki ya faxaxa iyakar
Kano zuwa Qaraye da Farin-ruwa an ce ya karvi
kuxin haraji a guraren da ya yaqa, amma wataqila
Sarkin bai mayar da abin al‟ada ba. Dalili kuwa
shi ne sai a lokacin Sarki Naguji (1194-1247) aka
sa wa dukkan talakawan Kano haraji. Ya fita yaqi
a gabas don ya faxaxa Kano, ya zauna a can lokaci
mai tsawo. Ya fara yaqi tun daga Kura har ya kai
Tsangaya, amma Santolo ce kawai bai iya cin ta
ba, sauran garuruwa irin su Panda da Takai duk
sun bi shi, kuma saboda daxewar da ya yi a waje
sai masu bin Tsumburbura suka nemi su yi masa
tawaye. Don haka da ya koma sai ya kama            129
           …………….Daga Dutsen Dala

manyansu, irin su Shamagi xan Mazauda da
Doriyi xan Bugazau da sauransu ya yanka su.
Sauran mabiya Tsumburbura suka tuba saboda
firgita da abin da Sarki ya yi wa manyansu. To
saboda wannan tawaye ne Sarki ya xora wa duk
mai bin gunki harajin tumuni na duk abin da ya
noma a gona tasa, kuma wannan shi ne ya faru ga
dukkan talakawan Kano har abin ya zama harajin
Sarki da mai unguwa (Ba a daina biyan wannan
haraji ba, sai da P.R.P. ta kafa mulki a Kano a
cikin 1980 A.D).

QARSHEN TSUMBURBURA DA
GUMAKAN SANTOLO
    Jihadin da aka fara tsakanin sarakunan Have
da mabiya Tsumburbura da gunkin Santolo tun
zamanin Bagauda, ya xauki lokaci mai tsawo.
Dalilin tsawon wannan jihadin shi ne sarakunan
Have koda yake ba sa bautar gunki amma da
alamar suna tsoron kai wa gunkin Tsumburbura
farmaki don kuwa ba su san sirrinta ba, don haka
suke tsoron abin da wataqila zai faru a kansu idan
suka yi mata farmaki. Su kuma mabiya
Tsumburbura sun lura da cewa sarakunan Have
sun fi son su san asirin Tsumburbura, kafin su yi
mata wani abu don haka suka qi gaya musu
asirinta. Domin kuwa idan har sarakunan suka san           130
Kano Qwaryar Qira…...

asirinta, to su mabiyanta kuwa tasu ta qare.
Hankalin da mabiya Tsumburbura suka samu a
cikin wannan kai-kawo tsakaninsu da sarakunan
Have shi ne su kwantar da hankalinsu, kada su yi
tawaye. Dama sun yi a zamanin Naguji xan Xariki
abin bai musu kyau ba. To don haka suke lallashin
sarakuna, suna ba su dukiya don su qyale su su ci
gaba da bautar gunkinsu. To amma kuma idan har
za su rabu biyu masu bin tsarin sarauta da masu
bin tsarin gunki, kowa yana nasa mulkin a cikin
mutanensa abin ba zai yi kyau ba. Wannan zama
na sulhu da yaudara ya kai har zamanin Sarki
Guguwa (1247-1290) da Shekarau (1290-1307)
amma a zamanin Sarkin Kano Umaru Tsamiya sai
tufka ta yi hanci, kuma qarshe abin ya zo.

SARAUTAR UMARU TSAMIYA
(1307-1343)(5)
   Da Umaru Tsamiya ya zama Sarkin Kano
sai ya tara duk mabiya Tsumburbura ya yi musu
magana. Ya ce ya kamata su sani cewa soyayya
ana gadon ta, qiyayya ma ana gadon ta. Saboda
haka babu wata yaudara tsakaninsa da su gama
mai yaudara matsoraci ne. Ya ci gaba da cewa ba
wani abu a tsakaninsu da shi, sai gaba da takobi da
mashi. Wannan huxuba ta Sarki Tsamiya ta firgita
mabiya Tsumburbura. Don haka sai duk suka taru            131
           …………….Daga Dutsen Dala

manyansu da qanana, birni da qauye suka yi
shawara su bai wa Sarki Tsamiya dukiya mai
yawa don su fanshi kansu amma sarki ya qi karvar
duk abin da suka ba shi na dukiya. Bayan wannan
Sarki ya sa musu ranar da zai zo ya yaqe su, ya
fashe gunkin nasu, ya tona masu asiri don a san ko
menene a ciki.
    Mutum ba zai gane qarfin mabiya
Tsumburbura ba da haxarin barinsu su ci gaba da
wannan tsari nasu ba sai ya ji yadda tarihin Kano
ya bayyana yadda suka yi yaqi tsakaninsu da Sarki
Tsamiya. Ga kuma yadda aka yi yaqin, bayan
Sarki Tsamiya ya sa masu ranar da zai zo ya yaqe
su. Littafin Tarihin Kano ya ce:
    “Sa‟adda suka ji faxar Sarki dukkansu
    suka taru a qarqashin gunkinsu daren
    Alhamis, birni da qauye jama‟a masu
    yawa, masu-kuru da gunduwa da
    tsantsima   dubu  da  arbamiyya,
    sarakunan baka arbamiyya da tsiraru,
    ba su gushe ba suna kewaye gunkin tun
    daga magariba har hudowar alfijir,
    yayin da alfijir ya hudo, Sarki ya fito
    daga xakinsa, ya tafi wurin gunkin a
    gabansa da mutum arba‟in kowane
    cikinsu yana riqe da garkuwar fatar
    giwa, yayin da ya kai gurin sai kafirai           132
Kano Qwaryar Qira…...

    suka hana shi ya shiga cikinsa, aka
    xaura yaqi”.
    To ka ji yadda yaqi ya afku tsakanin
mutanen Sarki Tsamiya da masu bin gunkin
Tsumburbura. A cikin wannan yaqi ne mutanen
Sarki musamman Bajere suka yi nasara suka dinga
kisan abokan gaba tasu da mashi har sai da suka
sadu da ginin gunkin. Bajere ya shiga cikinsa, ya
sami wani mutum ya jingina da itaciyar gunkin da
kuma jar macijiya a hannunsa. Bajere ya soki
mutumin da mashi, mutumin ya zabura ya yi
kururuwa, hayaqi ya fito daga bakinsa ya gama
gari duka. Wanan mutum ya gudu har ya faxa
Qofar Ruwa. Sarki Tsamiya ya zauna tare da
runduna tasa ana neman wannan mutum a cikin
ruwa, amma ba a same shi ba. Da Sarki ya koma
gida sai wannan mutum ya fito ya gudu zuwa
ruwan Xankwai.
    To ka ji qarshen gunkin Tsumburbura da
mai dankonta. Bayan wannan Sarki ya komo
qarqashin itaciyar nan ta mai danko ya rushe
gininta, ya tattara dukkan abin da ke qarqashin
itaciyar na tsafi ya halaka su. Wannan aiki na
Sarki ya firgita dukkan manyan masu bautar
Tsumburbura har duk suka gudu suka bar birnin
Kano, Sarki ya mallaki dukkan qasa baki xaya.
Hangen nesan da Barbushe ya yi na qarewar            133
           …………….Daga Dutsen Dala

mulkin Tsumburbura da mallakar mabiyanta bai
tabbata ba, sai a zamanin Sarkin Kano Tsamiya
(1307-1343).

SARAUTAR ALI YAJI (1349 – 1385)(6)
    Qoqarin da jikokin Bagauda suke yi na haxe
Kano a qarqashin mulki guda da kuma halaka
gumaka da suke yi ya qarawa Kano farin jini da
shahara. Idan aka haxa wannan qoqari da abin da
Kano ta samu na arziqin noma da cinikin fatauci,
za‟a ga dalilin da yasa baqi daga ko‟ina suka ci
gaba da zuwa Kano. Cikin irin wannan baqi akwai
Malamai da suka zo lokacin Sarkin Kano Yaji,
(1349 – 1385).
    Irin waxannan Malamai suna zuwa Kano ne
daga Mali da kuma Maghrib. Wataqila abin da
yake kawo su daga Afrika ta yamma da Maghrib,
labarin da suka ji na Sarakunan Kano da qoqarin
da suke yi na hana bautar gumaka. Domin tun
kafin Bagauda yazo Kano har zuwa zamanin
Sarkin Kano Tsamiya xan Shekarau, wadda ya
rushe Tsumburbura. An yi fiye da shekara xari
biyar ana bautar gumki a Kano. Wannan rushe
gunkin Tsumburbura da shafe wuraren bautarta ya
kawo haxe qabilar Dala da ta Maxatai qarqashin
mulkin Sarki xaya, shi ne Sarkin Kano. Wannan
           134
Kano Qwaryar Qira…...

hali kuwa ya kawo zaman lafiya ya kuma share wa
musulunci hanyar karvuwa a duk qasar Kano.
    Wani abin lura cikin dangataka tsakanin
Afrika ta yamma da Maghrib shi ne maqwabtaka
da kusanci wanda ya maida Afrika ta yamma wani
vangare na Maghrib. A nan ana nufin duk abin da
ya tashi a Maghrib sai ya malalo har Afrika ta
yamma ya zo mana nan, musamman in abin ya sha
fi addinin musulunci da ciniki don su ne kafar mu
ta samun labarin musulunci a qasashen larabawa
da kuma samun mu‟amalar ciniki da sauran
qabilun duniya ta hanyar kogin Rum, a wancan
lokaci (wato Mediterrenean Sea).
    Daulolin tajdidi wanda suka taso har suka
yaxu a Maghrib suka haxe qasashen guri guda har
suka qara cinye Andalus (Spain), irin su Al-
Murabixun da Al-Muwahhidun duk sun yi tasiri
wajen kafa daular Musulunci a Mali inda Sarkin
Mali Kankan Musa ya zama Amirul Mu‟minuna.
Bayan waxannan dauloli sun kafu har sun yaxa
Musulunci a Afrika ta Yamma sai malamai daga
cikinsu suka yiwo yamma suna ciniki suna bada
ilimin addinin Musulunci har suka zo mana Kano,
a qarqashin jagorancin shugabansu mai suna
Malam Abdulrahman Zaghaiti, su kuma an ce sun
zo ne daga wani gari daga Mali mai suna
            135
            …………….Daga Dutsen Dala

Wangara, shi ya sa da suka zo nan aka riqa kiran
su Wangarawa, wato mutanen Wangara.
    Har yanzu ba a sami littafin da yayi bayanin
zuwan Wangarawa Kano dai dai da littafin
Muhammadu Al-Hajj ba. Wannan littafi mai suna
Warqa Maktuba fiha Asl-al-Wangariyin al
Muntasibin Lil- Sheikh Muhammad b.Muhammad
b. Ibrahim b. Muhammad Qithima, Muhammad
Alhajj ne ya fassara shi daga Larabci zuwa
Ingilishi. Wannan littafi yana cewa waxannan
Wangarawa da suka zo a qarqashin jagorancin
Zaghaiti sun shigo cikin birni ta qofar Kabuga ne,
inda suka yi zangon qarshe kafin su qarasa fadar
Sarki cikin birni. Zuwan waxannan Malamai a
cikin shekara ta 1380, ba wani abu sabo yake
nunawa ba illa cigaba da zuwan masu hijira Kano
da zama tun lokacin kafata kamar yadda tarihi ya
tabbatar.
    Bayan waxannan Malamai sun shigo gari
daga inda suka yi zangon qarshe a Kabuga sai
suka isa gidan Sarki inda suka zauna a wani sarari
na qofar gidan tare da iyalinsu suna sauraron a yi
musu iso wajen Sarki Yaji, don suyi masa bayanin
abin da ya ke tafe da su. Suna cikin wannan zaman
ne La‟asar ta yi musu, suka yi Alwala suka fara
Sallah. Ashe abin nan da suke yi na sallar jam‟i
baqon abu ne a wajen yaran gari, saboda haka yara            136
Kano Qwaryar Qira…...

suka tada hayaniya da sowa sai a zo a ga wasu
mutane suna sunkuyawa suna sansanar qasa,
kamar yadda mai yin Sallah yake nunawa.
Wannan sowa ita ce ta jawo hankalin Sarki har ya
leqa ya ga waxannan Malamai da abin da suke yi
na Sallah. Sai Sarki ya yi sha‟awar wannan tsari
na Sallah, musamman da yaga matsayin limami da
na mabiyansa. Saboda wannan ne Sarki Yaji ya
kirawo Malaman ya musulunta a hannunsu.
    Bayan Sarki ya musulunta a hannun
waxannan Malamai sai suka umarce shi da ya gina
Masallaci saboda sallar yau da kullum da kuma
Sallar Juma‟a. A saboda haka Sarki Ali Yaji ya
gina Masallacin Juma‟a na farko a Kano, a
unguwar Juma ta cikin birni.
    Daga nan Malamai suka bawa kansu
ayyukan yaxa Musulunci. Babbansu Abdurrahman
Zaghaiti ya zama Alqalin Sarki. Gurdurmasu ya
zama limaminsa, kuma Lawan Ladani. Sauran
Malamai kuma Sarki ya rabasu unguwa-unguwa
irin su Mandawari da Jujin „Yan Labu da Maxatai
da sauransu, inda kowannensu ya kafa Makaranta
don koya addinin Musulunci.
    Waxannan makarantu su ne suka zama
rassan Jami‟ar farko a Kano wadda cibiyarta ta ke
Unguwar Madabo, inda ya zama cibiyar koyan
ilimin Shari‟a a Sudan ta yamma. Bayan haka ne            137
          …………….Daga Dutsen Dala

Ali Yaji ya yaqi Santolo da taimakon Malaman
Wangarawa ya ci garin ya rushe Gumakansu.
          138
Kano Qwaryar Qira…...

    SASHI NA BAKWAI
   ZAMANIN BUNQASAR KANO
     DA SHAHARARTA:
  MUHAMMADU RUMFA (1463-1499)

    Da alama a zamanin Sarkin Kano Abdullahi
Barja (1438-1452) ne yaqe-yaqen da aka yi saboda
haxe qabilun Kano guri guda suka qare. Qarshen
waxannan yaqe-yaqe ya kawo shigowar garuruwa
irin su Dutse da Miga cikin mulkin Kano. Daga
kudu kuma Galadiman Kano Dawuda ya faxaxa
iyakar Kano ya kafa garuruwa waxanda aka sawa
suna Indabo.
    Waxannan abubuwa sun buxe wa Kano
hanyar qulla hulxa ta diflomasiyya tsakanin ta da
Borno, inda Sarkin Kano ya yi caffa ya kuma riqa
kai gaisuwa. Wannan kuma shi ya kawo Barebari
masu hijira Kano, malamai da „yan kasuwa.
    Da cinikin Gwanja ya iso Kano a wancan
lokaci sai hanyar kasuwanci ta buxe tun daga
Borno har zuwa Gwanja da Dagwamba, kuma
Kano ta zama ita ce cibiyar cinikin waxannan
gurare.
    A zamanin Sarkin Kano Yakubu xan
Abdullahi Barja (1452-1463), fannonin ilimi iri
biyu suka zo wa Kano. Waxannan fannoni biyu su
ne ilimin Alqur‟ani wanda Barebari suka zo da shi            139
           …………….Daga Dutsen Dala

tun zamanin Abdullahi Barja da ilimin Lugga da
Tauhidi wanda Fulani suka zo da shi daga Mali.
Samun waxannan sababbin fannoni na ilimi sun
qara fannin ilimin da ake da shi a da wato, ilimin
Fiqihu da Hadisi waxanda ake yi bayan an yi
karatun Alqur‟ani. Kuma a wancan lokaci ne aka
fara ba wa baqi daga Borno sarautar qauye,
wataqila don su kafa makarantun Alqur‟ani a
waxannan qauyuka don samun hasken addinin
Musulunci

SABON JUYIN RAYUWAR KANAWA
A ZAMANIN MUHAMMADU RUMFA(1)
    Idan an lura da duk abubuwan da muka faxa
a sama na zaman lafiya da buxe hanyar kasuwanci
da qarin zuwan malamai Kano, waxanda suka afku
a zamanin Abdullahi Barja da xansa Yakubu, za a
ga cewa wata shimfixa ce ta juyin rayuwar
Kanawa aka yi wa sarakunan da za su zo don su yi
amfani da ita wajen cigaban Kano na arziqi da
ilimi. Kano ta yi sa‟a da Muhammadu Rumfa
(1463-1499) ya zama Sarkin Kano bayan mutuwar
waxannan sarakuna guda biyu, kuma ya yi amfani
da wannan shimfixa iyakacin qoqarinsa ya yi wa
Kano ayyuka na alheri waxanda ba wani sarki da
ya tava yi mata, tun farkon ta, wataqila har
qarshen ta.           140
Kano Qwaryar Qira…...

    Idan muka duba shekarun da waxannan
sarakuna biyu suka yi za mu ga shekarun da suka
yi suna mulki a Kano shekaru ishirin da biyar ne
(25), kuma sun yi waxannan shekaru ne akan idon
Muhammadu Rumfa, sannan yana xan sarki jikan
sarki. Kuma ya yi karatu ya sadu da malamai da
„yan kasuwar wancan lokaci, ya yi cuxanya da su
ya san komai na wancan zamani. Ya san abin da
zai gyara ya kuma san waxanda zai nema don a yi
gyaran tare da su idan ya zama sarki. Ban da
wannan kuma akwai labarin baka, wanda har
yanzu ba a tabbatar ba, na cewa Muhammadu
Rumfa yana xan sarki, ya yi tafiye-tafiye masu
yawa cikin qasashen Afirka da wajen ta. Saboda
haka yake da cikakkiyar masaniya a kan
abubuwan da suke tafiya a wancan vangare na
duniya.
    Akwai kuma jita-jitar cewa Sarkin Kano
Abdullahi Barja shi ne Sarkin Kano na farko da
yaje aikin hajji, wataqila tare da Muhammadu
Rumfa.

ZUWAN SHEHU MAGHILI DA
RUBUTACCEN TSARIN MULKIN KANO
NA FARKO(2)
   A zamanin Muhammadu Rumfa Kano ta
karvi baquncin wani Shehun Malami da ake kira            141
           …………….Daga Dutsen Dala

Al-Maghili, wanda ya taimaka wajen sauye-
sauyen da Muhammadu Rumfa yayi musamman
dangane da rubutaccen tsarin mulki a Kano. An
sami savanin ra‟ayi daga malaman tarihi na Kano
guda biyu a kan rawar da Shehu Maghili ya taka a
Kano wajen gyaran mulki da shari‟a, waxanda
Muhammadu Rumfa ya yi a lokacin mulkinsa.
Hassan Gwarzo(3) ya ce lokacin da Maghili ya zo
Kano ya tarar ana addinin Musulunci, to amma
babu al‟amudansa irin su shari‟a da limancin qasa
da tsarin mulkin Musulunci. Saboda haka Shehun
ya shawarci Sarki Rumfa da ya kafa waxannan
abubuwa a cikin gyaran mulkin qasa tasa. Wannan
ra‟ayi na Hassan Gwarzo idan aka karve shi, to ya
shafe duk abubuwan da malaman Wangarawa
suka kafa na shari‟a da limancin qasa da yaxa
ilimi tun zamanin Sarkin Kano Ali Yaji. Kuma ya
nuna Muhammadu Rumfa kamar ba shi ne ya fara
yin waxannan gyare-gyare ba. Wannan ra‟ayi na
Hassan Gwarzo bai sami karvuwa a wajen
Barkindo ba,(4) wanda ya ce ai kafin ma Shehu
Maghili ya iso Kano tuni Muhammadu Rumfa ya
kusan qare gyare-gyaren mulkinsa da sauran
ayyukan rayuwar jama‟arsa. Ya ci gaba da cewa
abin da Shehun ya yi kawai shi ne rubuta wa Sarki
Rumfa tsarin mulki wanda ya dace da abin da
yake cikin Alqur‟ani da sunnar Manzon Allah           142
Kano Qwaryar Qira…...

(S.A.W). Shehu Maghili ya rubuta littattafai guda
biyu waxanda suka qunshi tsarin mulkin Kano na
farko. Na xaya shi ne Taj-al-din fi ma Yajibu alal
Muluk da kuma Wasiyyat al-Maghili ila Abi
Abdullahi Muhammadu b. Yakub.
    Idan muka duba siffar Muhammadu Rumfa
wadda muka ce ya zauna da ubansa da kakansa
lokacin suna sarauta, kuma ya yi yawon duniya ya
san komai, za mu ga cewa Rumfa ba irin Sarkin da
zai zauna a mulki ba ne, sai abin da aka ce da shi
ya yi, sannan zai yi. Yana da nasa tsarin abin da
zai yi tun yana xan sarki, da ya zo kan karagar
ubansa ya fara abubuwan da ya yi niyyar yi na
gyare-gyare har Maghili ya zo ya taimaka masa,
amma ba shi ya tsara masa ba. Wannan shi ne abin
da Barkindo yake nufi, kuma shi ne ra‟ayin masu
bincike cikin tarihin Kano. Tarihin Kano ya
bayyana cewa Rumfa ya fito da abubuwa na juyin
zamani guda goma sha biyu a Kano,(5) amma ga
kaxan daga cikin su waxanda muka zava saboda
muhimmancinsu ga jama‟ar Kano baki xaya,
kuma har yanzu su ake yi ko ake koyi da su:
    1. Shi ne ya fara sa shari‟a ta zama abar
     karva ga qasar Kano inda ya naxa alqalin
     Kano kuma ya kafa masa majalisar
     shari‟a ta musamman a fadar sarki, inda
     masu qara za su dinga zuwa.            143
        …………….Daga Dutsen Dala

2. Shi ne ya fara naxa babban Limamin
  Kano saboda sallar Juma‟a da kuma ta
  yau da kullum. Wannan abu da Rumfa
  ya yi ya nuna cewa Kano ta zama qasar
  Musulunci tun wancan lokacin.
3. Shi ne ya kafa Majalisar qasa ta sarki
  wadda ake kira Tara-ta-Kano. Wannan
  majalisa ta qunshi manyan hakimai guda
  tara a cikin ta har da Babban Alqalin
  Kano (za a yi qarin bayani a kan wannan
  magana a gaba). Aikin wannan majalisa
  shi ne ta ba wa Sarki shawara akan aikin
  mulkin qasar Kano baki xayan ta, wanda
  Sarki da majalisarsa za su dinga yi yau
  da kullum, har da abubuwan da suka
  shafi yaqi da tsaron qasa da hulxa da
  qasashen waje. Wannan sabon juyi da
  Rumfa ya kawo ya canja matsayin
  Sarkin Kano na da, inda Sarki yake yin
  muxalaqin mulki, shi da bayinsa, babu
  wata majalisa da za ta ba shi shawara ko
  ta kwave shi in ya kauce hanya.
4. Saboda a banbance tsakanin sarakuna da
  talakawan qasa, sai Rumfa ya kawo
  tsarin sa manyan kaya da rawani da
  alkyabba don su zama su ne kayan
        144
Kano Qwaryar Qira…...

    sarauta (Royal Regalia) ga malaman fada
    na gargajiya.
   5. Rumfa shi ne ya fito da tsarin hakimai bi
    da bi wanda ake yi yanzu wajen
    gaisuwar sarkin Kano, kuma shi ne ya
    raba wa hakimai qauyuka cikin duk
    qasar Kano don su duba masa. Wannan
    shi ake kira da Turanci (divison of
    responsibility). Wato kowa a ba shi aikin
    da zai yi wa sarki don ya hutar da shi.
    Kalmar hakimi dai an samo ta ne daga
    harshen Larabci ma‟anarta shi ne mai
    hukunci da sulhu tsakanin talakawansa.
    An bai wa hakimai da dagatai wannan
    matsayi don su tabbatar da zaman lafiya
    a qasashensu, kuma su rage wa sarki da
    alqalai nauyi wajen ayyukansu na
    shari‟a. Wannan matsayi na hakimai shi
    Turawa suke kira (Justice of peace)
    wanda suke bai wa wasu shahararrun
    mutane a qasashensu. Ka ga ashe mu ma
    muna da irin wannan al‟ada a cikin tsarin
    mulkinmu na gargajiya tun zamanin
    Muhammadu Rumfa (1463-1499).
   6. Rumfa shi ne ya gina Kasuwar Kurmi
    domin ya yi wa hanyoyin cinikin Borno
    da na Gwanja tushe, kuma Kano ta zama            145
           …………….Daga Dutsen Dala

    mahaxar ciniki ta Afirka ta yamma.
    Wannan abu da Rumfa ya yi ya jawo wa
    Katsina asarar „yan kasuwa don haka ta
    faxa Kano da yaqi.
   7. Rumfa shi ya kawo kafa makarantun
    Alqur‟ani a ko ina a Kano birni da qauye
    saboda koya wa yara da manya karatu da
    rubutu, domin a canja musu alqibla daga
    rayuwar jahilci ya zuwa rayuwar ilimi da
    addinin Musulunci.
   8. Shi ne ya gina gidan sarki na yanzu
    wanda ake kira Gidan Rumfa, ya komo
    da masarautar Kano varin Maxatai aka
    bar varin Dala. Shi ne kuma ya kewaye
    birnin Kano da garu wanda aka fara yi
    tun zamanin Sarkin Kano Gijimasu, ya
    qarasa shi ya mayar da Birnin Kano
    cikakken birni.

YAXUWAR ILIMI A KANO
ZAMANIN RUMFA
   Ka dai rigaya ka karanta cewa addinin
musulunci yazo nan Kano a zamanin Sarki Kano
Ali Yaji (1349 – 1385), lokacin da malaman
wangarawa suka zo daga Malle. Ali Yaji shi ya
fara karvar addinin musulunci, kuma yasa
talakawansa duk suka bi, kuma su waxannan           146
Kano Qwaryar Qira…...

malamai sarki ya basu guraren zama inda zasu
bada karatu. Babbansu Abdurrahaman Zaite aka
bashi guri a Madabo inda ya sare bishiyar
tsumburbura ya gina masallaci a gurin, inda shi da
sauran malamai Wangarawa „yan uwansa suke yin
sallar jam‟i ako wacce rana. A haka Zaite ya kafa
makaranta a gidan sa don koya karatu da addinin
musulunci.
    Kamar yadda aka bawa Mallam zaite guri
ya yi gidansa da masallacinsa, hakama sauran
malaman aka basu gurare a cikin birni, irin su
Mandawari, Sheshe, Jujin „yanlabu, Maxatai da
sauransu, in da suka kafa makarantun koyar da
addini da karatun Alqu‟ani, ga „ya‟yan sarakuna
da talakawa. Abin da waxannan malamai na
wangarawa suka fi koyawa mutane shi ne ilimin
fikihu, da hadisai, wato al‟amuran sallah da na
shari‟a da kuma sunnar manzon Allah, bayan
karatun Alqur‟ani.
    A kuma zamanin sarkin Kano Yakubu
(1452-1463), Fulani suka zo qasar Hausa, suma
daga Malle kuma sun zo da ilimin Tauhidi da
lugga, wato ilimin harshen larabci da sarrafa shi,
har ila yau dai, a wancan zamani ne wasu malamai
daga Macina ta qasar Borno, suka zo Kano su uku.
Sarkin Kano ya naxa babbansu Algafati ya zama
Sarkin Gaya, don ya ci gaba da koya karatun            147
           …………….Daga Dutsen Dala

Alqu‟ani. Na biyunsu kuma ya tafi wajen Sarkin
Rano inda Sarkin Rano ya bashi guri don shi ma
ya koya karatu a can.
    Haka kuma a zamanin Sarkin Kano
Muhammadu Rumfa (1463 – 1499) Shaihu
Maghili, wani malami daga Tuwat ta Maroko yazo
tare da „yan uwansa malamai da yawa. Shehu
Maghili da „yan uwansa sun zo da littattafai da
yawa na koya addinin musulunci da shari‟a, kuma
a wancan lokaci malaman sun sami alfarma, da
girmamawa, saboda goyon baya da alheri da
sadakar da suke samu a wajen Sarkin Kano
Rumfa. Duk kuma sarki yayi musu haka ne don su
sami damar sakewa su koyawa jama‟a karatun
Alqu‟ani da addinin musulunci. Tun daga zamanin
Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ake bawa
Malamai gurare su zauna cikin birni da qauye don
su bawa jama‟a ilimi. Malamai irin su Shaihu Ba-
Tunishe da xan Gwauronduma, na bakin zuwo ta
cikin birnin Kano da Malam Abdussalami duk sun
zo Kano da littattafai iri daban-daban kuma an
basu guri sun zauna, sun ci gaba da bada ilimi.
    Wannan alheri da Kano take samu na zuwan
malamai su zauna a cikin ta ya faru ne a
sakamakon rauni da daulolin Malle, Songhai da
Borno suka yi, tun daga zuwan malaman
Wangarawa har vullowar jihadin Fulani. Gama su           148
Kano Qwaryar Qira…...

waxannan dauloli guda uku da na ambata su aka fi
sani da girmama malamai da basu sadaka, da
kyauta. Su ne suke bawa malamai alqalanci,
limanci da aikin ba da shawara akan mulki da
yaqi, kai hasalima dai Shaihu Maghili, babban
malamin Sarkin Songhai Muhammadu Askiya ne,
kuma da yazo nan Kano aikin da yayi wa sarkin
Kano Rumfa ke nan. Dan kuwa shi ne ya rubutawa
Rumfa littafin tsarin mulki na farko a Kano,
wannan littafi shi ne ya zama jagoran mulkin
musulunci a zamanin Muhammadu Rumfa har
zuwan Jihadi, sannan Shaihu Abdullahi na
Gwandu ya rubuta wa Sarkin kano Suleiman wani
tsarin mulkin wanda ake kira DIYA’U AL
HUKKAM.

TARBIYAR YARA A KANO
LOKACIN MUSULUNCI(6)
    Babban alheri da ribar da Kano ta samu
game da zuwan Malamai wannan gari, da kuma
xaukakar da suke samu daga Sarakunan Have shi
ne fito da hanyar koyawa yara karatun Alqur'ani
da addini a harshen Hausa. Da farko dai sai
Malamai suka qago yadda yara zasu koyi
Alqur'ani da sanin baqi ta hawa uku, wato, ta sanin
Babbaqu da fari, sannan Farfaru, sannan
Haddatu. Shi babbaku, sanin harrufan Alqur‟ani            149
            …………….Daga Dutsen Dala

ne a yadda suke ba tare da wasali ba. In har yaro
ya iya karanta harafin da yake cikin suratul Fatiha
wato "Alhamdu.." ba tare da wasali ba, to sai a ci
da shi gaba, a koya masa farfaru, wato a yiwa
harufan da ya sa ni wasali, da kuma yadda
wasalin yake sarrafa baqaqqe har su zama jumloli.
Bayan wannan kuma sai a shiga karatun surori
xaya bayan xaya da fatan sai an gama karatun duk
surorin Alqur‟ani. Wannan shi ake kira sauka.
Idan yara suka sauke Alqur'ani hizifi sittin, suka
san baqi sosai to sai a raba su biyu. Kashi na farko
waxanda suka nuna alamar haziqanci da murya a
wajen karatun Alqur'ani sai a kai su gabas, wato
Borno. Waxannan xalibai zasu koyi karatun
Alqur'ani da tajweed da hadda a hannun malaman
Alqur'ani irin waxanda ake bawa darajar tallake
(Ph. D.) a karatun turawa. Su irin waxannan
mahaddata na Borno. Ko dai sun samo karatunsu
ne daga jami' ar al- Azhar a Misra (Egypt) ko
kuma sun yi karatun nasu ne a wajen wasu
malamai da suka yi karatunsu a Misra.
    Bayan waxannan xalibai sun gama
karatunsu a Borno sun dawo gida sai a dinga,
kiransu "Barnawa" wato malamai da suka yi
karatunsu a Borno ke nan. Kuma sai a aika dasu
qauyuka da cikin birni domin su buxe makarantun
koyawa yara da manya karatun Alqur'ani.            150
Kano Qwaryar Qira…...

   Kashi na biyu kuma sune waxanda suka
nuna sha'awa tasu a wajen koyon ilimi bayan
saninsu na Alqur'ani. Su kuma sai a kai su wajen
malaman gari masu bada ilimi a zaure ko malaman
buzu waxanda suke zaune a unguwowi daban
daban a cikin gari masu bada ilimi a zauren su.
Malaman buzu, ko dai sun koyi karatunsu ne daga
jami‟ar Sankore ta garin Tambutu, ko kuma sun yi
karatunsu ne a wajen malaman da suka yi nasu
karatun a can Tambutu xin.
   Kamar yadda xaliban Borno suke qwarewa
a karatun Alqur'ani da tajweedi da hadda da
rubutawa, haka ma 'yan uwansu masu karatun
buzu suma suke qwarewa a koyon harshen larabci
da lugga tasa, ilimin addinin Musulunci, tarihi,
tauhidi, ilimin shari'a da sauran fannonin ilimi.
   Su ma irin waxannan xalibai na makarantar
buzu in sun gama sun sami iliminsu sai a dinga
kiransu "Tambutawa", domin a banbance da
fannin karatunsu. Su ma sai a aika da su, su
shimfixa nasu buzun domin koyawa jama'a cikin
birni da qauye ilimin addini da sallah domin
jama'a su san 'qabli' da 'ba'adi' wajen gyara sallah
tasu.
    A wannan lokaci na Rumfa ne Hausa ta
qara karvar yawa-yawan kalmomin larabci da suke
cikinta, kuma aka shirya nahawun Hausa a kan            151
           …………….Daga Dutsen Dala

layin nahawun larabci har harshen Hausa ya zama
rubutacce a harafin Ajami. Har ila yau dai a
wannan lokaci ne aka fito da karatun tafsirin
Alqur'ani a cikin watan azumi wato watan
Ramadan. Saboda yaxa addinin Musulunci a cikin
birane da qauyuka domin jama'ar musulmi su san
abin da Allah Maxaukakin Sarki yake faxa a cikin
Al-qur'ani mai tsarki. A wajen karatun tafsiri an
shirya cewa malamin Barnawa shi ne zai ja baqi,
kuma malamin Tambutawa ya fassarawa jama'a da
Hausa domin su gane abin da ake nufi da ma'ana
tasa.
    A zamanin Muhammadu Rumfa ne kuma
Kano ta kai qololi a shahararta ta wajen qaruwar
arziqi da ilimi a sakamakon buxewar hanyoyin
ciniki da qasashe. Abin takaicin shi ne bayan
Rumfa ya shuxe, sarakunan da suka biyo baya
basu ba da himma wajen cigaba da waxannan
ayyuka na alheri ba, sai kawai wasu daga cikinsu
suka koma gidan jiya, wajen tsafi da shirka. Suka
jefar da shari'a da bin kadin talakawa suka koma
zalunci da wulaqanta jama'a. Waxannan halaye su
suka jawo musu baqin jini daga wajen talakawan
qasa kuma suka kawo raunin mulkinsu. A nan
gaba kaxan zaka ga yadda barin hanyar Allah da
zalunce-zaluncen sarakunan Kano suka jawo
faxuwar mulkinsu da komawarsa hannun Fulani.           152
Kano Qwaryar Qira…...

    Waxannan abubuwa da muka faxa a sama
sune suka nuna cewa ilimin addinin musulunci da
malanta a Kano ba a fadar sarki kawai ake yi ba,
a'a addinin musulunci tuni ya zama hanyar
rayuwar mutane a Kano. Tun wancan zamanin ake
samun malamai a Kano masu yin rubuce-rubuce a
kan fannonin addinin musulunci domin shiryar da
jama'a hanyar gaskiya. Cikin irin waxannan
malamai akwai waliyai masu yawa irin su Wali
Mai Aduwa, Wali Mai Geza, Wali Mai Kargo,
Shehu Abdullahi Siqqa da sauransu. Wasu daga
cikin waxannan malamai kamar irin su
Muhammadu Zara wanda ya zama Wali mai
Kargo wa'azinsu na addinin musulunci yayi wa
sarakunan wancan lokaci tsauri ya jawo masa kisa
kamar yadda Chambalin ya faxa. A cikin littafin
sa mai suna TARQIQI MA QASA BI ZKIRI
AULIYA'A HAUSA, Mallam Adamu na Ma'aji, ya
lissafa waliyan Kano, da karamominsu, da
qaburburansu, waxanda har yanzu jama'a suna kai
ziyara domin girmamawa da neman albarka.

AMFANIN MALAMAI A CIKIN JAMA' A
   A farkon littafin nan mun ga yadda
Barbushe, limamin Tsumburbura, yake yiwa
mabiyansa limanci a ranakun haji da umra, wato
ranakun sallah babba da qarama. Haka kuma an            153
           …………….Daga Dutsen Dala

karanta yadda Mazauda, limamin Jakara, shi ma
yake yin nasa limancin a lokacin tsafinsu na yau
da kullum. In ban da duba na abin da zai faru a
gaba bamu san sauran ayyukan da waxancan
limamai suke yiwa mabiyansu ba. Amma ayyukan
da malaman addinin musulunci suke yi wa jama'ar
musulmi a kullum a bayyane suke, saboda haka
lissafa wasu daga cikinsu ba wuya.
    Duk wahalhalun da malaman Barnawa da
na Tambutawa suka yi kafin su sami karatunsu sun
sha su ne ba don kansu kawai ba, a' a sai don su
dawo su taimaiki jama'a baki xaya, musamman
jama'ar musulmi. In an yi la'akari da zamansu a
cikin jama'a, za aga ba don su ba da mutane basu
sami hasken musulunci ba. Kaxan daga cikin
ayyukan da suka yiwa musulumi na shiriya su ne:
   1. Tarbiyar yaran gari maza da mata wajen
    koya musu karatun Alqur'ani da sallah;
   2. Limanci da bada ilimi ga manya domin su
    zama malamai na gaba;
   3. Alqalanci da taimakon sarakunan qasa a
    majalinsu don bada shawara da ayyukan
    magatakarda da rabon gado;
   4. Xaura aure da raxa sunan 'ya'yan musulmi
    a bisa qa'idojin shari'a;
   5. Sallar jana' iza ga mamatan musulmi;
   6. Wa'azi ga jama'a a masallatai, kasuwanni


           154
Kano Qwaryar Qira…...

    da sauran guraren taruwar jama'a;
  7. Raya watan Ramadana (azumi), da tafsirin
    Alqur' ani, da hadisan Annabi domin
    sauran musulmi su san kalmomin ubangiji
    da sunnonin Manzon Allah da harshensu;
  8. Yin addu‟o‟i da roqon Allah a duk lokacin
    da wata musifa ta faxawa jama'a, ko kuma
    domin neman zaman lafiya, qaruwar arziqi
    da ije bala'i ga jama'ar musulmi baki xaya.

  Waxannan abubuwa haka suke a birni da
qauye, tun lokacin mulkin Have har zuwa yau.
Ban da waxannan abubuwa da muka ambata,
akwai kuma Malaman Tsibbu, da masu Duba da
malaman Taurari da na Hisabi. Da masu rubuta
magunguna na Layu, Guraye, da rubutun sha da yi
wa mutane quri'a don neman sa'a akan abubuwan
da mutane suke son yi.
            155
           …………….Daga Dutsen Dala

     SASHI NA TAKWAS
    LOKACIN RAUNIN KANO DA
    FAXUWAR MULKIN HAVE(1)

    Rumfa ya kafa harsashi mai qarfi na gina
Kano wanda da sarakunan da suka biyo bayansa,
masu niyya irin tasa ne, kawai zasu ci gaba da
ayyukansa. Domin a wancan lokaci tuni Kano ta
shahara akan zamowarta babbar qasa ta Musulunci
da arziqi. A kuma wancan lokaci ne qasashen
Turai suka fara samun labarin shaharar Kano akan
arziqi da musulunci, ta hannun shahararren
matafiyin nan mai suna Leo Africanus. Wannan
matafiyi ya ziyarci qasashen Hausa da Borno a
1513-1515, kuma ya zo Kano ne wacce ya kira
"Cano" a zamanin Sarkin Kano Muhammadu
Kisoki xan Abdullahi, jikan Muhammadu Rumfa,
(1509-1565). Ta rubutun Leo Africanus ne mai
suna History of Africa and The Memorable Things
Contained Therein, London (1600) Turawa suka
fara sanin labarin qasashen Afrika ta yamma, har
qasashen Hausa da Borno.
    Ayyukan da Rumfa ya yiwa Kano wanda ya
jawo mata arziqi da ilimin addinin musulunci
kuma sarakunan da suka biyo bayansa kamar guda
biyar suka ci gaba da qarawa, sun jawowa Kano
maqiya saboda kishi da hassada. Mussaman abin           156
Kano Qwaryar Qira…...

da Sarki Kano Abubakar Kado xan Rumfa yayi na
kawo qarin malamai daga Mali da kuma bunqasar
kasuwar Kurmi wacce ta zama babbar kasuwa a
qasashen Sudan ta yamma baki xaya. Tun farkon
kafa kasuwar Kurmi a zamanin Muhammadu
Rumfa, Katsina ta buxe qofofin yaqi da Kano a
kan don me Kano zata kafa kasuwar ciniki da
qasashen waje bayan a Katsina ne kawai irin
wannan kasuwar take. Fushin da Katsina ta yi
akan kasuwar Kurmi a Kano bai kai qoli ba sai a
zamanin Sarkin Kano Muhammadu Zaki (1582-
1618). A wancan lokaci ne Katsina ta dinga
kawowa Kano harin yaqi akai - akai har sai da
arziqin Kano ya tsaya cik, ya kasa tafiya. Fatake
da Malamai da Manoma da qananan „Yan kasuwa
duk suka guji guraren wannan tarzoma har yunwa
to afkawa Kano abin da ba'a tava yi ba a Kano tun
zamanin kafa ta har zamanin Muhammadu Zaki,
wacce aka yi shekara goma sha biyu ana yinta.
    Ana cikin wannan yunwa da masifar
Kastinawa sai ga Qwararrafawa sun dirkako Kano
da yaqi. Qwararrafa suka ci gaba da yaqar
qasashen Hausa. Waxannan masifu na yaqi da
yunwa su suka sa Kano tayi rauni matuqa da
gaske, al‟amura suka fara lalace ma ta. Da
wannnan musifa ta kai gaya sai Sarki ya tara
jama'ar Kanawa ya tambayesu shawara yadda za a            157
           …………….Daga Dutsen Dala

yi maganin musiffar yaqin Katsinawa. A wannan
taro ne wani malami mai suna Shehu Abubakar
Bayammi yayi wa Sarkin Kano alqawarin zai
taimakeshi ya rinjayi Katsinawa a yaqi, amma da
sharaxin in har yaci Katsina to kada ya dawo Kano
da zama ya koma wani gari. Da taimakon wannan
malami ne Sarki Kano Muhammadu Zaki ya xaura
yaqi ta tafi Kastina cikin watan azumi. Tarihin
Kano ya bayyana wannan yaqi kamar haka:
  "Sa'adda Sarki ya fita a cikin rana ta
  ishirin da biyu ga watan Ramadan, ya isa
  Katsina ranar idi bayan hudowar rana.
  Katsinawa suka fito suka taresu da
  garaya tun basu tafi idi ba, yaqi ya afku
  tsakaninsu.   Kanawa suka rinjayi
  Kastinawa matukar rinjaya, suka
  warwatsa su xai - xai, Kanawa suka
  ribato dawaki arbaminya da lifida sittin
  ba wanda ya san adadin abin da aka
  kashe da abin da aka kama daga cikin
  Katisnawa. Daga nan Sarkin Kano ya
  koma Qaraye ya mutu a cikinta.”
           158
Kano Qwaryar Qira…...

   Ko da yake wannan yaqi ba shi ne yaqi na
qarshe ba tsakanin Katsina da Kano, amma shi ne
ya fara karya lagon Katsina, kuma da aka naxa
Muhammadu Na Zaki xan Muhammadu Zaki sai
yaci gaba da qarfafa nasarar da ubansa yayi a
Katsina. Muhammadu na Zaki xan Zaki (1618-
1623), shi ne Sarkin da ya ya faxaxa birnin Kano,
ya qara girmansa, yaci gaba da yaqin Katsina yana
samun riba a kullum. Kuma Na Zaki shi ne
qarshen Sarakunan gidan Rumfa waxanda suka
dage akan tabbatar da abin da kakansu Rumfa yayi
wa Kano na alheri suka ma qara akai domin Kano
ta cigaba da qasaita. Amma a zamanin Muhamadu
Zaki ne aka fito da bautar "Dirki" wanda ya zama
gunkin kutumbawa.

LALACEWAR MULKIN HAVE A HANNUN
KUTUMBAWA(2)
    Bayan mutuwar Sarkin Kano Muhammadu
Na Zaki xan Zaki sarakunan da suka biyo bayansa
sai suka yi rashin sa'a har jama'a suka dinga ganin
ba abin da suka sa a gabansu, sai qoqarin rushe
kyawawan ayyukan da kakaninsu suka yi wa
Kano. Saboda sarakunan sun bar shari' a da adalci
ga jama'a, sun xau zalunci, da gariman kai da
al'adun shirka da tsafi, waxanda suka kaucewa
addinin musulunci. Wannan mummunar shaida da            159
           …………….Daga Dutsen Dala

tarihi yayi musu shi ya jawo musu suna
Kutumbawa, ma'ana tubabbu. An sa musu wannan
suna ne kawai domin a banbantasu da sauran
'ya'yan Bagauda, a haxasu da Maguzawa da
Warjawa ace „yan uwansu ne, amma su
Kutumbawa suka tuba suka shiga cikin mulkin
Kano, na kakansu.
    Kutumbawa sun fara mulkinsu ne a kan
Muhammadu Alwali Kutumbi xan Muhammadu
Nazaki (1623-1648). Sun fara mulki mai kyau da
bin qa'idojin musulunci da fari, domin a zamanin
Kutumbawa ne aka samu tabbacin Sarkin Kano
wanda ya fara zuwa Makka domin yin hajji in ka
xauke jita-jitar da aka faxa a baya ta zuwan
Abdullahi Barja. Wannan Sarki kuwa shi ne Sarki
Kano Alhaji xan Kutumbi (1648-1649). A
zamanin Kutumbi Kano ta fito daga rauninta har ta
fara yaqe-yaqe ba da maqwabtanta na kusa kawai
ba, a'a har ma da na nesa. Kutumbi ya faxaxa
iyakokin Kano gabas da yamma inda ya shigo da
garuruwa masu yawa suka dawo mallakar Kano.
Amma bayan rasuwarsa sai Kano ta koma kan
rauninta saboda raunin mafiya yawa daga
sarakunan da suka biyo bayansa. Ban da wannan
kuma an bayyana abubuwa masu yawa waxanda
suka kawo raunin Kano da faxuwar mulkin Have,
a zamanin mulkin Kutumbawa, amma uku daga           160
Kano Qwaryar Qira…...

ciki an fi ganin tasirinsu, kuma sune:

  1. Yaqe- yaqe na neman suna waxanda
   sarakunan Hausa bakwai da banza bakwai
   suka xorawa kansu saboda rashin
   tsawatarwa. Daulolin da suke hana irin
   waxannan yaqe-yaqe a qasar Hausa kamar
   su Malle, Songhai da Borno duk sun faxi a
   wancan lokacin don haka waxannan
   sarakuna suka shiga shargallensu domin
   hallaka talakawansu. Gama idan irin
   waxannan yaqe-yaqe sun tashi a qasa
   talakawa ake kashewa. Ba ma waxanda
   suka fi kowa yin asara a cikin irin
   waxannan yaqe-yaqe irin Fulani masu shanu
   waxanda dukiya tasu ta dabbobi a fili take
   babu kariya, sai a karkashesu a kore
   dabbobinsu sun zama ganimar yaqi.

  2. Zalunce-Zaluncen    da    sarakunan
   Kutumbawa suka fito da shi a Kano wajen
   sa Jangali ga Fulani, kuxin kasuwar Kurmi
   ga 'yan kasuwa, kuxin shuke-shuke ga
   manoma da kamun 'yan matan talakawa a
   mai da su kuyangi.
            161
            …………….Daga Dutsen Dala

  3. Fito da hanyoyin tsafi da bori wanda
   sarakunan suka yi domin neman kariyar
   aljannu daga abokan gaba.
  Waxannan abubuwa da muka lissafa da sauran
ire-irensu sune suka nesanta talakawa daga
sarakunan Kano na wancan lokaci. Talakawa suka
qi su matuqa har ta kai suna yi musu mummunar
addu'a, suna fatan Allah ya gaggauta karyewar
mulkinsu. Saboda wannan ne da Fulani suka fara
sukan sarakunan Have saboda waxannan halaye
nasu sai talakawa suka dinga saurarar su suna basu
goyon baya.
  Game kuma da yaqin Kano da Kastina wanda
aka dinga yi akai-akai tun zamanin Rumfa sai aka
samu qarewarsa a zamanin Sarkin Kano Shekarau
xan Alhaji, inda malaman Kano, su Atuman da
malam Bawa da Limamin „Yandoya, suka yi sulhu
tsakanin Kano da Katsina aka daina yaqin juna. To
amma kuma Sarki Shekarau sai ya fito da kama
matan talakawa da qwace musu dukiya tasu. Duk
matar da ya gani yayi sha'awa tata, ko yaji
labarinta a gidan wani talaka sai a aika a kamota a
kawo masa ita. Haka in yayi sha'awar abin talaka
sai yasa a qwato abin a kawo masa. Waxannan
halaye sune suka jawo aka tuve shi bayan shekara
biyu da sarauta, wato (1649-1651).            162
Kano Qwaryar Qira…...

    Wannan hali da Kano ta shiga na zalunci ya
jawo hankalin wasu malamai masu son gyara
harkar tafi da talakawa domin a sa ta akan
qa'idojin shari'a. Shehu Abdullahi Siqqa shi ne
Malamin da ya tashi tsaye ya na yiwa sarakuna
wa'azi akan su bi shari' a da sunnar Manzon Allah
cikin ayyukansu na mulkin jama'a. Abdullahi
Siqqa mutumin wani qauye ne Zawaciki mai nisan
kilomita biyar a kudu maso yamma daga birnin
Kano, a hanyar Fanshekara. Da ya shigo cikin
birnin Kano sai ya gina gidansa da masallacinsa a
Unguwar Gwale. Abdullahi Siqqa cikakken
malami ne, wanda yayi yawon neman ilimi tun
daga Kano har Fezzan da Agadas, kuma bafulatani
ne Baqadire na reshen Ahlal bait. Shi ne farkon
bafulatanin da ya fara kiran musulmi suyi jihadi
domin abi sharia a cikin duk wata rayuwa ta
talakawa da sarakuua.
    A zamanin Sarkin Kano Kukuna ne (1652-
1660) wa'azin Abdullahi Siqqa ya jawo masa
rigima da Sarkin Kano Kukuna da fadawansa, har
Shehun yayi fushi ya bar birni ya koma qauyensu
Zawaciki. Bayan barinsa Kano ne Qwararrafawa
suka afkawa Kano da yaqi Sarkin Kano Kukuna
da fadawansa suka gudu zuwa Auyo, suka bar
talakawa cikin musibar yaqi babu mai karesu.
Bayan wannan musiba ne ta Qwararrafa Sarki ya            163
           …………….Daga Dutsen Dala

dawo kuma ya rarrashi Shehu Abdullahi Siqqa ya
dawo cikin birni da zama domin ya taimakawa
Sarkin da abin da Allah ya hore masa na ilimi.
    Wataqila Sarkin Kano Kukuna ya dawo da
Abdullahi Siqqa ne saboda muhimmancin
malamin wajen ayyukan ilimi da na arziqin qasa.
Gama a wancan lokacin mabiyan Shehu Abdullahi
Siqqa masu yawa ne, kuma masu matuqar amfani
game da yaxa arziqin Kano, da kasuwanci.
Waxannan mutane sune suka kafa masana‟antar
yin alli na kaxin zare a unguwar Xandago. Suka
kafa masana‟antar yin tufafi na maza da mata a
unguwar Gawo da Makasa, inda ake saqar
gwadduna da zannuwan mata irin su saqaqqe da
bunu da sauransu.
    Haka kuma suka kafa masana‟antar yin
sabulun kanwa na wanke tufafi. Waxannan
masana'antu su suke ciyar da kasuwar Kurmi da
irin abubuwan da suke yi waxanda ake kaiwa
qasashen Turabulus, Agadas, da sauran qasashen
Afirka ta yamma. Cibiyar ilimi kuma wacce ya
kafa ita ce ta bunqasa har ta fitar da Malam Usman
na Hausawa xaya daga cikin almajiran Shehu
Usmanu na Kano waxanda suka yi tajdidi a Kano
a 1805 - 1807, inda suka kafa mulkin Fulani.
           164
Kano Qwaryar Qira…...

    Bayan Kukuna ne kuma Qwararrafawa suka
komo Kano da yaqinsu na qarshe a zamanin
Sarkin Kano Daxi (1670-1703). A lokacin Daxi ne
Kano ta kai lalacewa ta qarshe saboda Sarki ya bar
komai na gyara Kano da ci gabanta sai yawace-
yawace da rayuwar jin daxi da bin sha'awa tasa.
Don haka da mayaqan Qwararrafa suka iso Kano
sai suka sami gari tulus ba wata wahala wajen yaqi
da mutanen.
    Don haka da Qwararrafa suka faxa gari da
yaqi Sarki Daxi yayi xan abin da zai iya yi na kare
gari, ya ga ba zai iya ba sai kawai ya gudu ya tafi
Daura domin ya tsira, ya bar talakawan Kano a
hannun Allah, Qwararrafa suka kusa halaka birnin
Kano. Wannan zuwa na Qwararrafawa shi ne
qarshen zuwansu yaqi Kano. To amma qarshen
yaqin Qwararrafawa ba shi ne qarshen yaqe-yaqe
a Kano ba. Gama bayan su sai kuma sauran 'ya
'yan Bawo suka yiwa Kano tsinke suka dinga
xirkar ta da yaqi xaya bayan xaya, gama sun ga
Kano ta faxi gasassa.
    Daga cikin qasashen Hausa bakwai ta
'ya'yan Bawo Zamfara ita ce ta fara kawo wa Kano
harin yaqi a zamanin Sarkin Kano Sharifa xan
Daxi. Wataqila Zamafarawa sun manta da
tushensu na Kano, shi yasa Sarkinsu ya aiko da
yaqi Kano a qarqashin shugabancin wani            165
            …………….Daga Dutsen Dala

Bazamfare wai shi Yakubu xan Muzuru. Da
Zamfarawa suka zo Kano sai Kanawa suka fita
suka tare su a 'Yargaya, su kai yaqi tsakaninsu.
Zamfarawa suka rinjayi Kanawa matukar rinjaya.
Kanawa suka watse tilas, aka kashe Kanawa kisa
mai tsanani, suka gudu suka bar Sarki shi kaxai sai
wasu daga cikin maqarrabansa. Saboda ruxewar
Sarki da mutanensa sai da qyar suka gane hanyar
birninsu suka dawo gida.
    Wannan hali na a gudu a bar Sarki shi kaxai
a wajen yaqi wataqila alama ce ta cewa talakawa
sun gaji da zalunce-zaluncen sarakunansu
musamman shi kansa Sarkin Kano Sharifa.
Tarihin Kano ya nuna cewa Sarkin Kano
Muhammadu Sharifa shi ne ya fara abu bakwai a
cikin wannan gari na Kano, dukkansu na zalunci.
Waxannan abubuwa kuwa sune,
    Qaruwa da Rantsuwa da Matar-fada da
'Yan-dawaki da Qwaro da Mugun-haraji ga
dukkan budurwa idan ta yi aure da Kuxin kasuwar
Kurmi kowanne wata da sauran ire-irensu. ldan ka
haxa waxannan da zalunce-zalunce da jangali
wanda Sarkin Kano Kutumbi (1623-1648) ya
qirqiro da kamen matan talakawa da Sarkin Kano
Shekarau xan Alhaji (1649-1651) ya fito da shi za
ka ga cewa talakawan Kano suna da hujjar qin
sarakunan Kutumbawa. Kuma a wannan zamani            166
Kano Qwaryar Qira…...

ne kuma aka fara ganin farin kuxi, wato wuri a
qasar Hausa. Da yake kasuwar Kano ita ce cibiyar
ciniki a duk qasashen Hausa sai farin kuxi suka
qara bunqasa arziqin Kano da kasuwancinta.
Wannan abu shi ya tada kwaxayin Gobirawa har
yawunsu ya tsinke, suka dubi Kano duban
daqwalwar kaza gasasshiya.
    A zamanin Sarkin Kano Muhammadu
Kumbari xan Sharifa ne (1731-1743) gabar Kano
da Gobir ta tsananta a zamanin Sarkin Gobir Soba.
Idan Gobirawa suka yi rinjaye yau, Kanawa suyi
rinjanye gobe, suka yi ta yin haka kowace rana har
Gobirawa suka gaji suka koma gida domin su qara
shirya lokacin da zasu sake dawowa. Shi kuma
Sarki Kumbari a nasa shirin sai ya qara tsanantawa
talakawa, malamai da attajirai, wajen sa musu
sabon haraji da qarawa akan na da. Kumbari ya
tsananta kuxin kasuwa wanda ubansa Sharifa
(1703-1731) ya fara sawa, har kasuwa ta kusa
mutuwa. Bayan wannan kuma yasa kuxin jiziya
cikin gari har akan malaman sa. Wannan irin
haraji ba'a tava yin irinsa a Kano ba sai a zamanin
Sarki Kumbari. Gari duka ya tsananta, har
Larabawa suka riqa fita daga birni suna komawa
Katsina, talakawa kuma suka watse zuwa
qauyuka.
            167
           …………….Daga Dutsen Dala

   Wannan matsayi na Kano a zamanin
Kumbari shi ya ci gaba har zamanin xansa Alhaji
Kabi xan Kumbari (1743-1753). A zamanin Alhaji
Kabi ne Kano ta kai qarshen rauninta ta faxi
warwar. A Gobir, kuma Babari xan Ibn Ashe
(1742-1770) ya zama Sarkin Gobir, ya gaji Sarkin
Gobir Soba. Da Sarkin Gobir Babari ya ga Alhaji
Kabi yaci sarautar Kano sai ya aika masa da
neman sulhu tsakanin Kano da Gobir, amma,
Alhaji Kabi ya qi yin sulhu da Gobir, yace shi
dankwara ne daidai kan kowa. Saboda wannan ne
Sarkin Gobir Babari ya xaura yaqi mai qarfi ya
taho Kano domin xiban ganima. Babari yazo Kano
tare da xansa Bawa wanda daga baya ya zama
sarkin Gobir, sannan yana hakimi. A wannan
zuwa na Gobirawa ne suka sami Kano ta faxi
gasassa saboda rauninta. Talakawa sun watse sun
bar Sarki Kabi saboda haka ya rasa yadda zai yi da
mutanensa. Su kuma Gobirawa da suka ga wannan
rauni nasa sai suka zauna suka miqe qafafuwansu
a Kano suna yiwa talakawa waso da kisa a kullum,
har suka qafa qauyuka guda biyu na mayaqan su a
arewa da birnin Kano, a kan hanyar Dambatta.
Gurin da Sarkin Gobir ya zauna tare da rundinarsa
ta yaqi sai aka sawa gurin Gobirawa, inda kuma
xansa Bawa, Baciran Gobir ya zauna da tasa
rundinar ita ma aka sa mata Bacirawa. Waxannan           168
Kano Qwaryar Qira…...

qauyuka har yanzu suna nan a wannan guri kuma
mazauna cikinsu na asali Gobirawa ne tun daga
wancan lokaci.

GAM DA HARIN TAJDIDIN
SHEHU USMANU(3)
    Waxannan abubuwa da muka faxa a sama
na yaqe-yaqen zalunci, da qin talakawa sune suka
karya qasashen Hausa har da Kano. Bayan yaqin
Gobirawa ne na Sarkin Gobir Babari aka samu
zaman lafiya a Kano a cikin zamanin Sarkin Kano
Yaji na biyu (1753-1768) har talakawa suka dinga
komawa cikin birni, saboda qarancin cuta da
zalunci irin na qwace, sai dai na haraji da sauran
irinsu kamarsu jangali wanda Fulani ba sa so.
    Wannan zaman lafiya da aka samu ya
jawowa Kano komowar kasuwancita da aikin
noma wanda ya farfaxo da arziqinta na da.
Wannan kuma yasa Sarkin Kano Babba Zaki
(1768-1779) ya dawowa da Kano ruhinta, ya
kyautata harkar mulki da shirin rundinonin yaqi da
samun sababbin makamai irinsu bindiga. Babba
Zaki shi ne ya fito da qungiyar mayaqan „yan
bindiga, ya kuma nemo abokansa larabawan Libya
suka bashi mutane masu koyawa mayaqan bindiga
tun daga wancan lokaci. Shi ne Sarki na farko a
Kano wanda ya fara amfani da 'yan bindiga a            169
           …………….Daga Dutsen Dala

wajen yaqi har sauran sarakunan bayansa suka
gada. Shi ne kuma ya tsara fadar Sarkin Kano
yadda take a yanzu. Ya fito da Dogarai waxanda
zasu kareshi. Zamansa da tashinsa, baza a gani ba.
Ya fito da Sallama, ba mai ganinsa sai ta hannun
bayin Sarki, ya kuma rabawa manyan bayinsa
Hakimai da bayin Sarki domin su dubasu. Ba
Hakimin da zai gan shi sai dai ta hannun bawan da
yake duba shi.
    Duk da zaman lafiyar da aka samu a Kano
tun daga qarewar yaqe-yaqen 'ya'yan Bawo,
zalunce-zaluncen sarakuna da lalacewa tasu basu
qare ba. Saboda haka guna-gunin talakawa da yin
Allah wadai da sarakuna bai qare ba. Amma kuma
abin mamaki shi ne ba wani bahaushe a cikin
Hausawan qasarnan da ya tava fitowa fili ya
la'anci waxannan miyagun abubuwa da sarakunan
Hausa har na Kano suke yi a kullum.
    Wannan aiki na kuvutar da talakawa daga
zalunce-zaluncen waxancan sarakuna sai Fulani ne
kawai suka fara yi a duk qasashen Hausa. An ce
Fulani sun fara zuwa Kano su zauna tun zamanin
Sarkin Kano Yakubu xan Abdullahi Barja (1452-
1463). Abubuwan da suka kawo su kuwa sune
yaxa ilimi da samun qasa mai albarka saboda kiwo
da noma. A saboda haka suka shiga ko ina a Kano
suka zauna tare da mutane, suna kiwo, suna           170
Kano Qwaryar Qira…...

malanta da sauran mu'amula da mutane, wajen
auratayya da hulxar kasuwanci har suka zama
mutane xaya da Kanawa ba bambanci sai dai na
ilimi da arziqin dabbobi.
    Da Sarkin Kano Kutumbi ya fito da Jangali
sai Fulani suka zama sune masu tarawa Sarki irin
wannan haraji daga sauran 'yan‟uwansu na ko ina,
su kawo masa. Ta haka ne suka san inda duk 'yan
uwansu suke zaune a qasashen Hausa, da Borno,
domin karvar Jangali. Wataqila ta wannan hanyar
sadarwa ne wa'azin Shehu Usmanu ya riski sauran
Fulanin qasar Hausa da na Borno. Bayan aikin
Jangali kuma sai sarakunan Have suka sa su zama
magatakarda tasu, sune alqalansu, sune kuma
malamansu na fada. Saboda wannan ne Fulani
suka qara haxewa da Hausawa suka zama abu
xaya. wannan abu haka yake har a nan Kano.
    A zamanin Sarkin Kano Muhammadu
Alwali na biyu ne (1781-1807) wa'azin Shehu
Usman Xan Fodio ya bayyana, kuma ya yaxu a
duk qasashen Hausa da Borno. Da Malaman Kano
suka ji bayyanar Shehu a garin Xagel sai suka tafi
wurinsa suka yi masa, caffa suka karvo iznin yin
wa'azi a kan zalunci da al'adun maguzanci
waxanda sarakunan Have suke yi. Wani abin
al'ajabin tarihi shi ne cikin waxannan malamai na
Fulani da suka je wajen Shehu suka yi caffa,            171
            …………….Daga Dutsen Dala

akwai ma'aikatan Sarkin Kano Alwali da wasu
daga cikin 'yan majalisa tasa a cikinsu, kuma Sarki
Alwali xin shi ya basu izni don suje su samo
albarka saboda amfanin Kano baki xaya. Mutanen
Kano sun tabbatar da cewa Sarkin Kano
Muhammadu Alwali na biyu wanda Fulanin Kano
suka yaqa a tarzomar tajdidin Shehu Usmanu,
cikakken musulmi ne, mai qaunar malamai da
ibada. Saboda haka ne ma yasa aka halaka Dirki,
gunkin da sarakunan Kano suke bautawa tun
zamanin Sarkin Kano Nazaki xan Zaki (1618-
1623). Wannan sadaukantaka ta kare addinin
mususlunci da Alwali yayi ta jawo masa baqin jini
daga wajen bokayen Sarki na Dirki, saboda haka
suka dinga yiwa Sarkin Kano Alwali jafa‟i da
fatan qarewar mulkinsa. Su kuma malaman Fulani
da suka fara jihadi a Kano 1805, sai suka xauki
sarkin Kano Alwali a kafiri wai don ya qi tuba ya
bi Shehu. Wannan ra'ayi na Fulanin Kano bai sami
karvuwa ba a wajen mutanen Kano, waxanda suka
yarda da cewa Alwali cikakken musulmi ne, kuma
kashe shi da aka yi mutuwa ce yayi ta shahada.
   Waxannan abubuwa sune suka sa Sarkin
Kano Alwali ya shiga tsaka mai wuya. A gida ya
halaka Dirki domin a daina bautar gunki, a bi
addinin musulunci. Wannan abu ya jawo masa
baqin jini da qiyayya daga wajen mutanensa, har            172
Kano Qwaryar Qira…...

suna fatan Allah ya kauda shi yadda ya kauda
gunkinsu. Daga wajen malaman Fulani kuma
maimakon su gode masa, su goyi bayansa saboda
wannan aiki da yayi na kashe gunki, sai suka rufe
idanuwansu daga ganin wannan alheri, kuma suka
rufe kunnuwansu daga jin duk wani abu da za a
gaya musu na alheri game da shi.
    Saboda waxannan dalilai da muka ambata
ana iya cewa tarihin Kano ko malamansa ba suyi
wa Sarkin Kano Alwali adalci ba. Yayi shekaru
ishirin da shida (1781-1807) yana sarauta, kuma
ba shakka yayi abubuwa na alheri masu yawa, ciki
har da taimakawa Fulani talakawansa, amma duk
an share su, an yi masa qagen shi kafiri ne ba tare
da wata hujja ta gaskiya ba. Amma wani dace na
mulkin Kutumbawa shi ne mulkin ya fara da
Muhammadu Alwali Kutumbi, kuma ya kare da
Muhammadu Alwali na biyu. An ya ba Musulunci
a waxannan sunaye?

TARBIYAR YARA KAFIN ZUWAN
MUSULUNCI(4)
  An karanta a baya cewa cikin shugabannin
Kano guda goma sha xaya waxanda suka fara kafa
mulki a Kano akwai xaya daga cikin su mai suna
Doron Maje wanda shi ne ya ke xauke da sarautar
Sarkin samarin Kano, domin tarbiyar matasa maza            173
           …………….Daga Dutsen Dala

da mata na duka qasar Kano. An dai san cewa a
duk inda matasa suke a qasa, basa tafiya sai cikin
qungiya tasu. In maza ne haka zaka ga suna tafe,
ko suna zaune su da yawa suna wasa, ko suna yin
wani abu na kansu, ko na nishaxi, ko na hira. Idan
ma mata ne haka za ka gansu tare a wuri guda ko
suna hira ko suna gaxa da raye-raye da waqe-
waqe. To saboda ayi wa waxannan qungiyoyi na
matasa jagora da tarbiya sai mai garin ya naxa
musu Sarkin Sauri (Sarkin Samari) a cikin su, ko
kuma in su suka zavi xaya daga cikinsu ya zama
Sarkin Sauri sai maigari ya amince da shi ya san
da zamansa saboda alaqa tsakanin hukuma da
yara. Haka kuma maigari zai ba matasan filin
wasa wanda zasu dinga yin harkokin su na
wasannin motsa jiki na maza da na mata. Wannan
gurin wasa shi ake qira Datsa ko dandalin wasa.

ABUBUWAN DA AKE KOYAWA MATASA(5)
    Abubuwan da ake koya wa matasa a
wancan lokaci ba a rubuce suke ba. Abubuwa ne
waxanda aka saba yinsu tun iyaye da kakanni
domin rayuwa ta yau da kullum. Kuma hanyar da
ake bi ta koyawa iri biyu ce
    (a) hanyar koyarwa a aikace da nuna
    yadda za'a yi abu
           174
Kano Qwaryar Qira…...

    (b) Hanyar kwaikwayon manyan gari bisa
    abin da yara suka ga suna so, ko ba sa so.
    Hanyar koyarwa a kan nuni ta haxa da
aiyukan gida na yau da kullum. Idan „yan mata ne
za a ringa nuna musu yadda zasu taimaki iyayensu
mata wajen girke-girken abinci da renon jarirai da
sauran aiyukan da matan gida suke yiwa iyalinsu,
kamar dafa giya da sai da ita, noman rani da na
damina domin riqon kai ko da basu da aure, don
kada su yi karuwanci.    Su kuma yara maza
zasu bi iyayensu domin su koyi yadda ake
ayyukan gyaran muhalli da gina shi saboda
iyalinsu su sami gurin kwana mai aminci. Haka
kuma za'a koya musu noma da kiwon dabbobi da
irin sana'o'in da ake yi a gari kamar su rini, da
saqar tufafi da kayan gida irin su saqar zana, da
kan xaki, da tabarma, da asabari, da tufaniya, na
rufe qofar xaki. Haka kuma za'a koya musu xinkin
tufafi da aikin fata da qirar kayan aikin gona da na
gida da na wanzanci da sauran abubuwan da
jama'ar gari suke buqata. Kafin allura tazo Kano
da gashin kaza ake yin xinke-xinken tufafin maza
da na mata.
    Hanya ta biyu a tarbiyar yara ita ce ta
hanyar da matasa suke bi domin kwaikwayon
manyan gari. Tun da su matasa ba cikakken
hankali ne da su ba amma kuma suna xokin su            175
            …………….Daga Dutsen Dala

kwaikwayi iyayensu, kan ayyukan da suka gani
suna yi to suma sai su dinga yi, amma basu san
kyawun abun ba ko rashin kyawun sa, har sai an
shiryar dasu an nuna musu yadda za suyi. Ga
kuma xan misali akan abubuwan da suke koyo da
kansu domin neman shiryar da su hanya
madaidaiciya.

1)   SHUGABANCI:
    Ko wacce qungiya ta samari da 'yan mata
wato matasa, ta na da shugabanta wanda sauran
yara suka amince masa, shi zai yi hani da horo, shi
kuma yana da waziransa na kusa da shi waxanda
an yarda sune masu zartar da umarnin shugaban.
Irin wannan shugabanci na matasa, ba zave ake yi
ba, a'a halin yaro ne na haquri da tausayi, da yin
sulhu tsakanin yara da kuma jarimtakarsa take
sawa shauran yara duk su bi shi. Duk matashin da
yake zaluntar shauran yara to basa amince masa
balle ya zama shugaba.

2)  AYYUKAN DA SUKE YIWA JAMA'AR
   GARINSU:-
   Irin ayyukan da qungiyar samari suke yiwa
qauyukansu galibi ba sa su a keyi suyi ba, a'a sune
kawai suke yin ayyukan ko jama'a na so ko ba sa
so.Wani lokaci ayyukan da suke yi yana yiwa            176
Kano Qwaryar Qira…...

jama'a amfani, ko da yake da wauta suke yin
ayyukan, wani lokaci kuwa ayyukan nasu fitina ne
ga iyaye da shauran jama'ar gari. Don haka dole a
tsawata musu, a hana su yin ayyukan, ko a shiryar
dasu akan abin. Qungiyoyin matasa a kowane gari
sune 'yan kanzagin qin abin da mutanen gari basa
so. Idan sata ce suka ji manya basa so kowa yayi,
to sune zasu fara tona asirin duk wanda ya zama
varawo a garin, suyi tayi masa zambo suna
zaginsa a waqoqi iri dabam-dabam, a dukkan
kwararo da wajen wasanninsu. Imma sun ga
manyan gari suna yi musu dariya don suna
sha'awar abin da suke yi to, har sai su shige
makaxi da rawa, su dinga bin wanda suka ji ko
suka ga yayi sata suna jifansa da duwatsu, suna
zaginsa, suna cewa varawo-varawo, har ma su
kashe shi ko su yi masa illa, in dai jama'ar gari
basu cece shi ba. In karuwanci ne, ko shan abin
maye, ko vata 'yan matan gari ne jama'a basa so,
to yaran gari sune zasu fito su yaqi masu yi ta
wannan hanyar har sai masu yin waxannan
miyagun abubuwa sun bari, ko kuma manyan gari
sun cece su.
    In kuma wani abu mutanen gari suke buqata
ga Allah, kamar ruwan sama a lokacin fari, ko
yayewar wata annoba, ko lokacin da rana ta kama
wata ya zama yana zazzavi, da irin waxannan            177
            …………….Daga Dutsen Dala

abubuwa to sune zasu fara fitowa da kaxe-kaxensu
da waqe-waqensu na wauta da quruciya, suna nasu
roqon, wataqila Allah ya karvi nasu roqon ya
biyawa mutanen garin buqatarsu, kafin ma su su
fito su roqe shi. Gama Yara tuni sun yi magana da
Shi da harshensu wanda ya sha babban da na
manya.
    Saboda haka ba abin mamaki ba ne in aka
ce yara sun fi manya kusanci ga Allah, kuma sun
fi su son abin da Allah yake so ayi da kuma qin
abin da baya so ayi, gama su basu balaga ba balle
su san ha'inci da qwange wajen bin Allah. Tun da
yake suna bin iyayensu, guraren ibada, da inda ake
yin taro na alheri, kamar wajen xaurin aure da
suna da jana'iza, a waxannan gurare sukan ji
laifuffukan da mutanen gari basa so ayi, to fa su in
har suka kama mai yin wannan laifi hukunci irin
nasu zasu yi masa, idan bai yi sa'a manya sun hana
ba. Hukuncin yara kuwa na wauta ne, wato ihu ne
da jifa da zagi da cizo da suka har sai sun lahanta
mai laifi, koma su kashe shi, saboda rashin sanin
shari'a. Don haka ne manyan gari suke tsawatar
musu, su shiryar da su har suyi hankali.

3)  AYYUKAN DATSA
   Abubuwan da qungiyoyin samari da
„yammata suke yi na maguzanci tun lokacin Have            178
Kano Qwaryar Qira…...

har yanzu ba'a daina su ba a Kano. Koda yake dai
qarfin musulunci ya rage su da yawa duk da haka
suna nan. Na farko dai daga cikin waxannan al'adu
shi ne kafa gurin wasan samari da 'yammata a
cikin alqaryu. Ana kiran waxannan guraren
wasanni Dandali wato “Dandal” da Barbaci. A
qauyuka kuwa sunan gurin wasan samari da
'yammata Datsa. Datsa ita ce kalmar da ake
amfani da ita a ko'ina a Kano, har ma ana yin
karin magana da ita inda ake cewa "budurwa a
Datsa ta kowa ce". A duk inda Datsa take to a nan
ne yaran gari maza da mata suke taruwa, suyi
wasa da daddare, „yammata su ware suyi nasu irin
wasan na rawa da waqa kamar yadda samari suke
nasu na motsa jiki da wasa qwaqwalwa irinsu “A
tamango-tamango”, da “Allan ba ku”, da
“Langa”, ko “kulli-kucciya” da shauransu. Ko
wace Datsa tana da shuwagabanninta da kuma
dokokin ta wanda kowa ya karya za'a iya yi masa
hukunci.
    Shekarun wasanni a Datsa kuma suna
farawa ne daga yin kaciya zuwa shekarun yin aure
ga maza, 'yammata kuma daga shekara biyar
galibi zuwa sha biyar ko lokacin da ta sami miji.
Ga kuma yadda tsarin Datsa yake tafiya.
            179
           …………….Daga Dutsen Dala

1.  Shugaban Samari, wanda tuni kaji yadda
   shauran yara suke bashi shugabanci, kuma
   su karvi umarninsa da horansa.
2.  Sarauniyar 'yammata, ita ma halaye na
   gari da hazaqa da kyau ne su ke sa
   „yammata su bita su karvi umarninta
3.  Takata ko Laima:- Shi Takata shugaba ne
   yake naxa shi, kuma galibi ana zaven yaro
   mai kwarjini da rashin tsoro asa shi a
   Takata. Aikin Takata shi ne qulla zuminci
   da fahimtar juna tsakanin samari da
   'yammatan Datsa. Don haka kullum yana
   saduwa da sarauniya don suyi aiki tare.
   Kuma har ila yau dai Takata shi ne mai
   tsare mutuncin Datsa, ya hana faxa tsakanin
   samari ko tsakanin 'yammata, kuma ya hana
   duk wani saurayi na wata Datsa ya xauki
   budurwar Datsar da yake mulki, in ba shiri
   tsakanin Datsa tasa da ta saurayin da yazo
   neman 'yammatan Datsa tasa.

DOKOKIN DATSA(6)
    Yadda kowacce hukuma, ko qungiyar
mutane take kafa dokokin tafiyar da lamarinta na
yau da kullum, haka ma yara suke kafa dokokin
tafiyar da lamarin Datsar qauyensu na yau da
           180
Kano Qwaryar Qira…...

kullum. Dokokin da ake kafawa a Datsa sun haxa
da waxannan.

1.   Doka ce akan kowane yaron da yake wasa
   a Datsa, yazo aikn gayya a duk lokacin da
   aka neme shi.
2.  Duk saurayin da zai yi zance da budurwa
   tasa, ko su tafi tsarince sai yabi ta kan
   Takata, kuma ya biya goron sarauniya.
3.  Ba a yarda saurayi ya tava xan tofin
   budurwa tasa ba a lokacin yin tsarince wai
   don ya ga tsiraicinta. Duk saurayin da yayi
   haka ya zama mai neman ya koyi lalata ke
   nan don haka ya zama xan banza, sai a
   dinga yi masa zambo ana zaginsa har sai ya
   gudu ya bar Datsan don yayi abin kunya.

   Tsarince dai a al'adar maguzawa shi ne yaro
ya xauko budurwa tasa daga Datsa ya kawo ta
gidansu, a basu tabarma su kwana a xaki xaya
suna rungume da juna, amma kowa da durwatasa a
xaure, ba mai neman yayi lalata a cikinsu. Ko da a
Datsa xin ma yaro yana iya jan budurwa tasa su
kama wani gindin itace, ko wani sayi su rungume
junansu, su na zance, har a tashi daga datsa sannan
su rabu, amma ba mai neman wani da lalata.
Tsarince a wajen Maguzawa hanya ce ta sada aure            181
            …………….Daga Dutsen Dala

tsakanin yaro da yarinya don haka abin alheri ne a
gurinsu, ba na lalata ba.

4.   BAYAN DATSA
    Idan aka yi wa saurayi da budurwa aure to
sun fita kenan daga Datsa, amma ba zasu rabu da
ita nan da nan ba. Ita budurwa yayin da ta shiga
xakin mijinta, to sai qawayenta da qannenta yara
su dinga zuwa gidan ta, da daddare suna yin hira,
su na tatsuniyar gizo da qoqi, ana hira ana dariya
don a xebe mata kewar Datsa, taga kamar ba wani
abu da ya canja a rayuwarta ta budurci. Haka yara
zasu dinga zuwa wurinta yin tatsuniya har ta saba,
ta san ita matar aure ce. Idan ma amarya tana da
farin jini a lokacin da take Datsa, kuma mijinta
yana da sakin fuska ga yara, to an dinga ziyara tata
ke nan har lokaci mai tsawo. Saboda haka a
kullum tana jin labarin Datsa da shauran
„yammata da samarin da suka yi aure bayanta.
    Su kuma samari bayan sun yi aure sun fita
daga datsa sai su kafa qungiya tasu daban da ta
yaran Datsar dan kuwa yanzu sun zama samarin
gari ba yaran gari ba. Banbancin wannan qungiya
da ta Datsa shi ne ita wannan qungiyar ta samari
ce gurguzu, ba „yammata a cikinta, suma sukan yi
nasu taron hirar ne a gurin da ake kira Makwalla,
ba nisa daga Datsa inda zasu ringa aiken yara            182
Kano Qwaryar Qira…...

gidajensu suna kaiwa matansu saqo. Su waxannan
samari sune suke shiga shauran sana'o'in gari
bayan noma, irin su xinki da saqa da qira da
sassaqa. Wasu su shiga kasuwanci wasu su xau
gafaka, su shiga makaranta dan su zama Malaman
gari nan gaba. Har ila yau dai daga cikinsu ake
samun masu shiga tauri da farauta da tara karnuka,
domin koyon yaqi.

5.   FARAUTA DA TAURI
  Samarin da suka xauki yin farauta a gari, sai su
tara karnuka masu yawa, kuma su dinga cin
maganin qarfe da shauran magungunan tsare kai
saboda a wajen farauta akan yi faxa da abokan
gaba na wani guri. Ita farauta ana haxa ta ne a duk
qarshen shekara bayan an yi girbi, kaka ta zo.
Anan cikin birnin Kano ana haxa wannan farauta
ne a Kukar Bulukiya ta gindin Dala. Ka dai rigaya
ka karanta a baya cewa an fara kafa birnin Kano
ne ta farauta. Wato 'yan farauta ne suka fara kafa
wannan gari. To har yanzu ba'a daina wannan
sana' a ta farauta ba a cikin birnin Kano. In aka zo
haxa farautar lahadi a da, zaka ga saurayi fiye da
xari biyu, karnuka fiye da xari uku. A wannan
rana ce kowane xan farauta yake yiwa karnukansa
ado a wuya, da guraye iri daban-daban, kai wani
Karen ma sai ka ganshi an yi masa ado har da goto            183
            …………….Daga Dutsen Dala

na gashin jimina a wuyansa. Da an busa qahon
farauta sai kaga karnuka suna ruri, suna rimi, suna
hawa kafaxar iyayen gijinsu, suna tsuma dan
murna da sanin abin da ake so suyi a wannan rana.
Karnukan farauta, kamar dawakin yaqi suke a
Kano. A Kano, musamman a zamanin Sarkin
Kano Abdullahi xan Dabo, dawakin yaqi in suka ji
an buga bindiga "durum" duk sai, su xauki
haniniya da tsuma, su na rimi, su na haniniya don
sun san rannan za a tafi fagen fama.
    Qungiyar 'yan farauta, kamar kowacce
qungiya ta samari, ita ma tana da
shuwagabanninta, masu horo da hani, koda yake
qungiya ce, dai ta ganin dama. Muhimmai daga
cikin shuwagabanninta sune babban shugaban 'yan
farautar gari. Wannan mutum ba naxa shi ake
yiba, a' a shauran „yan farauta ne suke amincewa
da shi, su sa shi a gaba saboda qarfinsa ko farin
jininsa, ko karamcinsa da haqurinsa, to shi irin
wannan mutum shi ne yake zama shugaban 'yan
farauta, kuma shi ne mai haxa ta, ya gayyaci
shauran unguwoyi ko qauyuka a duk lokacin da
yake son haxa farauta. Shugaba na biyu kuma shi
ne Malamin 'yan farauta. Shi kuma aikinsa shi ne
bada sa'ar fita farauta da xaure dawa, don a sami
nama, kuma ayi farauta lafiya. Ka dai san cewa ko
da yara ne zasu fita farautar gafiya, to sai sun tafi            184
Kano Qwaryar Qira…...

da yaro, da ya sauqe Alqur'ani a cikinsu dan yayi
musu yanka.
   A zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero
(1926-1953) Shugaban „yan farautar cikin birni na
wancan lokacin shi ne Baba na Dumfa, kuma
Malamin farauta shi ne Malam Tingile. Dukkansu
a 'Yan tandu suke, kusa da Sararin Kabuwaya,
arewa da kasuwar birni. In an haxa farauta a cikin
birnin Kano galibi ana fita zuwa Dawan Kaya ne,
har Janguza. In kuma gabas aka yi to har bakin
qoramar Sauna, ko Jogana.
AMFANIN FARAUTA
   Farauta a qasar Hausa nishaxi ce ta samari,
kamar yadda shauran wasanni suke. Duk lokacin
da aka gama kauda amfanin goma kuma
abubuwan noma suka zo qarshe to samari da
'yammata sun shiga wasanni iri-iri ke nan na jin
daxi da nishaxi, don kuwa abinci ya samu.
   A nan Kano in lokacin girbin dawa yazo
wato daga watan Nuwamba, ko na Disamba, to
zaka ga samarin gari suna share filayen wasanni iri
dabam-dabam, yaran mahauta su share fage
saboda wasan dambe, 'ya'yan maguzawa su share
filayen kokawa da wasan shanci, ya' yan fulani su
kafa filin shaxi wato sharo. Duk waxannan
wasanni da kaji suna da irin gangunan da ake            185
           …………….Daga Dutsen Dala

kaxawa masu yinsu don a zuga su su hassala dan
su yi jarimtaka. Kuma a wannan lokacin ne dai za'
a fara haxa farauta ana shirya biki na wasan tauri
da ake yi da kixan gangi da na kurya, don zuga
„yantauri suyi wasa da qarfe ko su karya takubba
da wuqaqe, ko kuma rana ta vacewa wasu a
cikinsu su huda cikinsu, su tafi lahira.
    Duk waxannan wasannin da kaji ana yi, ba
kawai don nishaxi da gasa ake yinsu ba, a' a ana
yinsu ne dan koyon jarimtaka ko juriya, da iya
kare kai da koyon yaqi, kuma farauta da tauri sune
suka fi kowanne wasa koya yaqi, da kare gari. Su
qungiyoyin „yan farauta in suna gari to ba kasafai
varayi suke zuwa sata garin ba, gama yadda
varawo yake bin dare haka ma „yan farauta suke
bin dare suna yin farauta. In kuwa suka ga varawo
a garinsu yazo da niyyar sata, aiko sai sun bi shi
sun kama shi sun miqawa hukuma koma in yayi
rashin sa' a su kashe shi har lahira.
    Tun zamanin sarakunan Have 'yan tauri
suke da muqami a fada, gama galibi su ake yiwa
sarautar qauye don su hana varayi sakewa, su
kuma tsare jama'a tasu daga hare-haren abokan
gaba. A da, ba a baiwa mutum sarautar qauye
wato dagaci sai an san shi shiryayye ne, kuma
jarimi ne. In har varayi suka zo garinsa zai iya
yaqi da su ya cisu, ko ya kore su. Haka kuma 'yan           186
Kano Qwaryar Qira…...

farauta su ake bawa sarautar Jarmai.
   A zamanin sarkin Kano Alu ne „yan tauri
suka sami martaba ba ta wasa ba. Gama Alu ya
kafa musu qungiya ta mayaqa wacce ake kiranta
qungiyar „YAN DABA. Wannan qungiya ba
wanda yake cikinta sai 'yan tauri da 'yan farauta
gurguzu, dan kuwa ita ce qungiyar masu walwala
da takobi, da kutufani. Shugaban wannan qungiya
shi ne Musa Kabuwaya na 'Yantandu ta cikin
Birnin Kano. Shi Musa shi Sarkin Kano Alu ya
naxa Jarmai saboda shima ya gaji kakansa Jarmai
Sulaimanu wanda ake kira Kabuwaya. Gidan
Jarmai Sulaimanu yana sararin Kabuwaya ta
'Yantandu inda har yanzu zuri'a tasa, da ta bayinsa
suke zaune. Shi Jarmai Sulaimanu yayi zamani da
Sarkin Kano Ibrahim Dabo.
   A cikin gagararrun „yan tauri waxanda suka
shahara a zamanin Sarkin Kano Alu akwai Jarmai
Dikko, wanda yake Gwale, da kuma Jarmai Dila,
mutumin Gwauron Maje ta qasar Xanbatta. Shi
jarmai Dila maharbi ne kuma shi Sarki Kano Alu
ya naxa Sarkin Gaya bayan an yi Basasa.
Waxannan Jarumai guda uku da kaji labarin su,
wato Jarmai Musa da Jarmai Dikko da Jarmai Dila
sune shuwagabannin „yan ta kife a zamanin Sarkin
Kano Alu domin kuwa basa jin tsoron duk wani
mahaluqi a fagen daga. A taqaice dai qungiyar            187
            …………….Daga Dutsen Dala

'yan tauri sune suke tsaron birni da qauyuka kafin
turawa su bayyana, kuma da turawa suka zo, su
suka fara xauka 'yan dokan N.A tare da Dogaran
Sarki don tsaron gari.
RASHIN AMFANIN FARAUTA
    Duk abubuwan da kaji a baya na amfanin
farauta da tauri a taqaice na kawo maka. To amma
duk da haka farauta da tauri sukan sa wasu illoli a
cikin jama'ar gari. Da farko dai idan xan farauta da
tauri ya riqa har tsafi da shirku yake yi dan biyan
buqata tasa ta duniya. To, kaga an kaucewa
addinin Musulunci an shiga bautar aljani da iblis.
    Kuma har ila yau 'yan tauri da farauta in
ba'a yi sa'ar su ba a gari sukan zama varayin dare
ko 'yan fashi masu tsare hanya da hantsi. Duk
lokacin da irin wannan ya afku a gari to mutanen
garin da maqwabtansu, ba zasu zauna cikin aminci
da kwanciyar hankali ba, sai sun sami maganin
abin daga hannun dagacin garin, da yaransa .
GUDUNMAWAR MAGUZAWAN FARKO
   Bayanin da muka yi a cikin littafin nan tun
daga farko har qarshe ya na nuna cewa ashe
mazauna Kano na farko ba zaman bilkara suka yi
ba. Sun yi zama ne na tsari da hankali, da hangen
nesa, a cikin rayuwatasu ta addini, da mulki, da
hulxa, da tarbiyar „ya‟yansu. Mafi yawa daga


            188
Kano Qwaryar Qira…...

cikin abubuwan da suka yi masu kyau har yanzu
muna cin moriya tasu. Amma a wajen tarbiyar
yara Maza da Mata a nan muka gaza, muka kasa
kwaikwayonsu.
    Abin nufi a nan shi ne Maguzawa sun
shirya hanyar tarbiyar „ya‟yansu Maza da Mata
tun waccan lokacin da babu cigaba ta yadda za su
ci gashin kansu a rayuwar yau da kullum, ta
hanyar noma da sana‟a ba tare da dogara da wani
ba. Wannan yasa „yar Ba-maguje ba za tayi
karuwanci ba domin ta ci da kanta. Sai ta dafa
giya ta kai kasuwa ta sayar ta biya buqatunta, ko
tayi noman rani tayi kayan miya ta sayar ko tana
da miji ko bata da shi, domin ta sami abin
masarufi.
    Haka kuma xan Ba-maguje ba ya bara, ba
ya roqo, ba ya barance a gurin wani, ba ya zaman
banza. Sai yayi noma da rani da damina ya kuma
yi sana‟a ta samun abin masarufi na yau da kullum
ko mai qanqantar sana‟ar domin ya dogara da
kansa. Waxannan abubuwa su muka kasa yiwa
„ya‟yanmu Maza da Mata har cigaban da muka
samu na addinin musulunci da na zamani. A
wannan hali sai kaxan ne daga cikin „ya‟yanmu na
yau suke kaiwa gaci wajen samun tarbiyya mai
kyau, har su amfani kansu da iyayensu da shauran
jama‟a.            189
            …………….Daga Dutsen Dala

        TUSHEN BAYANI

    SASHI NA XAYA
1.  Lugard, F.S. (1906) Tropical Dependency,
   London, Frank Cass pp 227 – 8.
2.  Muhammadu Bello, Infaqul – Maisur
   (Whitting: ed: 1951) pp. 2 -3.
3.  Jinju, M.H. (1990) Garkuwar Hausa da
   tafarkin cigaba, Kaduna, Fisba Media
   Services. Wannan littafi na Jinju yayi bayani
   ne akan asalin harshen Hausa, cewa an same
   shi ne daga harshen Hamawa na Misra.
   Misrawa kuwa Qibxawa ne. Abin da wannan
   littafi ya qunsa na nazarin harshen Hausa ya
   isa shaida akan abin da Lugard ya faxa na
   cewa asalin Hausawa da harshen su daga
   Misra ne.
4.  Lugard, F.S. (1906), opcit: pp 229 – 30.
   wannan Fir‟auna wanda aka ce sunan sa
   Barkhou, to a zamanin sa ne aka saida
   Annabi Yusufu ga Qibxawan Misra, daga
   baya Allah ya kuvutar da shi daga qangin
   bauta, har ya zama Azizun Misra wato ma‟aji
   da Hausa. An ce Fir‟auna Barkhou ya zo
   qasar Hausa da mayaqa kamar 700,000
   waxanda suka karaxe duk qasashen Hausa.
   Da yawa daga cikin su ba su koma Masar ba            190
Kano Qwaryar Qira…...

  sun yi zaman su a nan.
5. Labarin Hausawa da Maqwabtansu, na Farko.
  NNPC Zaria, (1970) pp 1 -3.
6. Musulmi sun ci Iraq ne a zamanin Halifan
  Annabi na farko, Sayyadi Abubakar (632-
  634). Wanda ya ci qasar shi ne General
  Khalid Bin Walid.
7. Hodgkin, T. (1960) Nigerian Perspectives: An
  Historical Anthology. O.U.P, p 54.
8. Hogben, S.J and Kirk – Greene, A.H.M
  (1966) The Emirates of Northen Nigeria: A
  Preliminary Survey of their Historical
  Tradition. O.U.P pp 147 – 8.
9. Ibid. p. 153
10. Ibid. p. 154

SASHI NA BIYU
1. An juyo wannan bayani daga littafin Physical
  Features of Kano Na B.A.W. Travallion,
  Metropolitan Kano: Report of the Twenty Year
  Development Plan, 1963 – 1983. Kano (1963).
  An fassara shi da Hausa an kuma qara wasu
  bayanan.
2. Malam Adamu na Ma‟aji: Al-I‟ilan Bi Tarikhi
  Kano, ba‟a buga shi ba.
3. Yakasai, T. (2004): The Story of Humble Life:
  and Autobiography APL Zaria p 3.            191
           …………….Daga Dutsen Dala

4. An samo wannan bayani daga maqala akan
  aikin noma wadda Musa Sani Dawakin Tofa ya
  gabatar a cikin: Adamu, M.U. (ed) Mulkin
  masarauta a tsarin Dimokaraxiya: Jawabai da
  qasidun taron bita na farko domin Hakimai da
  Dagatai: Ofishin mai baiwa Gwamna shawara
  akan Harkokin Masarautu, Kano (2001) p. 48.
  An faxaxa bayanin da wasu bayanan.
5. Anon: Waqar Bagauda (1970).

SASHI NA UKU
1. Hogben and    Kirk-Greene: The Emirates of
  Northern Nigeria: a Preliminary Survey of the
  Historical Tradition, London, (1966) p. 36.
2. Ibid pp. 36-37
3. Fashewar madatsar ruwa (dam) ta Saddu
  Ma‟arib an yi bayaninsa a Alqur‟ani mai tsarki
  cikin Suratul Saba aya ta 15-19.
4. Hassan, H.I. Tarikhil Islam, wal-dini, wal-
siyasi, wal-ijma‟i Cairo, (1935).
5. Adamu na Ma‟aji, Al-atharul Kanawiyya, p.5
ba a buga shi ba.
6. Abdulkadir, T.A.: Establishment of Economic
Ventures by Local Government Areas (Gaya
Local Government Area), 1995. Wannan suna
“Kanoki” sunan Samawa da Hamawa ne waxanda
suka zauna a qasar Yamal. Mahaifin Annabin           192
Kano Qwaryar Qira…...

Salihu yana daga cikin masu wannan suna, shi
yasa ake kiransa “Salihu bn Kanoki”.
7. Asalin Littafin Tarihin Kano sunansa Tarikhi
Arbab Hazal-balad al-musamma bi Kano. Shi ne
kuma Mr. Palmer ya fassara da turanci yasa masa
Kano Chronicle.
8.   Wannan gari “Dahlak” a gavar kogin
maliya ya ke. Kuma tsibirai ne kamar guda xari,
masu kama da dutsen Dala.
9.   Lugard, F.S. : Tropical Dependency, opcit
(1906)
10. Adamu na Ma‟aji, Al-atharul Kanawiyya,
opcit. p. 5.
11. Anon, Labarin Hausawa da Makwabtansu,
Littafi na biyu NNPC Zaria, (1970) pp. 1-3.
12. Ibid pp. 1-3.
SASHI NA HUXU
 1.  Adamu    na  Ma‟aji:   Al-atharul
    Kanawiyya, opcit. p. 9
 2.  Labarin Hausawa da Makwabtansu,
    opcit. p. 3
 3.  Ibid p. 2
 4.  Ibid p. 2
 5.  Wasu abubuwa da Kano ta gada daga
    halayen qabilun Dala na farko sune:
    a. Zaman lafiya a tsakanin qabilu; don
     babu labarin yaqe-yaqe a tsakaninsu a


            193
           …………….Daga Dutsen Dala

      wancan lokacin;
     b. Rashin nuna banbancin qabila;
     c. Karvar baqi.
     Wannan shi ne halin Kano har yanzu.
SASHI NA BIYAR
  1.  Anon, Waqar Bagauda ta Kano,
     (1969) NNPC Zaria, pp. 3-5
  2.  Adamu, M.: (1978), The Hausa
     Factor in West African History, OUP
     Nigeria, Zaria/Ibadan
  3.  An yi bayanin Bagaudan farko da ya
     zo Kano shi da „yan uwansa domin
     farauta, suka koma noma suka yi
     arziqi,  suka    naxa   Bagauda
     shugabansu domin tsaro. Duba shafi
     na 56-60 na wannan littafin.
  4.  Hogben, S.J. and Kirk-Greene,
     A.H.M.: The Emirates of Northern
     Nigeria…. (1966), London, OUP pp.
     10-11
  5.  Ibid: A cikin hijira ta 683 ne rundinar
     mayaqan Uquba na qabilar Barbers
     suka yi masa tawaye suka yaqe shi
     har suka kashe shi a Qairawan. Daga
     nan suka kafa sabon mulki na qabilar
     Barbers.           194
Kano Qwaryar Qira…...

   SASHI NA SHIDA
   1. Hausawa da Maqwabtansu, Littafi na
     biyu (1970) NNPC Zaria, pp. 3-4
   2. Ibid p. 4
   3. Ibid pp. 4-5
   4. Ibid p. 6
   5. Ibid pp. 10-11
   6. Ibid pp. 12-15

   SASHI NA BAKWAI
   1. Hausawa da Maqwabtansu, opcit. pp.
     21-22
   2. Ibid pp. 21-22
   3. Gwarzo, H.I.: The Life and
     Teachings of Al-Maghili with
     Particular Reference to Sahara Jewish
     Community,   unpublished   Ph.D.
     Thesis, University of London, (1970)
   4. Barkindo, B.M.: The Role of Al-
     Maghili in the reform of Sarki
     Muhammadu Rumfa (1463-1499) of
     Kano: a Re-examination, Kano
     Studies new Series Vol. I 1987-88 pp.
     86
   5. Adamu, M.U.: Confluences and
     Influences: The Emergence of Kano
     as a City-State, Munnawar Books            195
       …………….Daga Dutsen Dala

   Foundation, Kano (1999) pp. 45-46
6.  Ibid pp. 46-47

SASHI NATAKWAS
1. Labarin Hausawa da Maqwabtansu:
  pp. 23-29
2. Ibid pp. 29-40
3. Ibid 41-43
4. Adamu, M.U.: Nazari na musamman
  akan Method of Teaching and Child
  Psychology (1962) School for Arabic
  Studies, Kano ba a buga shi ba amma
  akwai shi a hannun Mawallafin
5. Hassan, M. da Na‟ibi, S. The
  Chronicle of Abuja, Lagos, (1962)
6. Kano, (Mallam) Aminu.: Hikayoyin
  Kaifafa Zukata (sabon bugu):
  Mambayya House, Kano, (2003) p.
  39
       196
Kano Qwaryar Qira…...

        RATAYA
 LISSAFIN SARAKUNAN HAVE NA KANO
 DA SHEKARUN MULKINSU DANGANE DA
   SAVANIN MARUBUTA TARIHI

  Kamar yadda aka karanta a cikin littafin nan an
sami ruxani dangane da tarihin Kano musamman
abin da ya shafi shekarun kafa Kano da fara
sarauta a cikin ta. Yanzu ga banbance-banbancen
da aka samu daga marubuta tarihin Kano guda
biyar:
  1. Littafin Tarihin Arbab hazal Baladi (Littafin
    tarihin Kano)
  2. Littafin Taqyidil Akhbari na Alqali
    Muhammadu Zangi
  3. Littafin Al-iilan bi tarihi Kano na Malam
    Adamu na Ma‟aji
  4. Waqar Bagauda ta Malam Ahamadu na
    Rano
  5. Prose Writing in Ajami na Alhaji Umaru
    Bakabe
  Sai a lura duk inda aka sa “SH” ana nufin
shekara kenan, “WT” kuma wata ake nufi.
            197
           …………….Daga Dutsen Dala

Lissafin Littafin Tarihil Arbab Hazal Baladi Al
musamma Bi Kano
Lamba Sunan Sarki        Tsawon
                Mulkinsa
1.    Bagauda        S.H. 66
2.    Warisi         S.H. 33
3.    Aji Masu- Gijin Masu S.H. 40
4.    Nawata/Gawata     S.H. 2
5.    Xariqi-Yusa      S.H. 60
6.    Naguji         S.H. 55
7.    Guguwa         S.H. 44
8.    Shekarau        S.H. 17
9.    Tsamiya-Randamasu   S.H. 37
10.   Zamna Gawa-Usman S.H. 7
11.   Yaji-Ali        S.H. 37
12.   Bugayya-Muhammadu S.H. 5
13.   Kanajeji        S.H. 20
14.   Umaru         S.H. 12
15.   Dawuda         S.H. 17
16.   Abdullahi Barja    S.H. 15
17.   Dakauda        -
18.   Atuman         -
19.   Yakubu         S.H. 11
20.   Muhammadu Rumfa    S.H. 37           198
Kano Qwaryar Qira…...

21.   Abdullahi       S.H. 10
22.   Muhammadu Qisoki   S.H. 58
23.   Yakubu        -
24.   Dawuda Abasama    -
25.   Abubakar Kada     S.H.7 da WT
               6
26.   Muhammadu   Sha  S.H. 9
    Shiri
27.   Muhammadu Zaki    S.H. 37
28.   Muhammadu Na Zaki   S.H. 5
29.   Muhammadu Alwali   S.H. 26
    Kutumbi
30.   Alhaji        S.H. 1
31.   Shekarau       S.H. 2
32.   Muhammadu Kukuna   S.H. 1
33.   So Yaqi        -
34.   Muhammadu Kukuna   S.H. 8
35.   Bawa         S.H. 10
36.   Daxi         S.H. 34
37.   Muhammadu Sharifa   S.H. 29
38.   Muhammadu Kumbari   S.H. 13
39.   Alhaji Kabi      S.H. 10
40.   Muhammadu Yaji    S.H. 16
41.   Babba Zaki      S.H. 8
42.   Dawuda Abu A Sama   S.H. 5            199
          …………….Daga Dutsen Dala

43.  Muhammadu Alwali    S.H. 27
     Jimla         750
Lissafin Littafin Taqyidul Akhbari
Lamba     Sunan Sarki     Tsawon
                 Mulkinsa
1.    Bagauda       S.H. 70
2.    Haunasu       S.H. 40
3.    Saraka        S.H. 60
4.    Abu-giji       S.H. 2
5.    Guguwa        S.H. 50
6.    Makankari      S.H. 51
7.    Karaurawa      S.H. 8
8.    Randa        S.H. 30
9.    Zamna Gawa      S.H. 7
10.    Kutunqurasa     S.H. 7
11.    Bagaji        S.H. 5
12.    Kanajiji       S.H. 22
13.    Umaru        S.H. 12
14.    Nuwatau       S.H. 10
15.    Dauda        S.H. 70
16.    Abdullahi      S.H. 15*
17.    Yakubu        S.H. 10
18.    Muhammadu Rumfa   S.H. 37
          200
Kano Qwaryar Qira…...

19.   Abdullahi       S.H. 11
20.   Muhammadu Qisoke   S.H. 52
21.   Yakubu        WT. 5
22.   Dauda         WT. 2
23.   Abubakar       S.H. 7
24.   Muhammadu       WT. 5
    Shashare
25.   Muhammadu Zaki    S.H. 38
26.   Muhammad Gurzau    S.H. 4  da
               WT.5
27.   Alwali Kutumbi    S.H. 26
28.   Alhaji        S.H. 1
29.   Shekarau       S.H. 1  da
               WT.7
30.   Soyaqi        S.H. 1  da
               WT.2
31.   Muhammadu Kunkuni   S.H. 8
32.   Bawuri        S.H. 10
33.   Muhammadu Daxi    S.H. 30
34.   Sharifa        S.H. 30
35.   Kumvari        S.H. 13
36.   Tunqura ai kulbi   S.H. 9  da
               WT.9
37.   Yaji         S.H. 7
38.   Babba Zaki      S.H. 8            201
            …………….Daga Dutsen Dala

39.    Dawuda         S.H. 5
40.    Al-wali         S.H. 27
     Jimla          720.6
*A wannan lissafi na Muhammadu Zangi ya
tsallake Dakauda na 17 da Atuman na 18 a lissafin
littafin tarihin Kano, waxanda suke tsakanin
Abdullahi Barja da Yakubu. Kuma bai maimaita
sunan Kukuna ba wanda yai sarauta sau biyu. Shi
yasa lissafin sa ya tsaya a 40 ba kamar na littafin
tarihin Kano mai 43 ba.

Lissafin littafin Al-iilan Bi Tarihi Kano na
Malam Adamu Na Ma’aji
Lamba     Sunan Sarki     Tsawon
                 Mulkinsa
1.    Bagauda        S.H. 77
2.    Dawarwasa       S.H. 50
3.    Nawata/Gawata     S.H. 1
4.    Gijinmasu       S.H. 40
5.    Makankare       S.H. 70
6.    Bugaji        S.H. 2
7.    Guguwa        S.H. 70
8.    Tsariki        S.H. 60
9.    Shekarau (Wada)    S.H. 7
10.   Randamasu       S.H. 39            202
Kano Qwaryar Qira…...

11.   Zamnagawa       S.H. 9
    (Gakingakuma)
12.   Yaji         S.H. 20
13.   Bage         S.H. 5
14.   Kanajeji       S.H. 22
15.   Malam Umaru      S.H. 12
16.   Dawuda        S.H. 27
17.   Abdullahi       S.H. 25
18.   Yakubu        S.H. 10
19.   Muhammadu Rumfa    S.H. 30
20.   Abdullahi       S.H. 12
21.   Yakubu        WT. 6
22.   Dawuda        WT. 4
23.   Muhammadu Qisake   S.H. 58
24.   Yakubu     da  S.H. 1
    Muhammadu Sheshe
25.   Abubakar Kado     S.H. 7
26.   Muhammadu Zaki    S.H. 30
27.   Muhammadu Abda    S.H. 5
28.   Alwali Kutumba    S.H. 40
29.   Alhaji        S.H. 20
30.   Shekarau       S.H. 1*
31.   Kukuna        S.H. 8
32.   Bawa         S.H. 11            203
            …………….Daga Dutsen Dala

33.    Muhammadu (Daxin S.H. 33
      Allah)
34.    Muhammadu Sharifa   S.H. 30
35.    Kumbaru        S.H. 10`
36.    Muhammadu Kabi     S.H. 10
37.    Yaji          S.H. 3
38.    Babba Zaki       S.H. 8
39.    Dawuda         S.H. 5
40.    Alwali Qarami     S.H. 27
      Jimla         1078.2
*Shi ma wannan littafin ya tsallake Dakauda da
Atuma da Soyaqi kamar yadda muka gani a
lissafin Muhammadu Zangi to amma shi Malam
Adamu kuma ya haxe sarautar Yakubu na 24 da
sarautar qaninsa Muhammadu Sheshe wanda
kuwa ba zamani xaya sukayi ba. Da ya raba su da
lissafin sa sai ya zama 42 kenan tun da bai
maimaita sunan Muhammadu Kukuna ba, da yayi
haka da shi ma nasa lissafin yayi daidai da tarihin
Kano. Wajen lissafin shekaru kuma yayi daidai
domin shekarunsa sun haxa da shekarun sarakunan
hukumar farko ta     Maxatai ta Bagauda xan
farauta ya lissafa shekarun akan shauran
sarakunan Bagaudan Daura, saboda rashin samun
lissafin sarakunan farko.            204
Kano Qwaryar Qira…...


Lissafin Waqar Bagauda
Lamba    Sunan Sarki     Tsawon
                Mulkinsa
1.   Bagauda        S.H. 50
2.   Warisi        S.H. 50
3.   Nawatau        S.H. 70
4.   Gawata        S.H. 30
5.   Ajimasu        S.H. 40
6.   Makankari       S.H. 77
7.   Guguwa        S.H. 70
8.   Wada         S.H. 7
9.   Gaqin-gaquma     S.H. 60
10.   Bagaji        S.H. 2
11.   Shekarau       S.H. 17
12.   Kunajiji       S.H. 20
13.   Umaru         S.H. 12
14.   Muhammadu Rumfa    S.H. 30
15.   Dan Maganarku     S.H. 20
16.   Dauda         S.H. 25
17.   Abdullahi       S.H. 25
18.   Yakubu        S.H. 10
19.   Abdullahi       S.H. 1
20.   Muhammadu       S.H. 30            205
        …………….Daga Dutsen Dala

   Qisakewa
21.  Muhammadu Sheshe   WT. 3
22.  Yakubu        WT. 6
23.  Bubakar       S.H. 7
24.  Muhammadu Shashire  S.H. 5
25.  Muhammad Zaki    S.H. 40
26.  Kutumbi       S.H. 209
27.  Shekarau       S.H. 40
28.  Dauda        S.H. 20
29.  Alhaji        S.H. 50
30.  Soyaqi        -
31.  Kukuna        S.H.30
32.  Bawa         S.H. 30
33.  Muhammadu Daxi    S.H. 9
34.  Sharifa       S.H. 40
35.  Kumbaru       S.H. 80
36.  Muhammad Kubari   S.H. 10
37.  Yaji         S.H. 3
38.  Babba Zaki      S.H. 25
39.  Dauda        S.H. 5
40.  Alwali        S.H. 27
   Jimla        1033.36
         206
Kano Qwaryar Qira…...

*An tsallake Dawuda da Abdullahi Barja da
Bagauda da Atuman. Wannan lissafi na waqar
Bagauda yayi daidai da lissafin Adamu na Ma‟aji
shi ma ya lafta shekarun Sarakunan farko ta su
Bagauda xan farauta akan Sarkunan hukuma ta
uku ta Bagaudan Daura. Shi Bagaudan Daura
Kanawa ne da kansu suka kirawo shi suka naxa
shi sarkin Kano, domin Sarakunan bayan Bagauda
xan farauta irin su Gwale, da Yakasai, Sheshe, da
Guguwa duk sun qare. Ba shakka akwai alaqa ta
qabilanci a tsakanin Bagauda xan farauta da sabon
Bagauda da aka gaiyato daga Daura, amma ba ta
tatsuniyar Bayajida ba.

Hausa prose writing in Ajami na Alhaji Umaru
Ba-Kabe
Lamba    Sunan Sarki     Tsawon
                Mulkinsa
1.   Bagauda        S.H. 70
2.   Qunasan        S.H. 30
3.   Agmasu        S.H. 40
4.   Tarika        S.H. 60
5.   Abgaji        S.H. 2
6.   Guguwa        S.H. 50
7.   Makankari       S.H.1 daWT.7
8.   Karwana        S.H. 80            207
         …………….Daga Dutsen Dala

9.  Randa         S.H. 37
10.  Zamnagawa       S.H. 7
11.  Ture-Ture       S.H. 7
12.  Bogaji        S.H. 5
13.  Jilju         S.H. 10
14.  Yaji         S.H. 20
15.  Umaru         Kwana 12
16.  Nuta         Kwana 10
17.  Gawata        Kwana 15
18.  Dawuda        S.H. 15
19.  Abdullahi       S.H. 25
20.  Yakubu        S.H. 10
21.  Muhammadu Rumfa    S.H. 37
22.  Abdullahi       S.H. 11
23.  Muhammadu Kisoki   S.H. 58
24.  Yakubu        S.H. 10 da
              WT.5
25.  Dawuda        Kwana 50
26.  Abubakar Kado     S.H. 7
27.  Muhammadu       S.H. 1 da
   Shashire       WT.1
28.  Zaki         S.H. 30
29.  Muhammadu     xan S.H. 4 da
         208
Kano Qwaryar Qira…...

    Abdullahi        WT.5
30.   Muhammadu        S.H. 26
    Kushube
31.   Alhaji xan Kushibi   S.H. 1
32.   Shekarau     xan  S.H. 1 da WT 7
    Dausayi
33.   Kukuna         S.H. 8 da WT 8
34.   Soyaqi         WT. 2
35.   Abdullahi (Bawa) xan  S.H. 11 da WT
    Kukuna         4
36.   Muhammadu Dadi     WT. 8 da KW
                9
37.   Muhammadu Sharifa    S.H. 29
38.   Muhammadu        S.H. 13
    Kumvaru
39.   Muhammadu Kubi     S.H. 9 da WT.
                9
40.   Yaji          S.H. 16
41.   Babba Zaki       S.H. 8
42.   Dawuda         S.H. 4
43.   Muhammadu Alwali    S.H. 27
    Jimla          750.8
            209

				
DOCUMENT INFO
Shared By:
Categories:
Stats:
views:12822
posted:6/2/2011
language:
pages:208